Kissoshin Rayuwa Fatimah (s) 60

Assalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo

Assalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana Jalaluddeen Ruma ko kuma dai  cikin wasu littafan Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) shuwagabannin samarin Aljanna, da muke kawo maku, `mun tsaya inda muka kawo maku karshen Khudubarta (s) a gaban Khalifa na farko a kuma cikin masallacin mahaifinta manzon All..(s).

Mun ji irin tasirin da Khudubar ta yi a cikin sahabban manzon All.. (s) musamman a cikin mutanen Madina ko Ansar. A lokacinda Khalifa na farko ya ga irin tasirin da khudubar ta yi, sai ya sake hawa kan mimbarin manzon All..(s) ya sake yin Khuduba, inda a cikinta ya gargadi mutanen Ansar kan cewa ya ji labarin abinda wasu wawaye daga cikinsu suka fada, amma ba zai yi ammafani da karfi a kansu ba, saboda sune suka taimakawa manzon All..(s) a lokacinda ya yi hijira daga Makka zuwa Madina, amma zai yi shiru matukar ba’a taba shi ba.

A cikin khudubar ya zargi Amirul muminina (a) da ta da fitina bayan an dusheta, kuma yana amfani ko kuma neman taimakon raunana ko mata don cimma manufofinsa.

Sannan ya sifantasu da abubuwan da basu  dace ba, kuma mun zabi rashin ambaton hakan a cikin shirimmu.

Sai dai mun bayyana cewa Ummul Muminina Umma Sallama ( R) matar manzon All..(s) ta mayar masa da martani a lokacinda ta ji abubuwan da ya Fada dangane da Zahra da Mijinta Imam Aliyu (a).

Sheikh Jamaluddin Ashami ya kawo a cikin littafinsa Addurrul Nazim, yana cewa. Bayan khudubar Fatimah (s) a masallacin manzon All..(s) da kuma tasirin da ta yi a cikin sahabban manzon All..(s) musamman a cikin mutanen Ansar, Khalifa na farko ya sake hawan mimbari ya kuma yi khuduba inda a ciki ya amfani da kalmomin da  muka kawo a baya dangane da Imam Ali da kuma Fatima (a).

A lokacinda labari ya kai kunnen Ummu Salma (r )  matar matar manzon All..(s) sai ta fusata sannan tace: Shin waye zai fadawa Fatimah (s) hakan?. Na Rantse da All..ita hurul inice a cikin sifar mutane, tsarkakakkiya, daga dauda, kuma ta tashi a gaban mutane masu tsarki, sannan mala’iku ne suke kawo mata abinci, sannan ta rayu a cikin mata masu tsarki, sannan ta sami mafi kyawun tarbiyya. Shin kuna tsammanin manzon All..(s) zai hanata gadonta sannan ba zai fada mata ba?. All..ta’ala na fada, (kuma ka gargadi danginka na kusa} sura ta 26:214.

Ko kuna ganin ya gargadeta sannan ta sabawa gargadinta ne? Ita ce mafificin dukkan mata, kuma ita ce mahaifiyar shuwagabannin matan Aljanna, sannan wacce ake kwatantawa da Maryam(a), sannan All..ya cika sakonninsa gaa bil’adama da mahaifinta,  kuma yakan yi duk abinda zai iya yi don neman yardarta da kuma kwantar da hankalinta. Ku yi hankali manzon All..(s) yana gininku, sannan zaku koma zuwa ga All..T , a sannan zaku sani.

Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, saboda wannan maganar tata ce, aka hanata rabonta na kudaden da aka saba bata a ko wace shekara.

Daga nan sai Zahra (s) ta koma gida, ta sami cewa Amirulmuminina (a) ya na dakon dawowanta, a lokacinda ta shigo gida ta zauna, sai tace : Sai ta fada masa abubuwan da suka faru, da kuma irin damuwarta da yadda suka dage wajen hanata hakkinta, da kuma yadda suka yin isa daga karban gaskiyar abinda take fada.

Sai Imam Ali (s) yace mata: Ina rokin All..ya kareki daga duk wat acuta, makiyanki ne zasu halaka. Don haka ki kwantar da hankalinki.

 Ya ke diyar zabebbe yar gidan annabci, ki kwantar da hankalinki, idan abinda zaki rayu da shi ne kike bukata, wannan All..ya rika ya lamunce maki rabonki, ba wanda ya isa yah ana ki. Kuma abinda All..ya tanadar maki a can ya fi maki kan abinda aka kwace a hannunki.

Amma alokacinda matan Ansar suka ji abinda ya faru da Zahra musamman bayan khudubarta, sai suka aiko yi Magana da mazajensu kan cewa su je su nemi afawarta (s) sai wasu jama’a daga cikins (s) don neman afwata. Sai dai bamu sani ba, mazajenne suka umurci matansu, su shiga wajenta,

A lokacinda suka shiga wajenta (s) sun fada mata cewa: Ya shugaban mata, da Baban Hassan ya yi mana Magana kan wannan al-amarin kafin a kulla shi, da ba zamu zabi waninsa ba.   

Sai tace masu: ku barni da halin da nake ciki, baku da wani uzuri bayan abinda kuka yi, da kuma kuskuren da kuka aikata.

A wasu ruwayoyin an bayyana cewa matan Muhajirun da ansar ne suka shiga wajen Zahra (s) kuma suna da yawa, ba’a san wanda ya bada shawarar a su zo su bata hakuri ba, amma kuma magangandu da dama sun yadu a cikin madina dangane da Khudubarta da kuma yadda ta kare da  shuwagabannin gwamnatin lokacin. Musamman bayan da Amirulmunina (a) ya zagaya da ita cikin madina, musamman gidajen Ansar yana neman goyon bayansu don dawo da hakkinsa da kuma hakkin matarsa da aka kwace.

Wannan mai yuwa shi yasa suka aiko da matansu zuwa wajen Zahra (s) su bata hakuri sannan su bayyana mata yadda al-amura suka kasance har abinda ya faru ya faru.

Amma bayan shigowarsu wajenta (a) sun ce mata: Yayi kike ya diyar                    m an zo n All..(s), kamar yadda muka saba idan mutum ya zo wajen wani wanda yake fama da rashin lafiya zai tambaye shi dangane da lafiyarsa da kuma halin da yake ciki, amma Zahra (s) da ta tashi basu amsa sai ta fada masu a zafin da take ji a cikin zuciyarsa ba a jikinta ba. Don haka ta fada masu abinda ya fi damunta. Sai tace: Na rantse da All..na zama mai kin duniyarku, da kuma takaici ga mazajenku.

Wannan shi ne yafi damanta, kuma ta damu da yadda mutanen Ansar suka yi watsi da Ita, suka kuma zabe hanyar da bata dace ba, ko kuma suka ki taimaka mata a lokacinda take bukatar taimakonsu.

Sai ta kara da cewa na yi wasti da su bayan na jarrabesu. Na kuma kaurace masu bayan na ga cewa basu da anniyar kasancewa tare da ni, bayan na gane hakikaninsu. Abin kunya ne a garesu da takubbansu marasa kaifi.

A nan tana nufin cewa, abin kunya ne a garesu ta nemi taimakonsu amma su kasa taimaka mata. Abinda kungiya ne garesu, su yi shiru a dai dai lokacinda take kuka tana neman mataimaka wadanda zasu karbamata hakkin ta, suna nan amm basu taimaka mat aba.

Sai ta cewa gaba da cewa: Sun yi watsa da gaskiya bayan sun kasance masu daukarsa da muhimmanci.

Wato mutanen Ansar a farkon musulunci sun kasashen cikin wadanda suke taimakawa gaskiya, suka sade ransu don ya kafu amma kuma a halin yaznu sun fara was da shi, sabo sun kasa taimaka mata a lokacinda ta bukaci hakan daga wajensu.

‘Suna dokan duwatsu wadanda basa da karfi, suna bata masunsu’. Wannan saboda shi mashi dole ne ya kasance yana da karfi kafin ya huda wani abu, don haka idan ya rasa kaifinsa ba za iyi wani amfani ba. Don ba zai kashe makiyi ba.

“sannan suna kuskure wajen hukunta al-amura’ anan tana cewa, sauran amincewarsu da shugabancinda da ba ta iyalan gidan manzon All..(s). da kuma yin watsi da su a lokacinda suka bukaci taimakonsu.

“an batar da su da abubuwan wargi’ wato wadanda ba gaskiya ne ba, batanda ya sabbaba musibu ga al-ummar musulmi na karnuka masu yawa, kamar duk wanda ya karanta tarihin musulunci zai fahinci hakan.

Sannan ta karanta sura aya ta 80 na suratun Nisa inda All..T yake Magana dangane da Banu Isra’ila da kuma yadda malamansu da shuwagabanninsu suka batar da su, da kuma yadda hakan yana a matsayin baut ne a garesu, kuma sun halakasu suna                  sane da hakan.

Sannan tace ‘Lalle na daura igiyar a wuyarsu’. A nan tana nufin ta gama aikinta, ta kuma   kafa hujja a kan muhajiruna da Ansar, a khudubar da ta yi a masallaci, don haka a halin yanzu, hakkin abubuwan da zasu faru na bata ya hau kansu. Don haka su zasu gamu da All..sannan al-ummun da zasu zo nan gaba wadanda zasu gane kurakuransu.

‘Na sauke nauyin abinda ya faru a kan wuyarsu’ kuma ina da tabbacin cewa zata ji kunya a ranar da ba zata amfanesu ba.

A nan tana nufin, wadanda suka aikata ba daidaiba a wannan lokacin, zasu ji kunya a nan duniya sannan a lahira kuma zasu dauki alhakin duk barnan da ya faru ko kuma zai faru da al-ummar musulmi a cikin wannan al-ummar.

Dangane da wannan maganar ta Zahra(s), zamu fahinci haka a wannan zamanin da muke ciki, inda duk tare da tursasawa iyalan  gidan manzon All..(s) da mabiyansu da aka yi a tsawon tarihi , sai gashi ba inda zaka je a duniya sai ka samu Mabiya iyalan gidan manzon All..(s).

Kuma dukkan asiran da malaman tarihi da kuma sarakunan da suka gabata suka boye sai sun fara bayyana. Hatta wadanda basu da ilmi mai zurfi zasu fahinci kura kuran da wadannan magabata suka yi. Da kuma barnan da suka yiwa addinin musulunci bayan wafatin ma’aikin All..(s).

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments