Kungiyar Hamas Ta Ki Amincewa Da Kwance Damarar Kungiyar A Gaza

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ya yi watsi da bukatar HKI na kwance damarar dakarun kungiyan a matsayin sharadi na ci gaba

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ya yi watsi da bukatar HKI na kwance damarar dakarun kungiyan a matsayin sharadi na ci gaba da aiwatar da yarjeniyar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025. Kungiyar ta kara da cewa, kwance damara dakarun kungiyar jar layi ne a wajenta.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa HKI tana bukatar ta raba kungiyar da makamanta, kafin ta ci gaba da aiwatar da yarjeniyar ta watan Jeneru. Wannan  bukatar dai ta sa tababa a cikin yiyuwar tsagaita wuta tsakanin HKI da Hamas ya dore.

Yarjeniya ta yanzu dai, wacce ta faraaiki a ranar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025, kuma an tsara shi bisa marhaloli 3. Daga ciki har da tsarin yadda masu shiga tsakani zasu gabatar da musayar fursinoni da har zuwa janyewar sojojin HKI daga Gaza. Amma gwamnatin Natanyahu tace ba zata taba ficcewa daga Gaza ba.

Kakakin kungiyar Sami Abu Zuhri ya ce: Batun kwance damarar dakarun Izzudden Qassam, maganar banza ce. Makaman hamas jar laye ce, wand aba zata taba amincea da haka. Ministan harkokin wajen HKI, Gidion Sa’ar ya ce: Muna bukatar kwance damarar Hamasa da Jihadul Islamu da sauransu, sannan a mika mana yahudawan da ake garkuwa da su, idan sun yi haka, gobe ma a aiwatar da yarjeniyar.

Sannan wani kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem yace Hamas ba za ta amince da tsawaita marhala ta farko na yarjeniyar ba. Ya kuma bukaci a takurawa HKI don ta amince da ci gaba da aiwatar da marhaloli na gaba.

Natanyahu ya dauki yarjeniyar a matsayin na wucin gadi ne, don haka za’a iya komawa yaki a ko wani lokaci. A cikin makonni masu zuwa ne zamu gane, kan cewa, yarjeniyar zata ci gaba ko kuma za’a koma yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments