Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani  Sabon Makami Na Sirri

 Shugaban kasar Korea Ta Arewa Kim jung Un ne ya sanar da cewa kasarsa ta kera wani sabon makami na sirri, kuma ta samu ci

 Shugaban kasar Korea Ta Arewa Kim jung Un ne ya sanar da cewa kasarsa ta kera wani sabon makami na sirri, kuma ta samu ci gaba sosai a fagen nazari da binciken kayan tsaro.

Shugaban kasar ta Korea Ta Arewa Kim Jun Ung  wanda ya yi Magana da kamfanin dillancin labarun kasar ya kara da cewa; Sabbin makaman da su ka kera za su taimaka matuka wajen karfafa sojojin kasar.”

Haka nan kuma ya ce, kasar Korea ta Arewa ta kuma karfafa sojojinta na ruwa ta hanyar kara samar da jiragen ruwa na yaki masu ninkaya a karkashin ruwa.”

Kamfanin dillancin labarun Korea Ta Arewa ya sanar da cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasar Kim Jun Ung ya sa ido akan gwajin sabon makamin da aka yi, da su ka hada da jiragen sama marasa matuki na kai hari.”

Shugaban kasar ta Korea Ta Arewa ya jaddada muhimmancin yin amfani da kirkirarriyar fasaha domin karfafa harkokin tsaro.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted