Search
Close this search box.

Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Harbo Jirgin Yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta Lebanon ta sanar da kakkabo jirgin sama maras matuki kirar “Hermes 900” mallakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta Lebanon ta sanar da kakkabo jirgin sama maras matuki kirar “Hermes 900” mallakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi ta kasar Lebanon ta sanar da kakkabo jirgin saman yaki maras matuki ciki kirar Hermes 900 da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take amfani da shi wajen kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Lebanon, kuma kungiyar ta kakkabo jirgin ne da makaman da suka dace a cikin kasar Lebanon.

A sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya Asabar, ta ce ta kai wani harin kwantan bauna ne kan jirgin saman kirar Hermes 900 da ke kai hare-hare kan al’ummar Lebanon, tare da harbo shi a yankin kasar ta Lebanon, bayan sanya ido da kuma bin diddigin shawagin jiragen mamayar yahudawan sahayoniyya da suke kai hare-hare da suke janyo shahadar mutane da lalata dukiyoyin jama’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments