Kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto a jiya Talata cewa, shugaba Vladmir Putin ya amince da zama mai shiga tsakanin Iran da Amurka.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya amanci cewa, kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto majiyar fadar mulkin kasar “Kremlin” na cewa shugaba Vladmir Putin zai zama mai shiga tsakanin Iran din da Amurka.
Haka nan kuma kafafen watsa labarun na Rasha sun ce; Rasha da Amurka sun amince su yi wata tattaunawa ta daban akan Iran”.
Mataimakin shugaban kasar Rasha ya ambaci cewa, a yayin zaman da kasashen biyu su ka yi a Riyadh na Saudiyya, sun tattauna akan abinda yake da alaka da Iran.
Majiyar ta kuma ce abinda kasashen biyu suke son yin Magana akansa shi ne, shirin makamashin Nukiliya na Iran.