Kungiyar Hamas Ta Lashi Takwabin ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa

Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan mamayar

Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan mamayar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan sahayoniyya, tare da yin nuni da cewa, za ta ci gaba da kokarinta ba tare da wata matsala ba, domin kubutar da su ta kowace hanya.

Kungiyar Hamas ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a a yayin bikin sakin wani sabon rukunin fursunonin Falasdinu, tana jaddada cewa: Hamas ta sake sanar da babban alfahari da girmamawa ga al’ummar Falastinu masu tsayin daka, a daidai lokacin da aka sako wani sabon rukunin fursunonin Falasdinawa wadanda suke jarumai daga gidajen yarin yahudawan sahayoniyya, bayan gwagwarmaya ta tilasta musu bude kofofin gidajen yarinsu domin sake Falasdinawa, kuma karkashin yarjejeniyar dakatar da wuce gona da iri da musayar fursunoni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments