Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen Ta Jaddada Aniyarta Ta Taimakawa Falasdinawa

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Za su ci gaba da gwagwarmaya ko da Amurka zata tunkaro jirgin ruwanta da ke dauke

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Za su ci gaba da gwagwarmaya ko da Amurka zata tunkaro jirgin ruwanta da ke dauke da jiragen saman yaki zuwa tekun Bahar Maliya

Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi, a cikin jawabin da ya gabatar a jiya Alhamis cewa: Manufar Amurka da ‘yan sahayoniyya kokari ne kawai na son aiwatar da ayyukan zalunci kan raunanan al’ummu, yana mai jaddada cewa; Al’ummar Yemen za su ci gaba da gudanar da ayyukansu kan azzalumai ko da Amurka za ta kusato da babban jirginta mai dauke da jiragen yaki zuwa cikin tekun Bahar Maliya.

Sayyid Houthi ya jaddada cewa: Babu makon da zai wuce ba tare da al’ummar kasar Yemen sun ba da shahidai a tafarkinsu na jihadi ba, yana mai cewa: Ayyukan zaluncin yahudawan sahayoniyya da Amurka ke son aiwatarwa ayyukan zalunci ne kan al’ummar yankin domin cimma manufofinsu ta mamaya da babakere.

Sayyid Houthi ya kara da cewa: A cikin tsarin bikin zagayowar tunawa da shahidan na shekara-shekara a bana zai fi mayar da hankali ne kan abubuwa guda uku: Karfafa manufar jihadi da kimar shahidai da suka sadaukar da rayukansu domin Allah, da kuma tunawa da shahidai gami da daukar darussa daga tarihin rayuwarsu da jaddada muhimmancin shirye-shiryen da suka shafi kula da iyalan shahidan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments