Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa hare-haren ta’adanci wadanda sojojin Amurka da Burtaniya suka kai kan yankuna da dama a kasar ba za su hana mutanen kasar ci gaba da kare Falasdinawa a Gaza ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Al-huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Lahadi da yamma. Ya kuma kara da cewa sojojin kasar zasu ci gaba da kai hare hare kan katafaren jirgin ruwan yaki mai daukar jiragen saman yaki na Amurka, da ke cikin Tekun maliya.
Sannan yace za su ci gaba da kai hare hare kan jiragen HKI da na Burtaniya da na Amurkan, masu wucewa ta tekun malia kamar yadda ta bayyana tun farko.
Kafin haka dai jiragen saman yakin wadanda suka taso daga kan kataparen jirgin ruwa mai daukar Jiragen yaki na kasar Amurka, suka kai hare hare a yankuna da dama a kasar ta Yemen, wadanda suka hada da birnin San’a babban birnin kasar. Hare-haren dai sun kashe yara da mata da dama sannan sun lalata injunan bada wutan lantarki da dama.
Kungiyar Ansarullah ta kasar yemen dai ta tallafawa Falasdinawa a yankin tufanul Aksa wanda aka fara a ranar 7 ga watan octoban shekara ta 2023, har zuwa lokacin da aka tsagaita wuta tsakanin Falasdinawa a Gaza da HKI a ranar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025.
Amma a cikin yan makonnin da suka gabata HKI ta hana abinci da magunguna da kuma sauran bukatun Falasdinawa shiga yankin na Gaza. Wanda ya sa kungiyar ta koma tana hana jiragen HKI wucewa ta Tekun maliya.