Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa “ Amnesty International” ta zargi fira ministan HKI da cewa, mai aikata laifin yaki ne, da kuma amfani da yunwa a matsayin makamin yaki akan fararen hula.
Kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta bayyana cewa a cikin ganganci Netanyahu yake kai wa fararen hula harer-hare da kuma aikata laifuka akan bil’adama.
Haka nan kuma kungiyar ta yi gargadi akan ziyarar da Netanyahu zai kai wata kasa daga cikin wadanda su ka rattaba hannu a yarjejeniyar kafa kotun duniya ba tare da an kama shi ba. Kungiyar “Amnesty Interational” ta ce rashin kama Fira ministan na HKI zai kara ba shi karfin gwiwar ci gaba da aikata laifuka.
Dangane da gayyatar da kasar Hungary ta yi wa Netanyahu ya ziyarce ta, kungiyar Amnesty International’ ta bayyana shi da cewa cin zarafin dokokin kasa da kasa ne rena kotun, tana mai yin kira ga gwmanatin wannan kasar da cewa, da zarar ya isa, su damke shi, su mika shi ga kotun manyan laifuka ta kasa da kasa.
Fira ministan HKI zai kai ziyara zuwa kasar Hungary ne da take daya daga cikin wadanda su ka rattaba hannu akan yarjejeniyar Roma da ta kai ga kafuwar kotun manyan laifukan ta kasa da kasa. Ofishin Fira ministan ‘yan sahayoniyar ya ce, zaiyarar za ta dauki kwanaki biyar, zai kuma gana da takwaranta na wannan kasa Victor Orban.
Kotun kasa da kasa ta manyan laifuka ta fita da sammacin a kamo mata fira ministan HKI Benjemine Netanyahu saboda aikata laifukan yaki akan al’ummar Falasdinu.