Kissoshin Rayuwa: Sirar Fatimah Azzahra (s) 42

42-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda su

42-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda su ka zo cikin alkur’aini mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da lattafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Murtdha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na Maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon Allah(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) da muke mawo muku, mun tsaya inda muka bayyana yadda Zahra (s) ta yi kuka mai yawa, kuka wanda baya misaltuwa bayan rabuwarta da babanta kuma manzon All..(s).

Al-amarin ya kai ga makobtanta sun kasa hakuri, sai suka hanata kuka, sai ta rika fita zuwa wajen shahidan Uhudu tana kuka a kusa a kabarin Hamza dan Abdullahin (s).

Sannan a lokacinda ta kasa saboda rashin lafiya, sai kuma ta fara zuwa, makabartan Bakiyya da kuma baitul Ahzan, wanda Imam Ali (s) ya kafa mata saboda ta ci gaba da kuka dare da rana.

Sannan masu sauraro a yanzun zamu fara magana wacce take da nauyin gaske, wanda kuma ya shafi akidummu da kuma addinimmu. Saboda abubuwa ne wadanda suka faru da iyalan gidan makon All..(s) bayan wafatinsa(s). Abubuwa ne wadanda zama sanadiyyar rarrabuwar musulmi zuwa shi’a da sunna daga lokacin har zuwa yau shekaru fiye da 1 400 da wafatin manzon All..(s). Har’ila yau abubuwan da suka faru a bayan wafatin manzon All..(s) yana da nasaba da halin da musulmi suke a yau a duniya. Kasksance da mamaya da mulkin mallakar da kafirai suka yiwa musulmi shekaru kimani 100 da suka gabata yana da nasaba da halin da musulmi suka sami kansu a yau a duniya.

Abubuwan da suka faru da Fatima da mijinta Aliyu dan Abitalib (s), da kuma sauran manya manyan sahabban manzon All…(s), dangane da shugabanci da kuma wanda ya cancanta ko kuma wanda manzon All..(s) ya nada a matsayin Khalifa a bayansa,(kamar yadda Shia suka yi imani da shi) shi ne ya yi sanadiyyar rabuwar kan al-ummar musulmi gida biyu wato shia da sunnan, kuma wannan rabuwar tana nan har yau shekaru 1400 bayan wafatinsa.(s).

Kuma wannan al-amarin ya kai ga wadannan bangarorin musulmi biyu sun yi ta kafirta juna, suka kuma zubar da jinin juna a tsawon tarihin addinin musulunci. Wannan al-amirin ya shafi dukkan bangarorin addini, kama daga sanin All..(tauhidi) da sifofinsa, da ibadu da fahintar al-amura daban daban a cikin addini.

Don haka fadin abubuwan da suka faru tsakanin sahabban manzon All…(s) da kuma iyalan gidan manzon All..(s) karkashin jagoranci Ali da Fatimah (s), al-amarin ne mai matukar nauyi da hatsari, duk da cewa gaskiya dole a fade shi, ko da kuwa wani bangare na musulmi ba zasu ji dadinn jin hakan ba.

Don haka mai yuwa musulmi da dama wadanda ba za su amince da abinda zamu fada dangane da abubuwan da suka faru ga Zahra (s) bayan wafatin babanta manzon All..(s) ba, don haka ne muka zabi mu kawo hujja ko shaida kawai  daga littafan Ahlussunna waljama’a, don littafansu hujja ne a kansu. wannan kuma yana iya bude kwakwalan wadanda suke son gaskiya su koma gareta. Wadannan littafa su zama makoma ga duk wani wanda yake son karin bayani da kuma fahintar gaskiyar abinda yake faruwa.

Atakaice abinda ya faru shi ne, jim kadan bayan wafatin manzon All..(s)   sahabban manzon All..(s) daga cikin Ansar, sun hadu a wani wuri da ake kira sakifa, wanda ya kasancewa wurin taronsu ne a jahiliyya, sun fito da shugabansu Sa’ad dan Ubada a matsayin wanda suke son su zaba a matsayin wanda zai gaji manzon All..(s) a matsayin Khalifa.

Sun taru sun fara tattaunawa sai wasu sahabban kuma suna masallacin manzon All..(s) kusa da gidan manzon All..(s) suna jirin abin da zai zo bayan wafatinsa (s). Sai Khalifa na biyu Umar dan Haddabi ya zo masallaci ya zare takobinsa yana cewa, kada kowa yace manzon All..(s) ya yi wafata, sai dai ya je ganawa da Ubangijinsa ne, idan ya dawo zai yayyanka, hannaye da kafafuwan munafukai wadanda suka ce ya rasu.

Sai ya sanya kowa cikin tsaro, ana cikin wannan halin sai ga Abubakar dan Abi kuhafa ko Khalifa na farko ya iso, ya shiga gidan manzon All..(s) ya je ya tabbatar da cewa manzon All…(s) ya rasu. Sannan ya dawo masallaci ya tara mutane yana masu magana, a cikin manganganun da ya yi, ya ..ya kuma mutane wanda yake bautawa Muhammadu, muhammadu ya rasu, wanda kuma yake abutawa All..to All..yana raye baya mutuwa.

Sai ya karanta aya, wacce a cikinta All..T yana cewa : {..Muhammadu bai kasance ba sai manzo, shin idan ya mutu ko aka kashe shi zaku koma daga duga duganku,? Duk wanda ya koma ga duga dugansa ba zai cutar da All..da kome ba, da sannu All..zai sakawa masu godiya}.

Sai khalifa Umar yace kamar bai taba jin wannan ayar ba, sai ya zauna a kasa. Ana nan a masallaci sai ga Abu abidullahi dan Jarrah daya daga cikin sahbban manzon All.,.(s) ya zo ya fadawa Abubakar da Umar wani abu a kunnensu, sai da shi da su biyu suka tashi da sauri suka ka kai kansu, Sakifah, inda suka samu wasu Ansar suna taro don zabar wanda zai zama Khalifan manzon All..(s) a cikinsu, kuma Sa’ad dan Ubada shi ne dan takararsu.

Dagan an saka shiga jayayya da su wato tsakanin Ansar da kuma Quraishawa wato Abubakar da Umar. Abubakar na cewa ya ku mutanen ansar kada ku fitar da wannan al-amarin daga Kuraishawa don muhammda daga cikinsu ne ya fito, don su ne makusantan sa, amma mun yarda ku zama waziyar wato mataimaka amma shugabanci namu ne.

Sa’ad dan Ubada ya saba masu, ana cikin wannan hayaniyar wannan ya fada wannan ya fada, sai Umar ya kama hannun Abubakar ya shinfida ya fara yi masa bai’a a matsayin khalifan manzon All.., sannan wasu suka biyo har zuwa mafi yawan wadanda suka halarci taron na sakifa, wanda bai fi mutane kimani 100 ba.

Amma Sa’ad dan Ubada ya ki amincewa da Abubakar, har ma yana cewa ba zai barsu ba sai har makamansa sun kare, sai ya bada umurni aka dauko shi aka maida shi gida saboda bai da lafiya a lokacin.

Khalifa Umar a lokacin Khalifancinsa, an nakaltoci yana fada: Lalle bai’ar Abubakar ba zata ne All..ya karemu daga sharrinta, kamar yadda Bukhari ya kawo shi cikin sahihinsa, JZ2 Sh 158, sharhin Nahjul Balaga na Ibn abil hadid Almutazili JZ3 sh26.

Dagan an sai suka fito suka kama hanyar masallaci, duk wanda suka hadu da shi, sai suce masa yayiwa Abubakar bai’a don an yi masa bai’a a matsayin Khalifan manzon All..(s) haka suka yi har suka isa masallaci, suka tilastawa duk wadanda suke wurin yiwa Abubakar bai’a.

A duk wannan lokacin Aliyu da sauran Iyalan gidan manzon All..(s) suna gidansa suna kukan rasuwarsa, sannan Aliyu yana ayyukan jana’izarsa.

A lokacinda Aliyu (a) ya gama, aikin jana’izar manzon All..(s), aka yi masa sallah, aka sa shi a makwancinsa, sai ya koma gidansa. Kafin haka Khalifa Abubakar ya samu bai’ar mafi yawan sahabban manzon All..(s) a cikin madina da kuma wasu kauyuka gewaye da shi.

Sai ya aikawa Aliyu dan Abitalib (a) kan ya zo yayi masa bai’a, sai Aliyu yace ba zai yi ba, saboda shi ya cancanci su yi masa bai’a.

Don haka akwai wasu sahabban manzon All..(s) yan kadan wadanda suka tare a gadan Aliyu da Fatimah (s) sun ki amincewa da shugabancin Khalifa a Abubakar daga cikinsu akwai Zubair dan Awwam, salman Alfarisa, Mikdada dan Aswad, Abubzar Algifari, Ammar dan yasir da sauransu.

Daga karshe bayan kimani mako guda da wafatin manzon All..(s) Khalifa Abubakar ya aikawa Aliyu dan Abitalin sako, da ya zo yayi bai, da shi da duk wadanda suka taru a gidansa, idan ba haka ba zai dauki mataki.

Wanda khalifa Abubakar ya aika don isar da wannan sakon shi ne Khalifa Umar, tare da wasu sahabban. Suka tunkari gidan Aliyu dauke da garwashin wuta a hanunsu.

A cikin littafin Alamun Nisa, JZ 2 shafi na, 1207, Da Uqdatul Farid, JZ2 sh250, da Tarihin Abul Fidah JZ1 shafi na 156.  Duk sun ce: Sai Abubakar ya aiki Umar zuwa wajensu (Aliyu da wadanda suke tare dashi) sai ya fadawa Umar: Idan sun ki ya yake su:

Sai Umar ya gabato zuwa gidan Zahra (s) ya na rike da wuta, da nufin ya kona gidan idan sun ki fita su yi bai’a, sai ga Zahra (a) ta zo kofan shiga gidanta, ta kuma gansu, sai tace: Ya dan Khaddabi ka zo don ka kona gidammu ne? sai ya amsa: Ee, sai in kun shiga karkashin abinda mutane suka amince da shi.

A cikin Tarihin Tabari, da al-imama wassiya na Ibn Kutaiba, da sharhin Nahjul Balaha na ibn abil hadidi duk sun cewa: Sai Umar yace a kawo garwashin wuta, wallahi ko inkona gidan a kansu, ko su fito su yi bai’a. …a wani hadisin ya ce (Umar) ko ku fito zuwa bai’a ko in kona.

To, Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..h ya kaimu, zamu dora daga inda muka tsaya wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments