A yau litinin ne kungiyar Al-qassam brigades bangaren soji na kungiyar Hamas ta mika yahudawa guda 7 daga cikin guda 20 da ta kama su take rike da su ga hukumar kula da bada a gaji ta duniya a yankin Gaza
Kungiyar hamas ta cika alkawarin da ta dauka na mika sauran mutane da take tsare da su domin nuna gaskiyar aniyarta na kulla yarjejeniyar zaman lafiya da tsaro a yankin Gaza, duk da yake cewa Isra’ila ta kafa tarihin cin amana da rashin cika alkawari kan duk wata yarjejeniya da aka kulla tsakaninta da alummar falasdinu.
Wannan shi ne zangon farko na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma bayan shiga tsakani da aka yi a sharma El-shaikh da ya hada da kasashen Turkiya Masar da kuma kasar Qatar, kuma kasar Amurka ta zama mai sa ido a wajen saboda yanayin tsaro da ake ciki a yanki.
Kafafen yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa sunayen mutane da hamas ta saki yayi dai dai da wanda ke hanuun Isra’ila kuma yana wakiltar amincewar hukuma a matakin farko na aiwatar da yarjejeniyar,