Kissoshin Rayuwa: Sirar Farimah Azzahra (s) 43

43-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

43-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’aini mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da lattafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Murtdha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na Maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon Allah(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) da muke mawo muku, mun tsaya inda muka fara Magana kan yadda wasu sahabban manzon All..(s) jim kadan bayan wafatin manzon All..(s) suka fara jayayya a tsakaninsu kan wanda zai maye gurbinsa a matsayin shugaban al-ummar musulmi, wannan duk da cewa kwanaki 70 kafin wafatinsa ya nada Aliyu dan Abitalib(a) a wani wuri da ake kira Gadir tsakanin Makka da Madina bayan ya kammala hajjin bankwana a matsayin wanda zai zama khalifansa a bayansa.

Da farko khalifa Umar ne ya zare takokinsa ya hana kowa fadar cewa manzon All..(s) yayi wafati a masallacin manzon All..(s). sannan bayan da Abubakar ya zo sai ya shiga gidan manzon All..(s) ya fita sai ya je masallaci ya gabatar da shahrerren khudubarsa inda yake cewa, wanda yake bautawa Muhammadu to Muhammadu (s) ya rasu wanda kuma yake bautawa All..to All..yana nan baya mutuwa.

Sannan suka je sakifa suka yi ta jayayya da Ansar wadanda suka taro don zaben Sa’adu dan ubada a matsayin Khalifa, amma daga karshen sun sami nasara a kansu inda Umar ya fara yiwa Abubakar bai’a sannan sauran suka biyo, amma shi Sa’adu yace ba zai taba binsu ba sai makamansa sun kare.

Sannan mun ji yadda aka yiwa yiwa manzon All..(s) sallar Jana’iza ta musamman, da kuma yadda kammaninsa ya bambanta da sauran musulmi. Malaman tarihi na Ahlussun sun kawo a cikin littafnsu yadda Aliyu(a) da wasu daga cikin sahabban manzon All..(s) suka ki bai’a wa Khalifa Abubakar, kuma yana ganin hakkinsa ne aka kwace, don haka shi yafi cancanta a yi masa bai’a.

Wannan al-amarin ya kai ga Khalifa Abubakar ya aiki Umar tare da wasu sahabban manzon All..(s) da su je su fitar da Aliyu (a) daga gidansa da karfi idan shi da wadanda sule tare da shi suka ki a yakesu.

Umar ya na rike da wuta a hannunsa, ya tunkari gidan Zahra(s), sannan da ta ganshi sai ta tambaye shi, Ya dan Khaddabi! ka zo don ka kona gidammu ne? sai ya amsa: Ee, sai in kun shiga karkashin wanda mutane suka amince da shi.

A wani hadisin a lokacinda ya fadi haka, wani daga cikin wadanda suke tare da shi yace masa akwai Fatimah a cikin gidan, sai Umar ya amsa da cewa: ko da kuwa Fatimah tana ciki.

Ibn Kutaiba ya kawo a cikin littafinsa Al-imama wassiyasa a shafi na 19. Yana bayani kan yadda bai’ar Aliyu(a) ga Abubakar ta kasance bayan wafatin manzon All..(s).

Ya ce Abubakar ya nemi wasu sahabban manzon All..(s) wadanda suka ki masa bai’a sai ya samesu a wajen Aliyu dan Abitalib (s) wato a gidansa, sai ya aiki Umar zuwa wajensu. Ya zo ya kirasu, daga wajen gidan Ali (a), sai suka ki fita, sai yace a kawo masa itatuwan a kunna wuta, sai yace: na rantse da wanda ran Umar ke hannunsa ko ku fito ko kuma in kona gidan, da duk wanda ke cikisa.

Sai aka ce masa ya baban Hafsa: Lalle akwai Fatimah a cikin gidan, sai yace: ko tana ciki.

Sai yace sai suka fito suka yiwa Abubakar Bai’a, sai Aliyu (a), yace: na sha alwashin ba zan gushe ba sai na hada alkur’ani mai girma rubutaccensa,( don haka b azan yi bai’a ba).

A cikin wannan halin sai Fatimah (s) ta fito a kofar gidata tana cewa: Ban taba ganin mutane wadanda suka aikata mummuna abu da kuka aikata ba. Kun bar Jana’izan manzon All..(s) a gabammu, sannan kuka je kuka yanke al-amarinku kamar yadda kukesu, baku nemi izinimmu ba, kuma baku bamu hakkimmu ba.

Wani mawaki Muhammad Hafiz Ibrahim yana fada a cikin kasidarsa mai suna Umariyya, yana cewa:

Da zancen Umaru Ga Aliyu-wanda ya ji ya daukaka, haka ma wanda ya fadeta

Zan kona gidanka bazan bar Kowa cikinsa ba- Idan dai baku yi Bai’a Ba, Ko da diyar Mustafa na cikinsa

Ba wani wanda ya fadeta sai baban Hafsatu – A gaban Mayaki dan Adnanu mai kare ta.

Wannan kasidar tana tabbatar da cewa Khalifa Umar yayi barazana zai kona gidan Zahra da Ali(s) idan da shi  da wadanda suke cikin gidansu basu yi bai’a ba.

Amma me ya faru sun fito sun yi bai’ar ne ko kuma an kona gidan.? Malaman tarihi sun tabbatar da cewa Aliyu dan Abitalib yaki yiwa Khalifa Abubakar bai’a har zuwa watanni 6, don haka sanadiyyar haka an kona kofar shiga gidansa a lokacin.

A cikin ruwayar da Ibnu Jarir Attabari ya kawo, yace: Jarir ya karbo daga Mughira daga Ziyad dan Kulaib yace: Umar dan Khaddabi ya zo gidan Aliyu, a lokacin Zubair da Talha suna cikin gidan Aliyu, da wasu mazaje daga muhajirun, sai yace: Na rantse da All..sai na kona gidan nan a kanku ko kuma ku fito ku yi bai’a, sai Zubair ya fito da takobinsa a zare a hannunsa, sai yayi targade sai takobinsa ya fadi, sai suka yi wof a kansa suka kama shi suka fitar da shi daga gidan… har zuwa karshen hadisin.

Sannan sharistani ya ruwaito cewa, Lalle Umar ya daki cikin Fatima (s) a ranar Bai’a, har sai da ta zubar da cikinta, na danta mai suna Musinu. Yana fada: Ku kona gidanta da wanda ke cikinsa. Ba wanda yake cikin gidan sai Fatima da Aliyu da kuma Alhassan da Alhussain(a).

A cikin lisanul Mizan na ibn Hajar Askalani yana cewa: Lalle Umar, ya ture Fatima (a) da kafarsa har sai da ta yi barin cikin danta Muhsinu. Sannan Ibn Jazzabah ko Kharzazabah: Yace: Zaid dan Aslamu ya ce: Na kasance cikin wadanda suka dauki itatuwa don kona gidan Fatima(s) tare da Umar, mun je har kofar gidan, a lokacin, Aliyu tare da mutanensa sun ki su yi bai’a, sai Umar yacewa Fatimah: Ki fita daga gidannan ko in kona shi da wanda yake cikinsa. Sai ya ce (ibn Aslama): A cikin gidan akwai Aliyu da Fatimah da Alhassan da Alhussain(a) da wasu jama’a daga cikin sahabban manzon All..(s)….   

Sai Fatimah (s) ta ce wa Umar: shin zaka kona yaya na? Sai yace: Ee, na rantse da All..ko su fito su yi bai’a.

Wannan kadan kenan daga abinda ya zo dangane da wannan al-amari a cikin littafan Ahlussunna waljamaa, wanda yake son Karin bayani ya shiga cikin littafan tarihi zai ga Karin bayani ko kuma fiye da abinda muka kawo.   

Bayan abinda muka kawo na babuwan da suka faru bayan wafatin manzon All..(s) zamu iya fahintar yadda wasu sahabban manzon All..(s), suka yi da iyalan gidan manzon All..(s) a bayansa. Zamu fahinci cewa wasu daga cikinsu basu kiyayewa manzon All..(s) huruminsa a cikin diyarsa Fatimah (s) ba. Basu kiyaye masa huruminsa a cikin keta hurumin gidan diyarsa Zahra (s) ba.

Banda haka basu kiyaye masa huruminsa dangane da wasiyyinsa, kuma surukinsa Aliyu dan Abitalib (a) ba. Basu kiyaye masa huruminsa a cikin jikokinsa Alhassan da Alhussain(a) ba.

Banda haka munji yadda wasu daga cikinsu su suka yi barazana kona gidansu, ko kuma sun cutar da iyalan gidan manzon All..(s) gaba dayansu, bayan wafatinsa da yan kwanaki. Sun yi barazanar kona diyarsa Fatimah, da mijinta da yayanta tare da wadanda suke tare da su a cikin gidanta.

Zahra’u (s) bata tsammanin za’ayi mata haka bayan wafatin mahaifinta ba, duk da cewa ya gaya mata za’a yi mata hakan. Amma, ji daban gani kuma ya fi ji. Ance gani ya kori ji.

Munji yadda wasu suka fada cikin gidanta ba tare da izininta ba, alhali a lokacinda manzon All..(s) ya na da rai, idan ya zo kofar gidan yakan yi sallam har sau uku idan ba’a amsa masa ba sai ya koma ba zai shiga ba. Sai gashi ko kasar Kabarinsa bai bushe ba, an keta hurumin wannan gidan an shiga ba tare da sallama ko neman izini ba.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments