Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa

Wata majiya ta hizbbulla  ta fadawa gidan talabijin din al-hadatha cewa kungiyar tana nan kan bakanta na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka sanyawa

Wata majiya ta hizbbulla  ta fadawa gidan talabijin din al-hadatha cewa kungiyar tana nan kan bakanta na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka sanyawa hannu tsakaninta da isra’ila musamman a yankunan kudancin kasar da kuma tekun litani

Duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan decembar shekara ta 2024 amma akwai fargaba sosai  a iyakokin labanon da Isra’ila , sai dai hizbullah ta fitar da sanarwa a baya bayan nan wanda ke nuna shirinta na mayar da martani mai tsanani idan israila ta tsokaneta, duk da kasashen yamma na kokarin ganin an kawar da makamai da kuma rage tasirinsu,  adaidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yiyuwar sake barkewar wani rikici

Ministan harkokin wajen kasar faransa Jean-neol barrot ya bayyana cewa kasarsa na goyon bayan kwabe makaman hizbullah  kuma yayi kira ga isra’ila da ta janye daga wurare biyar masu muhimmanci a kudancin labanon.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments