Assalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhaka barkammu da
sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo
maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin
wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya.
Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana
Jalaluddeen Ruma ko kuma dai cikin wasu littafan Da fatan masu sauraro
zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya
gabata, a kuma sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan
mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) shuwagabannin samarin Aljanna, da
muke kawo maku, `mun tsaya inda muka kawo maku karshen Khudubarta
(s) a gaban Khalifa na farko a kuma cikin masallacin mahaifinta manzon
All..(s).
Mun ji irin tasirin da Khudubar ta yi a cikin sahabban manzon All.. (s)
musamman a cikin mutanen Madina ko Ansar. A lokacinda Khalifa na farko
ya ga irin tasirin da khudubar ta yi, sai ya sake hawa kan mimbarin manzon
All..(s) ya sake yin Khuduba, inda a cikinta ya gargadi mutanen Ansar kan
cewa ya ji labarin abinda wasu wawaye daga cikinsu suka fada, amma ba
zai yi ammafani da karfi a kansu ba, saboda sune suka taimakawa manzon
All..(s) a lokacinda ya yi hijira daga Makka zuwa Madina, amma zai yi shiru
matukar ba’a taba shi ba.
A cikin khudubar ya zargi Amirul muminina (a) da ta da fitina bayan an
dusheta, kuma yana amfani ko kuma neman taimakon raunana ko mata
don cimma manufofinsa.
Sannan ya sifantasu da abubuwan da basu dace ba, kuma mun zabi
rashin ambaton hakan a cikin shirimmu.
Sai dai mun bayyana cewa Ummul Muminina Umma Sallama ( R) matar
manzon All..(s) ta mayar masa da martani a lokacinda ta ji abubuwan da ya
Fada dangane da Zahra da Mijinta Imam Aliyu (a).
Sheikh Jamaluddin Ashami ya kawo a cikin littafinsa Addurrul Nazim, yana
cewa. Bayan khudubar Fatimah (s) a masallacin manzon All..(s) da kuma
tasirin da ta yi a cikin sahabban manzon All..(s) musamman a cikin
mutanen Ansar, Khalifa na farko ya sake hawan mimbari ya kuma yi
khuduba inda a ciki ya amfani da kalmomin da muka kawo a baya
dangane da Imam Ali da kuma Fatima (a).
A lokacinda labari ya kai kunnen Ummu Salma (r ) matar matar manzon
All..(s) sai ta fusata sannan tace: Shin waye zai fadawa Fatimah (s)
hakan?. Na Rantse da All..ita hurul inice a cikin sifar mutane,
tsarkakakkiya, daga dauda, kuma ta tashi a gaban mutane masu tsarki,
sannan mala’iku ne suke kawo mata abinci, sannan ta rayu a cikin mata
masu tsarki, sannan ta sami mafi kyawun tarbiyya. Shin kuna tsammanin
manzon All..(s) zai hanata gadonta sannan ba zai fada mata ba?. All..ta’ala
na fada, (kuma ka gargadi danginka na kusa} sura ta 26:214.
Ko kuna ganin ya gargadeta sannan ta sabawa gargadinta ne? Ita ce
mafificin dukkan mata, kuma ita ce mahaifiyar shuwagabannin matan
Aljanna, sannan wacce ake kwatantawa da Maryam(a), sannan All..ya cika
sakonninsa gaa bil’adama da mahaifinta, kuma yakan yi duk abinda zai iya
yi don neman yardarta da kuma kwantar da hankalinta. Ku yi hankali
manzon All..(s) yana gininku, sannan zaku koma zuwa ga All..T , a sannan
zaku sani.
Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, saboda wannan maganar tata ce,
aka hanata rabonta na kudaden da aka saba bata a ko wace shekara.
Daga nan sai Zahra (s) ta koma gida, ta sami cewa Amirulmuminina (a) ya
na dakon dawowanta, a lokacinda ta shigo gida ta zauna, sai tace : Sai ta
fada masa abubuwan da suka faru, da kuma irin damuwarta da yadda suka
dage wajen hanata hakkinta, da kuma yadda suka yin isa daga karban
gaskiyar abinda take fada.
Sai Imam Ali (s) yace mata: Ina rokin All..ya kareki daga duk wat acuta,
makiyanki ne zasu halaka. Don haka ki kwantar da hankalinki.
Ya ke diyar zabebbe yar gidan annabci, ki kwantar da hankalinki, idan
abinda zaki rayu da shi ne kike bukata, wannan All..ya rika ya lamunce
maki rabonki, ba wanda ya isa yah ana ki. Kuma abinda All..ya tanadar
maki a can ya fi maki kan abinda aka kwace a hannunki.
Amma alokacinda matan Ansar suka ji abinda ya faru da Zahra musamman
bayan khudubarta, sai suka aiko yi Magana da mazajensu kan cewa su je
su nemi afawarta (s) sai wasu jama’a daga cikins (s) don neman afwata.
Sai dai bamu sani ba, mazajenne suka umurci matansu, su shiga wajenta,
A lokacinda suka shiga wajenta (s) sun fada mata cewa: Ya shugaban
mata, da Baban Hassan ya yi mana Magana kan wannan al-amarin kafin a
kulla shi, da ba zamu zabi waninsa ba.
Sai tace masu: ku barni da halin da nake ciki, baku da wani uzuri bayan
abinda kuka yi, da kuma kuskuren da kuka aikata.
A wasu ruwayoyin an bayyana cewa matan Muhajirun da ansar ne suka
shiga wajen Zahra (s) kuma suna da yawa, ba’a san wanda ya bada
shawarar a su zo su bata hakuri ba, amma kuma magangandu da dama
sun yadu a cikin madina dangane da Khudubarta da kuma yadda ta kare
da shuwagabannin gwamnatin lokacin. Musamman bayan da
Amirulmunina (a) ya zagaya da ita cikin madina, musamman gidajen Ansar
yana neman goyon bayansu don dawo da hakkinsa da kuma hakkin
matarsa da aka kwace.
Wannan mai yuwa shi yasa suka aiko da matansu zuwa wajen Zahra (s) su
bata hakuri sannan su bayyana mata yadda al-amura suka kasance har
abinda ya faru ya faru.
Amma bayan shigowarsu wajenta (a) sun ce mata: Yayi kike ya diyar
m an zo n All..(s), kamar yadda muka saba idan mutum ya zo wajen wani
wanda yake fama da rashin lafiya zai tambaye shi dangane da lafiyarsa da
kuma halin da yake ciki, amma Zahra (s) da ta tashi basu amsa sai ta fada
masu a zafin da take ji a cikin zuciyarsa ba a jikinta ba. Don haka ta fada
masu abinda ya fi damunta. Sai tace: Na rantse da All..na zama mai kin
duniyarku, da kuma takaici ga mazajenku.
Wannan shi ne yafi damanta, kuma ta damu da yadda mutanen Ansar suka
yi watsi da Ita, suka kuma zabe hanyar da bata dace ba, ko kuma suka ki
taimaka mata a lokacinda take bukatar taimakonsu.
Sai ta kara da cewa na yi wasti da su bayan na jarrabesu. Na kuma
kaurace masu bayan na ga cewa basu da anniyar kasancewa tare da ni,
bayan na gane hakikaninsu. Abin kunya ne a garesu da takubbansu
marasa kaifi.
A nan tana nufin cewa, abin kunya ne a garesu ta nemi taimakonsu amma
su kasa taimaka mata. Abinda kungiya ne garesu, su yi shiru a dai dai
lokacinda take kuka tana neman mataimaka wadanda zasu karbamata
hakkin ta, suna nan amm basu taimaka mat aba.
Sai ta cewa gaba da cewa: Sun yi watsa da gaskiya bayan sun kasance
masu daukarsa da muhimmanci.
Wato mutanen Ansar a farkon musulunci sun kasashen cikin wadanda
suke taimakawa gaskiya, suka sade ransu don ya kafu amma kuma a halin
yaznu sun fara was da shi, sabo sun kasa taimaka mata a lokacinda ta
bukaci hakan daga wajensu.
‘Suna dokan duwatsu wadanda basa da karfi, suna bata masunsu’.
Wannan saboda shi mashi dole ne ya kasance yana da karfi kafin ya huda
wani abu, don haka idan ya rasa kaifinsa ba za iyi wani amfani ba. Don ba
zai kashe makiyi ba.
“sannan suna kuskure wajen hukunta al-amura’ anan tana cewa, sauran
amincewarsu da shugabancinda da ba ta iyalan gidan manzon All..(s). da
kuma yin watsi da su a lokacinda suka bukaci taimakonsu.
“an batar da su da abubuwan wargi’ wato wadanda ba gaskiya ne ba,
batanda ya sabbaba musibu ga al-ummar musulmi na karnuka masu yawa,
kamar duk wanda ya karanta tarihin musulunci zai fahinci hakan.
Sannan ta karanta sura aya ta 80 na suratun Nisa inda All..T yake Magana
dangane da Banu Isra’ila da kuma yadda malamansu da shuwagabanninsu
suka batar da su, da kuma yadda hakan yana a matsayin baut ne a garesu,
kuma sun halakasu suna sane da hakan.
Sannan tace ‘Lalle na daura igiyar a wuyarsu’. A nan tana nufin ta gama
aikinta, ta kuma kafa hujja a kan muhajiruna da Ansar, a khudubar da ta yi
a masallaci, don haka a halin yanzu, hakkin abubuwan da zasu faru na
bata ya hau kansu. Don haka su zasu gamu da All..sannan al-ummun da
zasu zo nan gaba wadanda zasu gane kurakuransu.
‘Na sauke nauyin abinda ya faru a kan wuyarsu’ kuma ina da tabbacin
cewa zata ji kunya a ranar da ba zata amfanesu ba.
A nan tana nufin, wadanda suka aikata ba daidaiba a wannan lokacin, zasu
ji kunya a nan duniya sannan a lahira kuma zasu dauki alhakin duk barnan
da ya faru ko kuma zai faru da al-ummar musulmi a cikin wannan al-
ummar.
Dangane da wannan maganar ta Zahra(s), zamu fahinci haka a wannan
zamanin da muke ciki, inda duk tare da tursasawa iyalan gidan manzon
All..(s) da mabiyansu da aka yi a tsawon tarihi , sai gashi ba inda zaka je a
duniya sai ka samu Mabiya iyalan gidan manzon All..(s).
Kuma dukkan asiran da malaman tarihi da kuma sarakunan da suka
gabata suka boye sai sun fara bayyana. Hatta wadanda basu da ilmi mai
zurfi zasu fahinci kura kuran da wadannan magabata suka yi. Da kuma
barnan da suka yiwa addinin musulunci bayan wafatin ma’aikin All..(s).
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau na yau sai
kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi
wa barakatuhu.