Search
Close this search box.

Kungiyar Hizbullahi Ta Yi Luguden Bama-Bamai Kan Cibiyar Sojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kungiyar Hizbullahi ta Lebanon ta yi luguden wuta kan hedkwatar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke garin Kiryat Shemona Mayakan gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da

Kungiyar Hizbullahi ta Lebanon ta yi luguden wuta kan hedkwatar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke garin Kiryat Shemona

Mayakan gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Lebanon sun yi ruwan bama-bamai kan hedikwatar runduna ta 769 ta Gabas (mai alaka da runduna ta 91) ta rundunar sojin yahudawan sahayoniyya da ke barikin Kiryat Shemona na haramtacciyar kasar Isra’ila.

A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullahi ta fitar ta bayyana cewa: Domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da suke tsayin daka a Zirin Gaza da kuma goyon bayan jajircewarsu a fagen mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila, mayakan Hizbullahi sun kai wasu jerin hare-hare kan garuruwan Yaroun da Khiyam musamman kan hedkwatar rundunar sojin yahudawan sahayoniyya ta 769 ta Gabas (da ke da alaka da bangaren 91) A cikin barikin Kiryat Shemona tare da yin luguden rokoki da dama na Katyusha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments