Kissoshin Rayuwa: Sirar Fatimah Azzahra(s) 40

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’aini mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da lattafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Murtdha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na Maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon Allah(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) da muke mawo muku, mun tsaya inda muka fara kawo maku hadisin Imam Sadik (a) dangane da yadda wasiyar manzon Allah(s) ta kasance ga Aliyu dan Abitalib(a).

Mun bayyana cewa, kamar yadda ya zo cikin hadisin, mala’ika jibiriku ne ya sauko da wasiyar tare da wata jama’a daga cikin mala’iku, suka bukaci kowa ya fita daga cikin dakin sai Aliyu(a) sannan Fatimah(s) tana tsaye tsakanin labule da kofa.

Bayan haka mala’ika Jibirilu ya fadawa manzon Allah(s) ya zo da littafin daga Allah wanda a cikinsa alkawali ne da ya dauka tsakaninsa da shi, wanda kuma ya sanya mala’iku shaidu a kansa, a yanzu suna sun su shaida cewa ya mikawa Aliyu dan Abitalib(a) wannan alakawalin a matsayinsa na wasiyyinsa.

A lokacinda jibiru (a) ya fadi haka, sai Imam Sadik (a) ya ce: gabban manzon Allah(s)  suka yi karkarwa (don girman al-amarin.). Sai manzon Allah(s) ya ce:  Ya Jibirilu!: Ubangijina shi ne Amince, kuma amince daga gareshi yake, kuma gareshi ne amince yake komawa, ya yi gaskiya ya kyautata. Ka kawo littafin. Jibrilu (a) ya bashi, sannan ya umurceshi ya mika shi ga Amirulmuminina (a).

Sai yace masa ka karanta shi, sai (amirul muminina (a) ya karanta shi harafi harafi,

Sai manzon Allah(s) ya ce Ya Aliyu! Wannan shi ne alkawali tsakanina da Ubangijina, da kuma sharadinsa gareni, kuma amanarsa, kuma hakika na isar (da sakon musulunci) na yi nasiha na isar da amana!.

Sai Aliyu (a) yace: Kuma iyayena fansarka, ni shaida ne gareka, na isarwa da nasiha da kuma gaskata abinda ka fada. Kuma jina, da ganina da tsokar jikina da jinni na duk sun shaida maka.

Sai Jibirulu yace: Ni kuma ina daga cikin wadanda suke maku shaida bisa hakan. Sai manzon Allah(s) ya ce: Ya Aliyu! Ka karbi wasiyata, ka fahince ta, kuma ka lamuncewa Allah da ni kan aiwatar da abinda ke cikinta?  Sai Aliyu ya ce: Ee, iyayena fansarka, na lamunce maku cikata, kuma Allah shi ne mataimakina, da gamdakatar na kan aiwatar da ita.

Sai manzon All..(s) ya ce: Ya Aliyu ! Ina son in kafa shaida a kanka, kan na cikata a ranar kiyama.

Sai Aliyu Yace: Ee ka kafa shaida! Sai manzon Allah(s)  ya ce: Lalle Jibirilu da Mika’ilu su na a tsakanimmu a halin yanzu, tare da su akwai mala’iku makusanta, zan sanyasu shaida a kanka. Sai Aliyu yace: Su shaida, kuma iyayena fansarka ina kallonsu, sai manzon All..ya sanyasu shaida.

Yana daga cikin abubuwan da manzon Allah(s) ya shardanta masa, tare da umurnin Jibirilu daga Allah mai girma da daukaka, kan cewa:

Ya Ali! Zaka cika duk alkawulanda da suke cikinta (wasiyar) wanda ya hada da jibintar wanda ya jibanci Allah da manzonsa, da kuma barranta da kuma adawa ga wanda yake adawa da Allah da manzonsa, da baranta daga garesu, ta yin hakuri da hadiya fushi, bisa rasa hakkinka, kwace khumusinka, keta huruminka, ? Sai yace: Ee ya manzon All..(s).

Sannan Amirulmuminina (a) Ya ce: Na rantse da wanda ya tsaga kwaya, kuma ya kaga halittu. Hakika na ji Jibirilu (a) ya na fadawa annabi(s), ya ce: Ya muhammadu, ka fada masa lalle za’a keta huruminsa, kuma shi  hurumin Allah ne, kuma hurumin manzon Allah ne, da kuma cewa za’a jika gemunsa da danyen jinin kansa.

Sai Amirulmuminina (a) yace: na gigice a lokacinda na fahinci ma’anar kalmar daga amintacce Jibirilu sai na fadi a kan fuskata, sai na ce: Ee! Na yarda, na amince. Kuma ko da an keta hurumi, aka kashe sunnan manzon Allah(s), aka yayyaga littafi, aka rusa Ka’aba, aka jika gemu da danyen jinin kai, ina mai neman lada a wajen Allah  har abada, har sai na riskeka.

Sannan manzon Allah(s) ya kira Fatima da Alhassan da Alhussain (s) ya sanar da su kwatankwacin abinda ya fadawa Amirulmuminina(a) suka fadi abinda ya fada. A nan ne sai aka sanyawa wasiyar hatimi na zinari wanda wuta bai taba shi ba, sannan aka mikawa Amirulmuminina (a) wasiyar.

Wanda ya ruwaiti hadisin ya ce wa baban Alhassan (Alkazim (a): Iyaye na fansarka ba zaka ambaci abinda yake cikin wasiyarba? Sai yace: Sunnar Allah da sunnan manzonsa (s) ne. Sai na ce: A cikin wasiyyar akwai batun, zasu kwace su kuma sabawa Amirulmuminina(a)?

Sai ya ce: Ee na rantse da Allah kadan kadan, harafi harafi, baka ji zancen Allah mai girma da daukaka inda yake cewa

{Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani} Yasin 12.

Na rantse da Allah hakika manzon Allah(s)  ya fadawa Amirulmuminina da Fatima (a), shin baku fahinci abinda na gabatar maku da shi ba, kuka kuma amince da shi? Sai suka ce: Ee, kuma mun yi hakuri bisa duk abinda ya bakanta mana rai ya kuma fusatamu.

Manzon Allah (s) ya kasance a cikin sa’o’in da suka rage masa yana sanye da kansa a kan kirjin Aliyu (s), amma sai yana rungumar Fatima a kan kirjinsa sai ya cire ta, ya sake dawo da ita, alhali hawaye na kwarara daga idanunsa har sun jike gemensa, haka ma zanin gadon da yake kansa.

A cikin wannan halin Alhassan da Alhussain suka zo suna sumbantar kafafuwansa suna ta kuka da babban murya. Aliyu ya na son daga su daga kafafuwansa, sai manzon Allah(s)  ya ce masa: Ka barsu su sunsuneni ni ma in sunsunesu, su yi guzuri daga waje na, nima inyi guzuri daga wajensu, da sannu za su hadu da girgize-girgize da al-amura masu wuya, Allah ya la’anci wanda ya tsoratar dasu, ya Allah na mika maka kula da su da kuma salihan bayi.

A dayan bangaren Zahra (s) tana kuka a dai dai lokacinda babanta mai tausaye da soyayya yake dab da wafati, tana cewa: ya babana ba zaka yi mani magana ba,? lalle ina kallonka kana barin duniya?, ina kallon mala’ikun mutuwa sun kewaye da kai ko ta ina. Sai yace mata: Ya diyata lalle zan rabu da ke, amince ya tabbata a gareki.

A cikin littafin Kasful Gumma, sai manzon All..(s) ya ce mata: Ya diyata, ke  abin zalunta ce a baya na, kuma mai rauni a baya na, duk wanda ya cutar da ke ya cutar da ni. Kuma duk wanda ya nisantaki ya nisantani, wanda kuma ya sadar da zumunci da ke ya sadar da zumunci da ni, wanda ya yanke zumunci da ke ya yanke zumunci da ni, wanda ya yi maki adalci yayi mani adalci, don ke daga gareni kike ni daga gareki naki. Ke tsokace daga gareni da kuma raina da ke sassa na.

Sannan Yace: Ina karar duk wanda ya zalunceki daga cikin al-umma ta. Ba’a dade ba, sai Aliyu (a) ya tashi yana cewa: Allah ya girmama ladarku da annabinku, Allah ya dauki ransa zuwa wajensa.

Dagan an sai suka daga sauti da kuka ta ko ina, Zahra (s) tana cewa: Ya babana, ubangi ya kusanto da shi! Ya babana Aljanna Firdausi masaukinka, Ya babana  Jibirilu yana jajensa, Ya babana, ya karbi kiran Ubangiji, da ya kira shi.

Aliyu (a) yana fada: Ya manzon Allah(s). Sannan Alhassan da Alhusain suna fada Ya kakana ya kakana.

Masu sauraro a nan zamu dasa Aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan Allah ya kaimu, wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments