Kungiyar Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Kai Wa Yemen Hari Da HKI Ta Yi

A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta yi tir da harin da HKI ta kai wa biranen San’aa da kuma Hudaida a

A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta yi tir da harin da HKI ta kai wa biranen San’aa da kuma Hudaida a raanr Alhamis din da ta gabata wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 12 da kuma jikkatawa.

A cikin bayanin, kungiyar ta Hizbullah ta siffata “Isra’ila” da cewa daidai take da cutar daji, sannan ta ce; Saboda kasar ta HKI ta kasa cimma manufofinta a cikin fagage da daman a gwgawarmaya, ta koma kai wa kasar Yemen hare-hare domin ta rufe ranunita.

Bugu da kari, kungiyar ta Hizbullah ta yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su daina yin shiru akan laifukan da ‘yan sahayoniyar suke tafkawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments