Search
Close this search box.

 Kungiyar Hizbullah Ta Harba Wa HKI Makmai Masu Linzami Fiye Da 200

A yau Alhamis kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba wa HKI malamai masu linzami fiye da 200  da kuma jerin jirage marasa matuki a

A yau Alhamis kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba wa HKI malamai masu linzami fiye da 200  da kuma jerin jirage marasa matuki a karkashin mayar da martani na kisan gillar da ta yi wa daya daga cikin kwamandojinta.

Daga cikin yankunan da hare-haren na HIzbullah su ka shafa, da akwai barikin sojan “Ilayat’ da kuma barikin “Katsafiya, da kuma babbar shalkwatar rundunar motoci masu silke da Gamila.

Bugu da kari, kungiyar ta Hizbullah ta sanar da kai wasu hare-haren ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuki akan cibiyoyi masu yawa na ‘yan mamaya.

HKI ta kai hari ne a garin Sur dake kudancin Lebanon wanda ya yi sanadiyyar shahadar daya daga cikin kwamandojin kungiyar ta Hizbullah.

A wani bayanin na daban da kungiyar ta Hizbullah ta fitar, ta bayyana kai wasu hare-haren ta hanyar amfani da makamai masu linzami samfurin; Burkan”akan cibiyar “Rusait-al-alam” da hakan ya haddasa tashin gobara a cikinsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments