38-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’aini mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da lattafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Murtdha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawai na maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////…. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon Allah(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) da muke mawo muku, mun tsaya a idan muka yi Magana dangane da yadda Zahra (s) ta kasance taskar ilmin mahaifinta manzon All..(s) musamman a abubuwan suka shafi mata. Saboda akwai tambayoyin da manzon All..(s) ya yi wa wasu sahabbansa dangane da mata, ba wanda ya san ansar sai Zahra(s), sannan da ya ji ta bada amsar tambarsa sai yace: Ita daga gareni ce.
Sannan munji yadda Zahra(s) take kiyaye hijabinta na musulunci a duk lokacinda na waje zai shigo wajenta, inda a nan ma manzon All..(s) ya yabeta. Sannan mun bayyana cewa mafi yawan matsalolin da mata musulmi da wadanda ba musulmi ba suke fama das u, suna tasowa ne daga reshin amfani da hijabin addinin musulunci. A duk lokacinda mata suka fara kiyaye hijabin musulunci zasu rabu da matsaloli da dama.
Haka kuma a duk lokacinda suka yi watsi da hijabin musulunci a nan kuma zasu hadu da matsaloli ba iyaka. Wannan halin zai ci gaba har zuwa lokacinda da su ka dawo kan hijabin na musulunci.
Sannan mun yi Magana dangane da addu’o’in da aka karbo daga wajen Zahra (s), suna da yawa sosai, amma mun zabi wasu daga cikinsu, daga ciki har da Du’aun Noor, mun kuma tarjamata da harshen hausa don fahintar abinda ke cikinta. Sannan munji yadda Zahra (s) ta bawa Salaman Alfarisi( r) wannan Addu’ar shi kuma ya rantse da Allah kan cewa ya bawa mutum sun fi dubu a Makka da Madina wadanda suke fama da zazzabi kuma sun warke da yardar Allah.
A cikin shrimmu na yau zamu shiga wani fasali mai muhimmanci a rayuwar Zahra(s) wanda kuma shine rasuwar mahaifinta cikamakin annabawa, kuma mafi soyuwar halittun Allah Muhamadu dan Abdullah (s).
Manzon All..(s) ya saba fadawa Zahra(s) al-amura masu zuwa na al-ummarsa da makomar wasu da dama daga cikin sahabbansa. Saboda matsayin da take da shi a wajen Allah da kuma mahaifinta, yakan kebeta da wasu labarai ko kuma al-amuran da al-ummarsa zata shiga ciki da kuma makomar hatta daddaikun iyalan gidansa daga ciki har da ita Zahrah (s). Ya fada mata abubuwanda da za su faru da ita bayan wafatinsa.
Manzon All..(s) ya fadawa al-ummarsa alamun tashin kiyama da al-amuran da za su faru a ranar kiyama, ya fadawa wasu daga cikin sahabbansa kan cewa ga yadda karshen rayuwarsu zata kasance a bayansa. Mun karanta yadda ya fadawa Jabir dan Abdullahin Ansari(r ) kan cewa zai yi tsawon rai har ga jikansa, mai suna muhammadul Bakir(a) wanda zai tsaga ilmi tsagawa, idan ya ganshi, ya isar da sallamansa gareshi, kuma ya san cewa mutuwarsa ta kusa.
Kuma haka ya faru Jabir ya rayu har sai da ya ga Imam Muhammad Albakir (a) dan Imam Aliyu zainul Abidina(a) dan Imam Husaine dan Fatima (s), a lokacinda ya je gidan mahaifinsa Imam Aliyu zainul Abidina a Madina. Inda jabir ya ganshi ya kuma isar da sallamar manzon Allah(s) sannan ya yiwa kansa ta’aziyyar mutuwarsa kuma bai dade ba ya rasu.
Hakama manzon Allah (s) ya fadawa Aliyu dan Abitalib (a) a cikin wata Khuduban da ya yi a cikin wata Sha’aban dangane da watan Ramadan mai tahowa, inda a lokacinda Amirul mumina (a) ya tambyeshi a karshen Khudubar, menene mafificin aiki a cikin watan Ramadan sai ya amsa da cewa: Shi kauracewa abubuwan da Allah ya haramta, sannan ya yi koka, sai Aliyu (a) ya tambayeshi me ya saka kuka ya manzon Allah (s), sai yace: Abinda zai faru da kai a cikin watan Ramadan a bayana, shakiyyi dan uwan wanda ya suki taguwar Annabi Salihu zai tsaga kanka da takobi sai jinin kanka ya jika gemunka. Sai Aliyu (s) ya ce: Amma zan tsira da addini na? sai yace: Zaka tsari da addininka.
Haka ma manzon Allah(s) ya fadawa Aliyu (s) zai yaki rundunoni uku a bayansa, masu, karya alkawari, azzalumai da kuma wadanda za su fice daga addini kamar yadda kori yake ficewa daga bakarsa. Kuma Aliyu (s) ya yakesu a lokacinda ya karbi khalifancin musulmi shekaru 25 bayan wafatin manzon All..(s). Ya yakesu a Busra a yakin Jamal, da Siffin da kuma Nehrawan.
Har’ila yau manzon Allah(s) ya fadawa Ammar dan yasin kan cewa, azzalumar kungiya ce zata kashe shi, yana kiransu zuwa aljanna suna kiransa zuwa wuta. Haka kuma ya faru Ammar dan Yashir (r ) ya yi shahada a yakin siffin a bangaren Aliyu dan Abitalib(s), a lokacinda Abul-Gadiya daga cikin sojojin Mu’awiya dan Abu sufyan ya sareshi da takobinsa bayan ya sha ruwa daga azuminda ya yi yina da shi.
Manzon Allah(s) ya fadawa wasu daga cikin sahabbansa makomarsu tun yana da rai, wasu alkhairi wasu kuma mummunar cikiwa. Ta yaya ba zai fadawa diyarsa Zahra (s) abinda zai faru da ita a bayansa ba? Ta yayi ba zai fada mata abinda zai faru da iyalan gidansa a bayansa ba?.
A baya mun karanta cewa manzon All..(s) yayi kuka a randa aka haifi jikansa Imam Hussain(a) sannan ya sha kuka bayan haka, yana cewa al-ummata zata kasheshi a bayana.
Don haka manzon Allah(s) ya fadawa iyalan gidansa abinda zai faru da su a bayansa, jim kan bayan wafatinsa. Ya fada masu irin musibun da zasu fada masu bayan wafatinsa. Ya fara daga Zahra(s) wacce kamar yadda zamu gani, a ranar wafatinsa sai da ya sake nanata mata abinda zai faru da ita, daga ciki ya fada mata: Ke ce zaki fara riskata daga cikin iyalan gida na.
An karbo hadisi daga dan Abbas yana cewa, a lokacinda wafatin manzon All..(s) ya kusa, ya yi kuka har sai da gemunsa ya jike da hawayensa, sai ake ce masa: Ya manzon All..(s) ! me ya saka kuka? Sai yace: Ina kuka saboda zuriyyata, da abinda masharranta daga cikin al-ummata zasu yi da su bayan wafatina, kamar ina ganin Fatimah (s) an zalunceta a bayana, tana kira! Ya babana! Ba wanda zai taimaka mata daga cikin al-ummata.
A lokacinda Fatima (s) ta ji hakan, sai ta yi kuka. Sai manzon All..(s) yace mata: Kada kiyi kuka ya diyata: Sai tace: Bana kuka don abinda zai faru dani a bayanka, sai dai ina kuka saboda rabuwa da kai ya manzon Allah(s).
Sai yace mata: Ina maki bushara ya diyar Muhammadu (s), kace na farko daga cikin dangina da zai fara haduwa da ni.
A wani hadisin Ibn abbas yana cewa ya ji manzon Allah(s) yana fada dangane da Fatimah(s)…kuma a lokacinda na ganta (Fatima) sai na tuna da abinda za’a yi da ita a bayana, kamar ina ganinta, kaskanci ya shiga gidanta, an keta huruminta, an kwace hakkinta, an hanata gadonta, an karya awazanta, an bararda cikinta, tana kira, tana cewa: Ya Mohammad, ba wanda zai amsa kiranta, kuma tana neman taimako, ba wanda zai taimaka mata. Ba zata gushe ba tana cikin bakin ciki da bacin rai tana kuka a bayana, tana tunuwa da yankewar wahayi daga sauka a cikin gidanta, a wani lokacin kuma tana tunawa da rabuwa da da ni, sannan idan dare yayi tana kewar muryata, wacce ta saba ji idan ina tahajjudi da Alkur’ani mai girma, sannan ta ga kanta kaskantacciya bayan daukaka da take da shi a rayuwar mahaifinta….har zuwa karshen hadisin.
Masu sauraro saboda kurewar lokaci a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan Allah(s) ya kaimu. Wassalamu alikaum wa rahamatullahi wa barakatuhu.