Kungiyar M23 Ta Sanar Da  Kwace Iko Da Garin Goma

Ana ci gaba da fada mai tsanani a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo tsakanin sojojin gwamnati da kuma mayakan kungiyar M 23 da suke samun goyon

Ana ci gaba da fada mai tsanani a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo tsakanin sojojin gwamnati da kuma mayakan kungiyar M 23 da suke samun goyon bayan kasar  Rwanda.

A yau Litinin wannan kungiyar ta sanar da cewa ta kama garin Goma da shi ne babban birnin yankin gabashin kasar ta DRC.

Wannan sanarwar dai ta zo ne gabanin cikar wa’adin sa’oi 48 da kungiyar ta bai wa sojojin gwamnatin DRC da su a jiye makamansu a kasa.

MDD ta bayyana cewa da akwai rudani a tsakanin mutanen garin da adadinsu ya kai miliyan biyu.

Da akwai dubban mutanen yankin da su ka sami mafaka a cikin garin na Goma saboda yakin da ake fama da shi.

‘Yan tawayen sun yi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankulansu,tare da yin kira ga sojojin gwamnati da suke cikin garin da su kai kansu cikin filin wasan kwallo kafa na birnin.

Gwamantin kasar ta bayyana abinda M23 ta yi da cewa shelanta yaki ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments