Kofar Iran A Bude Take Don Tattaunawa Da Kasashen Turai

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar Iran a bude take ga kasashen Turai don tattaunawa da fahintar juna kan matsalolin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar Iran a bude take ga kasashen Turai don tattaunawa da fahintar juna kan matsalolin da bangarorin biyu suke sabani a kansu, tare da mutunta hurumin Juna.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Netherlands Caspar Veldkamp.

Ministan ya kara da cewa dangantakar diblomasiyya tsakanin Dutch da Iran tsohuwar dangantaka ce. Sannan Iran ta na da nufin fadada shi.

A Nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Netherlands ya yaba da yadda dangantaka tsakanin kasasrsa da Iran yake bunkasa.

Sannan dangane da tsabirin kasar Iran guda uku, Abu Musa, Tumbe kucek da Bozorg wadanda iran take takaddama da UAE dangane da mallakarsu, ya ce abu ne wadanda kasashen biyu suke iya warwarewa a tsakaninsu. Banda haka yace dokokin kasa da kasa ma suna iya warware wannan sabanin da ke tsakaninsu.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments