Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa
a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake jawo maku kissoshi
wadanda suka zo cikin arkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda
suka hada da littafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Mutahhari, ko cikin
littafin Mathnawa na maulana Jalalauddeen Rumu, ko kuma dai cikin wasu littafan
da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
//.. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a
kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) kuma mahaifiyar
Alhassan da Alhussain (a) da mukekawo maku, mun tsaya inda muka fara kawo
maku khudubarta (s) a masallacin manzon All..(s), a kuma gaban Khalifa na farko
kuma sahabban manzon All..(s) da dama wadanda suke cikin masallaci a lokacin.
A cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku ci gaba da kawo maku
Khudubar, inda muka kawo inda tayi Magana kan irin halin da larabawa suke ciki
kafin zuwan musulunci, ta bayyana irin kasaksncin da suke ciki, idan ana maganar
manya manyan kasashen duniya a lokacin, wato farisa da ruma ta gabas, da kuma
yadda nasu karfi suke zaluntar marasa karfi a tsakaninsu, suna cikin tsaro dare da
rana, amma sai All..T ya tsamar da su daga wannan halin tare da babanta, ko
mahaifinta manzon All..(s).
Sannan ta bayyana matsayin babanta a cikin halittun All..T . inda ya zabe shi ya
sake sabensa ya sake zabensa, zabe na farkin tun kafin halittar yan adama, zabe na
biyu shi ne zabensa a matsayin halittar All..na farko sannan zabensa na ukku bayan
ya an halicce a matsayin mutum.
Har’ila yau tayi maganar yadda mijinta Aliyu dan Abitalib (a) ya kasance yana
yaye wa manzon All..(s) duk wata matsala ta yakar kafirai da makiyan All… Idan
ya fita a ko wani yaki ba zai dawo ba sai tare da ya sami nasara a kan makiyansa.
Sannan ta kawo matsayin Ahlulbaiti (s) a cikin al-ummar manzon All..(s). Ta
bayyana cewa su ne nayi na biyu bayan Alkur’ani mai girma wadanda manzon
All..(s) ya barwa musulmi a bayansa, a matsayin wadanda zasu jagorancesu zuwa
gaskiya.
Ta kuma bayyana yadda wasu daga cikin sahabban manzon All..(s) suna jiran su ji
mutuwar manzon All..(s).
Amma bayan wafatinsa tunda dama munafukai ne sai suka bayyana munafurcinsu.
Suka kuma fara cutar da iyalan gidansa suka kuma bar Alkur’ani mai girma.
Saboda ya bayyana matsayin Ahlulbaiti da kuma matsayinsu da All..ya basu.
Sai ta ci gaba da cewa, ina za’a je da ku alhali littafin All..yana tsakaninku? Kuma
hukunce hukuncesa a bayyana suke, sannan alamomin sa -wadanda zaku gane
gaskiya da su- suna cikinku? Haka ma gargade-gargadensa suna nan a fili, kuma
umuce -umurcensa suna bayyane,? Amma duk kun jefasu a bayanku . shin kunan
son barinsa ne,? -wato Alkur’anin-? Ko kuma kuna son yin hukunci da waninsa.?
To in dai haka ne, wannan musayar ya munana, sannan bayan kun hau kanta, wato
khalifanci, al-amura suka tabata a gareku, sai kuka fara tada fitina, kuma kwace
dukiyoyin iyalan gidan manzon All..(s).
A nan tana maganar kwace abubuwan da ta mallaka daga gonar Fadak da dukiyar
fai’u da kuma khumisi ko kuma gadonta. Da kuma takurawa wadanda basu amince
da jagorancin wadanda suka kwace khalifanci daga hannun wadanda suka kasance
hakinsu ne.
Sai taci gaba da cewa: sai kuma karban kiran shaidan batacce, na dushe hasken ma
bayyani, da boye sunnar annabi (s) mai tsarki. Kuna riya cewa kuna son hana
aukuwar fitina, amma kuma gaskiyan al-amarin ita ce kuna son shafe hasken iyalan
gidan manzon All..(s). sannan kuna cutar da iyalansa a cikin a boye da kuma
bayyane.
Amma zamu ci gaba da hakuri da cutarwarku kamar wanda ake yayyanka jikinsa
gunduwa gunduwa da wuka. Cutar da aka yi mana kamar wanda aka soka masa
mashi a cikinsa.
A halin yanzu dai kuna riya cewa bamu da gado, shin hukuncin jahilia kuke so, wa
yafi All..hukunci ga mutane wadanda suka kasance masu kasancewa.
A nan tana Maganar (s) kan cewa, a hukuncin Jahiliya, mata basa gado, sai dai
maza, don haka shin hukuncin Jahiliya ne ake son a dawo da shi, bayan da addinin
musulunci ya zo ya shafe hukuncin jahiliyya ya kuma bawa mata da maza gado.
Sai ta ci gaba da cewa: Ee gaskiya ne, wannan hukuncin ya bayyana a gareku
kamar rana, kan cewa ni diyarsa ce. Shin ba za ku hankalta ba? Ya ku musulmi,
shin za’a rinjayeni a kan gadona. Ya dan Abi kuhafa, shin a cikin littafin All..ne kai
zaka gaji mahaifinka, ni ba zan gaji babana ba.? Ka zo da wani abu wanda ba
gaskiya ba.
Shin da gangan ne kuka bar littafin All..kuka yi jifa da shi a bayanku? , kamar
yadda All..yake cewa: Kuma sulaiman ya gaji dawuda, sanna ya fada a cikin
abinda ya zo daga labarin Zakariya, a sanda ya ce: Ya bada waliyi daga wajenka.
Wanda zai gajeni ya yi gado daga cikin dangin Yakuba, Yace: Ma’abuta zumunci
sashensu sun fi cancanta da sace, a cikin littafin All…
Yace: All..na maku wasiyya a cikin yayanku, na miji yana da rabo ninki biyu na
mace. Kuma yace: Idan ya bar wasiyya na alkhairi, ga iyaye da makusanta da
kyautatawa, hakki ne ga masu tsoron All..su aiwatar da shi.
Tana nufin (s) a cikin wadannan ayoyin da ta ambata, akwai ida All..T ya fidda
annabawa cikin yayansu su ba zasu gajesu ba? Idan har haka ne shin All..ya sanar
da wata aya wacce bai sanar da mahaifina ba, ? don a lokacin khalif ana farko yace
mata : Ya ji manzon All..(s) yana fadar cewa : Mu annabawa ba’a gadommu, duk
abinda muka bari sadaka ne. shin yaushe haka ya faru gashi alkur’ani mai girma
yana cike da ayoyi wadanda suka nuna yayan annabawa suna gadon iyayensu.
Babu wata aya a cikin alkur;ani mai girma wacce ta kebe manzon All..(s) kan cewa
yayansa basa gadonsa, don shi ma kamar sauran annabawa yayansa zasu gaje shi.
Sai taci gaba da cewa:
Amma kun riya cewa bani da rabo?, ba zan yi gadon mahaifi na ba. Shin All..ya
kebanceku da da wata aya wanda bai sanar da ita ga mahaifin na ba?
Ko dai kuna ganin, Mabiya addinai biyu basa gadon juna, ? ee gaskiya ne kafiri ba
zai gaji musulmi ba, sai taci gaba da cewa: Shin ni da babana ba kan addini daya
muke ba? A nan tana shin suna shakka kan cewa ita musulma ce, wacce ta cancan
ta gaji Babanta wanda ya kawo addinin musulunci?
Sannan ta ciga da cewa: Ko dai ku ne kuka fi sanin- Umumin alkur’ani da
khususinsa, fiye da babana da dan ammi na -(wato hukunce hukuncen da ya game
kowa da kuma wadanda aka kebe shi ga wasu banda wasu. Don ayoyin gado sun
game kowa da kowa, kuma inda an kebe manzon All..(s) da wani hukunci, da ya
fadawa Zahra (s), don it ace, kadai mai gado da ya bari in banda thumunin da
matansa gaba daya zasu yi mushahara a cikinsa. Ta yayin manzon All..(s) zai
fadawa wan ikan cewa su annabawa ba’a fagonsu duk abinda suka bari sadaka ne,
amma bai fadawa wacce ita ce shari’ar musulunci zaka gaje shi? ).
Ko kuma suna ganin sun fi mijinta Aliyu dan Abitalib (s) sanin Alkur’ani mai
girma, duk da cewa manzon All..(s) yace shi ne birnin ilmi Aliyu dan Abitalib shi
ne kofar sa, duk wanda yake son ilmi ya bi ta kofar. Da haka ne da bai barta ta zo
masallaci ta yi Magana dangane da gadonta ba, da ya fada mata cewa bata da gado
don ita diyar annabi (s) ne don su annabawa ba’a gadonsu.
Sai ta ci gaba da cewa: gashi nan ka je da ita, (wato dukiyar mu ko khalifanci)
kome a shirye yake don amfaninka, zata hadu da kai ranar kiyama. (wato kowa zai
hadu da ayukansa a ranar kiyama. Kamar yadda All..T yake fada (sun sami abinda
suka aikata duk sun halarto) . Sai ta ci gaba da cewa: Madallah da mai hukunci
All… Wato a ranar kiyama All..ne da hukunci ba wani ba, kuma All..adili ne kuma
baya zalunci.).
Sai taci gaba da cewa: kuma shugaba shi ne Muhammadu. A nan tana nufin
manzon All..shi ne mai gabatar da kara a ranar kiyama a gaban All..shi mai mai
husuma da wanda ya zalunci iyalan gidansa a ranar kiyama. Sai tace: Mahadar
kuma itace ranar kiyama. Kuma a ranar kiyama masu barna zasu yi asara. Kuma ko
da kunyi nadama, wannan ba zai amfane ku ba.
A nan kuma tana nufin nadama a ranar kiyama ba zai amfanesu ba, amma a duniya
da zasu yi nadama da an karbi tubansu, kuma za’a basu dama su gyara. Sanna tace:
Akwai matabbata ga ko wani labari, da sannu zaku sani. “Sa’an nan da sannu zã ku
san wanda azãba zã ta zo masa, ta wulakantã shi (a dũniya), kuma wata azãba
zaunanna ta sauka a kansa (a Lãhira).” .
A nan Zahra (s) tana gargadi ne, ga wadanda suke nufin iyalan gidan manzon
All..(s) da zaba mai tsanani a ranar Lahira.
Sannan ta juya wajen Ansaru, (wato mutanen madina wadanda suka karbi manzon
All..(s) da wadanda suka yi hijira tare da shi zuwa madina, sun kuma taimaka masa
suka kareshi da sauran sahabansa daga makiyansu, suka kuma taimaka, har zuwa
kafuwa da kuma nasarar addinin musulunci da kuma yaduwarsa a dukkan kasashen
larabawa a lokacin, ) sai tace: Ya ku zabbu, masu taimakawa addini, wadanda suka
kare addinin musulunci,me yasa kuka yi shiri dangane da hakki na? -da kuma barci
daga karman mani abinda aka kwace daga hannu na? shin manzon All..(s) bai ce,
ana kare mutum ne a cikin yayansa ba?
A nan kuma tana tunatar da su kan fadin babanta manzon All..(s) kan cewa: Ana
kiyaye mutuncin mutum ne da kyautatawa yayansa a bayansa ba? Shin ni ba
diyarsa ba? Manzon All..(s) ba babana ba? Me yasa ba zaku kiyaye mutuncinsa a
taimaka mani don kwatar hakkin na ba? Kamar yadda larabawa suke cewa (don ido
guda ake girmama adanu dubu.
A wata nashar, tace: Shin manzon All..(s) bai cancanci a kiyaye mutuncinsa da
yayansa ba? .
To masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata
fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.