Kungiyar Bada Agaji Ta  ‘Red Cross” Ta Ce Ta Fice Daga Jumhuriyar Nijer

vvddxfKungiyar bada agaji ta Red Cross ta nbada sanarwan cewa ta rufe ofishinta a Nijer kuma ta fidda dukkan ma’aikatanta na kasashen waje daga kasar.

vvddxfKungiyar bada agaji ta  Red Cross ta nbada sanarwan cewa ta rufe ofishinta a Nijer kuma ta fidda dukkan ma’aikatanta na kasashen waje daga kasar.

Ta kuma kara da cewa, gwamnatin kasar ta bukacin kungiyar ta fice daga Nijer tun watanni 4 da suka gabata, amma bata yi hakan bas ai yanzu.

ICRC ta tabbatar da hakan a ranar Alhamis da ta gabata Sannan Patric Yousuf daraktan kungiyar a Nahiyar Afirka ya bayyana cewa sun janye ma’aikatansu a Nijer sannan suna tattaunawa da gwamnatin kasar don sake dawowa kasar da kuma ci gaba da ayyukansu na bada agaji.

A cikin watan Fabrayrun wannan shekara ne ministan harkokin wajen kasar ya bada wannan umrnin ba tare da bayyana dalilan yin haka ba.

Kungiyar ta bada sanarwan cewa tun watan Fabrairun wannan shekara ne suke bin jami’an gwamnatin sojojin kasar domm samun takamemmen dalilin da yaaa sa suka dauki wannan matakin amma daga karshe sun fice daga kasar bayan sojojin sun dage a kan rufe ofishin kungiyar

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted