Kungiyar Ansarallah Ta Kasar Yemen Ta Bude Ofishinta A Bagadaza

Kungiyar Ansarulla ta kasar Yemen ta bude babban helkotan kungiyar a birnin Bagdaza babban birnin kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran a

Kungiyar Ansarulla ta kasar Yemen ta bude babban helkotan kungiyar a birnin Bagdaza babban birnin kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran a Bagadaza, ya nakalto wata majiya kusa da ofishin firai ministan kasar Iraki Muhammad shia Assudani, wanda bai son a bayyana sunanta ya na fadar haka, ya ce wannan ba ofishin kungiyar Ansarullah ne aka bude ba, said a helkwatan kungiyar ne a kasar Iraki.

Ya kuma kara da cewa kafin haka wakilin kungiyar a kasar Iraki, Abu Idris al-Shorfi ya shiga tattaunawa mai zurfi da jami’an gwamnatin kasar ta Iraki kafin ya sami damar bude helkwatan kungiyar a nan birnin Bagdaza.

An bude babban ofishinn kungiyar a kasar ta Iraki ne a kusa da yankin Green Zon na birnin Bagdaza, kusa da ofishoshin jakadacin kasashen Amurka ta Burtania suke.

Majiyar ta kara da cewa Iraki ta amincewa kungiyar ta bude helkwatanta a kasar Iraki ne da sharadin kungiyar ba zata shirya wani abu na cutar da wata kasa daga cikin kasar Iraki ba.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments