Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (s) 11

11-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda

11-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin rumi. Ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasan ce tare da mu.

///..Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a shikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Hassan (a) jikan manzon All..(s) kuma limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), sannan dan Fatimah(a) diyar manzon All..(s) na farko.

Masu sauraro a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana cewa, Manzon All..(s) ya isar da manzancon ne a ranar Ghadir shekara ta 10 bayan hijira a wani wurin da ake kira Ghadir Khom dake tsakanin Makka da Juffa, wannan sanen nen wuri wanda ya kasance mikati ga mutanen Makka da kewaye. Inda ya nada Aliyu dan Abitalib (a) a matsayin Khalifansa, kuma wanda zai jagoranci al-ummarsa zuwa tudun na tsira a nan duniya da kuma Lahira. Sai dai al-umma ta yi watsi da su sun kuma kafirwa ni’imar da Al..ya yi masu.

Don haka sai All..ya mai da kungiyoyi suna yakar juna, ko wace kungiya tana alfahiri da abinda ya tara na mutane, yana kuma riye cewa su kadai ne suka kan gaskiya.

Mun ji yadda Imam Hassan (a) ya kafa hujja da ayar Ghadir ya kuma bayyana cewa bayan saukar ayar ne kakansa ya kama hannun mahaifinsa ya daga hannun babansa ya kuma ce duk wanda ni shugabansa ne to Aliyu shugabansa ne . Ya ubangiji ka jibance wanda ya jibance shu ka tabar da wanda ya tabar da shi.

Daga krashen mun ji Imam Hassan (a) ya fada masu cewa sun ji manzon All…(s), ko kakanda yana fadawa babana kan cewa: Matsayina da kai kamar matsayin Haruna da musa be sai babu annabci a bayana.

Hakika littafan tarihi suna dauke da wasu abubuwa da dama dangane da hadisin Ghadir da kuma yadda limamai daga iyalan gidan manzon All..(s) da malamansu suka yi ta kafa hujja da shi a tsawon tarihi.

Ammam al-ummar ta zabi wani abu daban ta kuma zabauwa kanta sabanin haka bayan ta fahinci abinda hadisin Ghadir ya kunsa.

Sannan bayan komawar Madina daga aikin hajji, manzon All..ya zauna wasu kwanaki sai aka umurceshi ya yiwa ma’abuta kaburbura a Baki’a. Sai ya kira Abu Mauhiban, wanda ya kasance maulansa ne wanda ya saye shi kuma yentar da shi, a lokacinda yazo a cikin dare, sai yace masa an umurce ni in yiwa mutanen makabartan baki’a istigfari, ina son ka rakani, sai Abu muhiba ya rakashi zuwa Baki’a inda ya tsaya ya kuma yi masu istigfari kamar yadda aka umurce shi.

Da farko ya yi sallama ga mamata da suke makabartan, sannan , ya kuma ce masu, kunji dadi da halin da suke ciki, Daga nan sai ya fara bada labarin bakar fitina wacce zata fadawa al-ummarsa a bayansa.

Sai ya fara addu’a yana cewa: Amincen All..su tabbata a gareku ya ku ma’abuta kaburbura, Lalle ku ina maku murna kan halin da kuke ciki, idan an kwatanta da halin da mutanen suke ciki a halin yanzu. Hakika fitinu kamar bangarorin duhun dare yana kan hanyar zuwa cikinsu, sun bin juja, duk wanda yazo daga baya sai yafi muni kan wanda ya zo gabaninta.).

A lokacinda Abu Mauhiban ya ji addu’ar manzon All..(s) da kuma abinda yayi magana na gabatowar fitina, sai ya fara gurin ina ma da ace ya mutu. Sai manzon All..(s) ya ce masa: Lalle ni an bani mabudan taskokin duniya da dawwa a cikinta sannan Aljanna, sai na  zabi haduwa da Ubangiji na, sannan Aljanna.)

Sai Abu Mauhiban ya ce masa: Iyaye na fansarka shin ba zata karbi mabudan taskar duniya ka dawwa a cikinta sannan Aljanna bayan haka ba?

Sai manzon All..(s) ya fada masa bukatarsa mai tsanani na haduwarsa da All.. sai yace masa{ Babu wallahi na zabi haduwata da All..) sannan ya nemi gafara ga ma’abuta makabartan Baki’a sannan ya juya ya koma gida.

A lokacinda manzon All..ya ga alamun wafati a kusan zuwa, sai yana son ya karfafa Aliyu (a) al-amarinsa a bayansa, sai ya tarawa Usama dan Zaidu runduna, wanda hakan zai nisantar da dukkan wadanda suke kodayin khalifanci daga madina a lokacinda zai yi wafati, sannan Amirul mumina(a) zai karbi jagoranci ba tare da wata matsala ba.

Don haka ya hada runduna karkashin jagorancin Usuma dan zaidu, sannan ya tura dukkan wadanda yake da tabbacin cewa suna kodayin khalifanci a bayansa su fita yaki tare da Usama dan zaidu. Manzon All..(s) ya tura  tare da Usama, dukkan manya-,manyan sahabbai daga ciki har da Abubakar da Umar da Uthman da Ubu ubaida dan Jarra, da bashir dan Sa’adu da sauransu.

Ya shugabantar da Usama dan Zaidu a kansu, wanda ya kasance dan shekara 17 a duniya ne.

Manzon All..(s) ya kulla tutar yaki ya bawa Usama dan Zaidu ne kwanaki 4 kafin karshen wata Safar na shekara ta 11 bayana hijira. Sannan ya fadawa Usaman, : Kaje inda aka kashe babanka, ka tattakasu da dawakanka, na shugabantar da kai wannan rundunar.

Ka kai hari kan mutanen ‘Abni” da sassafe, ga gaggauta tafiya saboda kada labarinka zuwarka ya isa kafin ka iso. Idan All..ya baka nasara a kansu ka, kada ka dade a cikinsu. …har zuwa inda yace : ka dauko masu baka labari, ko ta’a ina. Tare da kai, su rika baka labari.

Sai a ranar 28 ga watan Safar, sai rashin lafiyar manzon All..(s) yayi tsanani, kuma zazzabi ya rufe jikinsa. Tare da tsananin ciwon kai. Amma wasu suka ce zazzabin da kuma ciwon kan saboda abinci mai guban da ya ci a baya ne, a yakin Khaibara. Suka ce yana cewa : Har yanzun ban gushe ba anajin dandanon abincin da na ci a khaibara.

A lokacinda gari ya waye, sai ya ga wasu sahabbansa wadanda suka sabawa umrninsa, suna cikin Madina kamar yadda aka bashi labari.

Sai ya sake fita a ranar 29 ga watan safar ya sake kullawa Usama dan Zaidu tuka ya ce masa, ta tafi yaki da izinin All.. kan tafarkin All.., ka yaki kafirai).

Sai usama yak arbi tutan sannan ya mika shi ga Buraidatul Aslami, sannan ya je ya yi sansanin A Jurf kafin sauran mutane su taru su tafi da shi.

Sai mutanen sun yi ta jan kafa, sun ki fita tare da shi suna, jinkiri sosai, sai Umar ya fadawa Usama: Manzon All..(s) ya mutu kana a matsayin shugaba na?.

Sai suka fara yin korafi kan shugabantar da Usaba a kansu, musamman ganin cewa su, dattawa ne masu fararen geme, sannan usama kuma dan zaidu na Haritha ne wanda ya kasance yentaccen bawan manzon All..(s) wanda ya yenta shi.

Don haka sun yi ta jan kafa wajen hadewa da sauran rundunar Usama, kuma maganganunsu ya isa kunnen manzon All..(s).

A lokacinda ya ji sukarsu ga shugabancin Usama da kuma jan kafar da suke yi, sai rashin lafiyarsa ya karu, sannan ciwon kai ya rufe shi, ya kuma yi bakin ciki sosai kan hakan. Sai ya fito yana daure da kansa da wani kelle, yana kuma jin tsoron dabarar da yayi ba zai kai ga nasara ba.

Ya je masallaci ya hau mimbari a ranar 10 ga watan Rabi’ul awwal, ya bayyana bakin cikinsa da rashin tafiyarsu, da kuma sabawa al-amarinsa. Sai ya fara khuba yana cewa :

Ya ku mutane ! wani irin zance ne nake ji daga wajenku, dangane da shugabancin Usama, wallahi idan kunyi suka kan shugabancin Usama, to kun yi suka kan shugabancin babansa a baya, Na rantse da All… lallei ya cancanci shugabanci , kuma babansa ma ya cancance ta.

Sai ya sauka daga membari, ya koma gidansa yana cewa, ku tafi da rundunar Usama, ku aiwatar da rundunar Usama, All..ya la’ani wanda bai je tare da rundunar Usama ba.

Amma dukkan jawabai da kuma maganganinsu dangane da rundunar Usama, shiga zuciyarsu ba. Sai ma sun yi ta gabatar da uzuransu ga manzon All..(s) bayan dukkan maganganu masu zafi da ya fada dangane da rundunar Usama.

Don haka sun yi watsi da dukkan maganganunsa (s) dangane da rundunar Usama. Wanda ya sa Usaba yak asa tafiya. Har abinda ya faru ya faru.

Wanda yayi tunani a cikin abubuwan da suka faru a wancan lokacin zai fahinci wasu al-amura kamar haka.

01-Dagewar manzon All..(s) wajen ganin rundunar Usama ta tafi, hatta a lokacinda yake fama da tsananin rashin lafiya, da kuma la’anar da yayi kan duk wanda ya ki fita tare da rundunar Usaba, ya nuna cewa dabarar da yayi na fitar da dukkan wadanda suke kodayin shugabanci ko khalifanci a bayasa, dubarar ba za ta sami nasara ba. Don zai yi wafati sunan cikin madina. Zasu aiwatar da shirinsu na kwace khalifanci daga hannun Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a).

02- sun gano cewa idan sun bar Madina, sannan manzon All..(s) ya rasu, babu wanda zai yi maganar Khalifancin manzon All..(s) a lokacin, Amirulmi muminina (a) zai karbi khalifanci da sauki, sannan ko sun dawo ba za su iya yi masa tawaye ba.

03- Manzon All..ya sanya Usama dan zaidu kan shugabancin runduna ne, saboda idan ya dora tsoffi da kuma wadanda suka kashen shuwagabanni a cikinsu, to zasu yi amfani da wannan damar don cimma manufofinsu ta kodiyan khalifanci a bayansa.

Amma usama matashin ne, idan sun ce Aliyu matashi ne to Usama ma matashi ne.

Da wasu dalilai a dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments