Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin romi. Ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu saurarozasu kasan ce tare da mu.
///… Masu sauraro, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun fara bayyana maku iran matsayin da Imam Hassan (s) da kuma dan’uwansa Immam Hussain suke da shi a wajen All..T da manzonsa (s), mu yi maganar cewa, inda ya bayyanasu a matsayin samarin Aljanna, sonsu sun sa, kiyayya da su kiyayya ga Al..da manzonsa, kamar dai yadda ya kasance da mahaifiyarsu Fatimah (s). Mun kawo Hadisi inda manzon All..(s) yake fada dangane kaninsa Imam Hussain (a) kan cewa, shi limamina ne, dan limami ne, dan uwan limami ne, sannan mahaifin lilamai 9 , wato daga yayansa da zurriyarsa. Kun kawo sunan lamaman wadanda suma suna daga cikin wadanda All..ya tsarkakesu ya tafiyar dadauda a garesu tafiyarwa.
Har’ila mun ji yadda manzon All..(s) yakan je masallaci damam Hassan (a) sai yak an kan kakansa yana wasa sannan shi kuma ya bar shi yana wasa sai har ya gaji, ya sauka, sannan yadaga kansa daga sujuda. Don bayansan a bata masa wasansa.
Munji yadda ya gadar da su halayensa a lokacinda mahaifiyasu Fatima(s) ta zo da su wajen kakansu a rashin lafiya ta karshe da ta sameshi, sai ya gadarwa Imam Alhussan kamani da hakurinsa, sannan ya gadar da Alhussain Jaruntansa(s).
Ya ce: wanda ya sosu ya so shi ya so All..zai sa su a aljanna, sai sa a aljanna, wanda kuma yakisu ya ki shi ya ki All..zai sa su a wuta.
Idan mun ci gaba zamu ji wasu kari daga Shirin matsayin Imam Alhassan (a) da kuma Alhussain (a), wanda manzon All..(s) ya fada dangane da su, ammah da khassa.
Da farko Imam Hassan (s) shi ne jikan manzon All..(s) na farko wanda ma’asumai suka yi tarbiyyarsa.
Ya sami tarbiyya daga kakansa manzon All..(s) kai tsaye, wato ya tashi a gidan wahyi, sannan tsakanin iyaye dukkaninsu tsarkakku ne, ba abinda yake fita daga wajensu sai Alkhairi, ba wani wanda ya sami tarbiya a cikin dukkan al-ummar musulmi kamar shi da kuma dan’uwansa Imam Hussain (s). don dikkan wadanda suka yi masu tarbiya masumai ne. don haka ba wanda ya sami damar samun tarbiyyar manzon All..(s) kamar shi da dan’uwansa Imam Hussain (a).
Don haka tun suna kanana suka dauki halayen kakansu da iyayensu na kirin mutane da kuma shiryatar da su zuwa hanya madaidaiciya, da hikima da kuma wa’azi mai kyau.
An ruwaito cewa, Imam Hassan da dan’uwansa Imam Husain (a) wata rana suna kanan yara, amma sai suka ga wani dattijo wanda bai iya alwala ba, wanda da kai tsaye suka fada masa bai iya alwala ba, dai za ice ta yaya ku kananan yara kuka iya al-awala amma ni tsoho ban iya ba. Sai suka yi wata dabara don gyarawa wannan dattijo Alwalarsa. Sai suka fada masa ya kai dattijo. Sai suka kirkiro jayayya atsakaninsu a gaban wannan dattijon, sai wannan ya fadawa wannan baka iya alwala ba, sai dayan kuma ya kia ne baka iya alwalaba. Sai suka bukaci dattijon ya zama mai hukunci a tsakaninsu, don a gano waye bai iya alwala ba.
Sai dayansu yayi alwala irin ta dattijan, dayan kuma yayan alwalan da ya dace: da suka yi, sai dattijon ya ga dayansu yayi alwala irin tasa, a yayinda dayan kuma yayi alwalan mai kyau. Sai tatijon ya fahinci cewa shi suke son su yi wa gyra.
Sai yace masu yak u shuwagannina dukkanku kun iya alwala, dattijon Jahili ne bai iya alwala ba. Hakika ya koyi alwala daga wajenku. Ya tuba a hannunku, ….) har zuwa karshen hadisin wanada Biharul Anwar Jz 10 ShFi 89.
Wannan ya nuna irin yadda halaye kakansu da iyayensu suka yi tasri a tarbiyan da suka samu a wajensu.
Malaman tarbiyya sun bayyana cewa yara suna daukar halaye daga iyayensu ko wadanda suke masu tarbiyya da farko a matsayin taklidi ko kuma koikoyo ne, amma wannan koikoyon a hankali zai zama dabi’a, da kuma halayensu. Wannan shi ne muhimmancin samun tarbiyya a wajen masana da malamai, ko wajen shuwagabannin halittu, manzon All..(s) da wasiyansu da kuma gidan wahayi.
Saboda irin yadda Imam Hassan (s) ya dauki halayen kakansa manzon All..da kuma fahintarsa, har ya ga duk abinda ya ji ya ji a wajensa ko kuma ya gani ya rikeshi a kansa, idan ya koma gida wajen mahaifiyarsa Zahra (s) sai ta tambaye shi abinda ya ji babanta ya fada da abinda ya gani a masallaci, sai ya dawo da su gaba daya a kasa. Don haka ya zama wasila ta karaawa mahaifiyarsa sani.
Don haka yana haddace dukkan ayoyin alkur’anin da manzon All..Ya karanta a masallaci ko a wani waje, ya dawo ya fadawa mahaifiyarsa. Sai ita kuma ta fadawa Amirulmuminina (a) abinda aka yi a massalci, ko abinda babanta ya fada, sai yayi ta mamakin hakan, sai yace mata daga ina kika san hakan, sai tace: Daga da na hassan.
A wasu lokuran Amirul muminina (a) yakan boye a wani lungu a cikin daki don jin abinda Imam Hassan zai fadawa mahaifiyansa Zahra idan ya dawo daga masallaci ko daga wajen kakanka, sai ya zo ya fada mata duk abinda ta ji, wajen kakanta.
Sai Imam Hassan ya zo ya fadawa mahaifinsa dukkan ayoyin da kakaknsa ya fada a masallaci kamar yadda ya saba, sannan jikinsa ya kada saboda ayoyin da yake karantawa, sai ya tsaya ya kasa magana. Sai Zahra(s) ta ce masa: Ya da na me ya sa jikinka ke kadawa idan kana karanta ayoyin alkur’ani,? Sai yace: Ya ummah! kada kiyi mamakin abinda yake faruwa da ni, saboda wani babba yana kula da nai. }.
Wannan a karan kansa ya nuna cewa yana fahintar al-amura sosai, wato abinda tsaro a wata ayar da kakansa ya karanta masa, sai jikinsa ya kada, don yana fahintar ma’anar ayoyin ba haddacewa kawai yake yi ba, a’aa yana fahintar ma’anoni masu zurfi da suke cikin ayoyin. Kuma wannan ya nuna cewa duk tare da karancin shekarunsa(s) All..ya na sana masa al-amura da dama, wanda manyan-manya malamai masu tsorin All..ma, sai wanda yake da rabo ne yake samun wana abu dan kadan, daga abinda iyalan iyalan gidan annabta suke suke samu.
Wannan ya zo dai dai da wani hadinsi inda manzon All..(s) fada dangane da wasinsa kan cewa (..an arzutasu da fahintata da ilmi na..).
Idan baku manta ba, a sirar manzon All..(s) mun kawo maku wani hadisi daga Imam Ali (s) yana cewa a wata khudubarsa, mai tsawo yana fada dangane da manzon All..(s)..(….hakika, All..ya hada shi da wani ma babba daga cikin mala’ikunsa, tun lokacinda aka yayi shi, yana nuna mamsa halaye masu kyua..) har zuwa karshen hidisin. Don haka, wasiyansa ma haka suke.
Imam Hassan (a) ya haddace abubuwa da dama daga wajen manzon All..(s) yana dan shekara 4 a duniya, ga wasu hadisan da aka ruwaito daga wajensa yana yaro.
01-Imam Hassan (s) ya ce manzon All..(s) ya sanar da ni kalmomin da zan fada a kunutu na Ra’ka’ar witiri: Allahumah dini fi man hadaita..Ya Ubangiji ka shiryar da ni cikin wadanda kake shiryarwa, kuma ka gafarta mani cikin wadanda kake gafartawa, kuma ka jibanci al-amarina cikin wadanda kake jibantan al-amarinsu, kuma ka sa albarka a cikin abunda ka ba ni, kuma ka kare ni daga sharrin abinda ka hukunta, to lalle kana hukunci, kuma ba mai hukunci a kanka, kuma Lalle wanda ka jibanci al-amarinsa ba zai kaskanta ba, albarka ta tabbata a gareka, Ya Ubangiji, Madaukaki) Sahihu Tirmizi ya kawo wannan hadisan a JZ 01 SF 93.
Hakama Hakim Nishaburi a cikin Mustadrak dinsa MJ 3 Sh na 172.
02-Umair dan Ma’amun ya ruwaito hqdisi: Yace: na ji Hassan Dan Aliyu dan Abitalib (a) yqnq ce wa: Wanda yayi sallar asubaha, ya zauna a inda yayi sallar, har rana ta fito, hakan zai kasance masa, kariya daga shiga wuta, ko yace, maraba da wuta.
Usdul Ghaba 2/11.
03-wasu daga cikin sahabansa suka ce masa9q0, me zaka tuna daga manzon All..(s) ka fada mana? Sai yace: Na dauki dabino guda, daga dabinan sadaka, sai ya fito da shi daga bakina hatta da yawun da ya garwaya da shi, sai aka ce masa, ya manzon All.. me ya faru da wannan dabinon? Sai yace: Mu iyalan gidan Muhammadu (s) sadaka bata halatta a garemu.
04-An tambayi Imam Hassan (s), dangane da abinda yaji daga manzon All..(s): Sai ya ce: Na ji shi yana fadawa wani mutum: Ka bar abinda kake kokwantonsa, zuwa ga abinda baka kokwanto, don lalle shi sharri, kokwanto ne, sannan Al-khairi nutsuwa ne.
05-Imam Hassan (a) ya fadawa sahabbansa, dangane da halayen kakansa manzon All..(s) da kuma sirarsa. Sai yace: Manzon All..(s) ya kasance, idan wani ya roke shi wani abu baya mayar masa, sai da abunda yake bukata, ko kuma da abinda ya sawwaka na zance.
06-Imam Hassan (a) yace: Ku kira mani shugaban Larabawa-yana nufin Aliyu- Sai A’isha ta ce masa, ba kaine shugaban larabawa ba, ? sai Yace: Ni shugaban bani Adama ne Aliyu kuma shugaban Larabawa. Sai aka kira shi, a lokacin ya zo gabansa, sai ya aika a kira Ansar, a lokacinda suka taru, sai ya juya zuwa wajensu yana mai cewa:
Ya ku mutanen Ansar, shin ba zan nuna maku wani abu ba, idan kun yi riko da shi ba zaku bata ba har abada a baya na? . Sai suka ce, ee ya manzon All..ka fada mana, : Ga wannan Akiyu, ku soshi da so na, ku girmamashi don girmana, To Lalle Jabra’il ya fada mani da abinda na fada muku, daga wajen All..mai girma da daukaka. Malaman hadisa da dama sun ruwaito wannan hadisin daga wajensa.
Wannan duk tare da karancin shekarunsa (a). wanda yake nuna cewa a ido ne kawai shi yaro, amma a hakikaninsa yana fahintar duk abinda yake faruwa, yana kuma kiyaye koma fiye da yadda wasu manya-manya mutane suke fahinta.
Wannan kadan Kenan daga cikin hadisan da Imam Hassan(a) ya ruwaito kai tsaye daga manzon All..(s). Hadisai wadanda shi da kansa ya ji ko ya gani ya kuma rike abinda manzon All..(s)
Wannan duk da cewa manzon All..(s) ya yi wafati Imam Hassan (a) bai fi shekaru 7 a duniya ba. Kuma kamar yadda muka fada a baya yakan haddace maganganun manzon all..(s) a gidansa a ko a masallaci ya dawo gida wajen mahaifinsa Fatimah (s) ya fada mata duk abinda yaji wajen manzon All..(s). Kuma a wani lokaci sai ta ga cewa yana karkarwa yana figishi saboda tsaron All..da kuma abinda ya fahinta na abinda ya ji wajen kakansa manzon All..(s).
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.=======67