Kungiyar Hizbullah Ta Kai Hare-Hare Kan Matsugunin ‘Yan Sahayoniyya A Gabashin Birnin Qudus

Kungiyar Hizbullah ta yi ruwan bama-bamai kan matsugunin ‘Ma’aleya- Adumim’ da ke gabashin birnin Qudus da aka mamaye Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun yi furuci

Kungiyar Hizbullah ta yi ruwan bama-bamai kan matsugunin ‘Ma’aleya- Adumim’ da ke gabashin birnin Qudus da aka mamaye

Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun yi furuci da cewa: A yammacin jiya Asabar mayakan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta                                              Hizbullah sun yi luguden makamai masu linzami kan matsugunin yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida na Ma’aleya-Adumim da ke gabashin birnin Qudus da aka mamaye.

Sanarwar sojojin ta kuma ce: Na’urorin kariya na kakkabo makamai masu linzami na gwamnatin mamayar sun kasa kakkabo makaman masu linzami, sakamakon haka suka isa inda aka tsaita su, wadanda suka haddasa tashin gobara a yankin.

Tashar talabijin ta 12 taharamtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Tashin bama-baman sun yi sanadin samu gine-gine da janyo barna gare su a yankin Binyamin.

A cewar majiyoyin yankin, yankin da ke kewayen matsugunin Ma’aleya- Adumim ya kunshi sansanoni da dama na sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments