Kissoshin Rayuwa Fatimah (s) 58

Assalamu alikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sakesaduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo makukissoshi wadanda suka zo

Assalamu alikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake
saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku
kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan
wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Shahid Aya. Murtadha
Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana Jalaluddin Rumi. Ko
kuma cikin wasu littafin. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a ciki sirar Fatimah
Azzahra(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun tsaye a
cikin khudubarta (s) inda take Magana da mutanen Ansar wato madina, Inda ta
fada masu kan cewa ‘ta yaya zasu bari a zalunceta a cikin al-ummar mahaifinta
a dai dai lokacinda suke da karfin kare mata hakkinta’.
Sannan ta zargi khalifa na farko da kwace hakkinta duk da cewa hakkokinta sun
tabata a cikin Alkur’ani mai girma. Sannan ta jera wasu tambayoyi ga khalifa na
farko, wadanda suka hada da cewa, shin All..T ya kebanceshi da wasu ayoyi ne,
wadanda bai yi wahayi ga babanta ba?, ko kuma sun san wasu abubuwa a cikin
alkur’ani mai girma wadanda mijinta Aliyu dan Abitalib (s) bai sani ba?. Ko dai
da gangan suka sabawa Ubangiji a cikin abubuwan da ya saukar dangane da
hakkokinta?
Bayan da ta ajiye maganarta (s), sai Khalifa na farko ya bata amsa da cewa : Ya
diyar manzon All..(s), babankin ya kasance, mai tausayi ne ga muminai, mai
yawan kyauta da jinkai a garesu, kuma ya kasance azaba mai tsanani da ukuba
babba ga kafirai. Idan an nasabta shi, zamu tabbatar da cewa shi mahaifinki ne,
banda sauran mata, kuma shi dan’uwan mijinki ne banda sauran sahaban. Ya
zabeshi kan dukkan abokai ko sahabbansa, sannan shi kuma ya taimaka masa a
cikin dukkan al-amura masu muhimmanci a lokacin isar da sakon All..T ga
mutane.

2

Ba mai sonku sai mai rabo, ba kuma mai kinku sai shakiyyi marasa rabo, ku ne
zurriyar manzon All..(s) masu tsarki, zababbu a cikin zababbun All… Kune masu
shiryar da mu zuwa hanya madaidaiciya, sannan masu jagorantarmu zuwa
masaukimmu a Al-janna.
Ya ke mafi alkhairin mata, diyar mafi alkhairin annabawa, kin fadi gaskiya a
zancenki, kuma kin rika kowa a cikar hankalinki. Ba wanda ya isa ya hanaki
hakkinki, haka ma ba wanda yake musanta gaskiyarki. Na rantse da All.., ban
taba sabawa manzon All..(s) ba, kuma duk abinda na yi bisa amincewarsa ne,
nake yi, mai khidima baya karya ga wadanda yake masu khdima. Kuma
All..Shaida ne, kuma ya isheni shaida, kan cewa na ji manzon All..(s) ya na
cewa: Mu annabawa ba ma gadar da zinari ko azurfa, haka ma gida ko filaye,
abin sani kawai muna gadar da littafi, da hikima da ilmi, da annabci. Sannan
abinda muka bari na dukiya, to na mai jibintan al-amrin musulmi a bayammu
ne, zai hukunta abinda ya ga dama a kansa.
Kuma tuni mun rika mun yi amfani da dukiyar da kike Magana a kanta, wajen
sayan makamai wadanda musulmi zasu yi yaki da su, su yaki kafirai da su, kuma
yaki wadanda suka yi tawaye fajirai da su. Wannan shi ne ra’ayin musulmi gaba
daya, bai kadaita da shi ba. Bil’hasali ma ba na dorawa musulmi ra’ayi na.
wannan shi ne halin da nake ciki da kuma dukiyata, duk suna gaba gareki, ki
hukunta abinda kika ga dama dasu ba wanda zai mayar da umurninki.
Ke ce shugaban matan al-ummar mahaifinki, kuma kace tsarakekkiyar itaciyar
yayanki, ba wanda ya isa ya musanta falalarki, haka ma ba wanda ya isa ya
musanta tsarkin nasabarki, hukuncinki abin zartarwa ne kan abinda na mallaka,
kina son in sabawa babakin ne a cikin wannan al-amari?.
Karin bayani a kan jawabin Khalifa na farko shi ne, da farko ya tabbatar da
cewa Fatimah (s) ita ce shugaban matan al-ummar babanta, kuma tana da

3

tsarkin da ba wanda ya isa ya karyata maganata. Da kuma matsayin mijinta a
wajen manzon All..(s), dangne da abinda ya ce ya ji daga manzon All..(s) na
cewa su annabawa ba’a gadonsu a abinda suka bari na abin dukiya na
majibincin al-amura a bayansa ne, sai dai Alkur’ani, da hikima da kuma annabci
ne yayansa suke gada. Sannan abinda suka bari na dukiya hukuncinsa na
hannun wanda ya zama majibincin al-amarin al-umma a bayansa ne!.
Da farko ta yaya manzon All..(s) zai fadawa wanda baya gadonsa kan cewa ba’a
gadonsa a dukiyar da ya bari bai fadawa wacce itace kadai zata gajeshi a cikin
danginsa ba.
Ta yaya aka yi manzon All..(s) bai fadawa Fatima (s) wacce, a shari’ar musulunci
ita ce kadai zata gaje shi, bayan wafatinsa in banda thuminin da za’a fitarwa
matansa su 9 su raba a tsakaninsu. ? a wannan hukuncin duk abinda manzon
All..(s) ya mallaka ko ya bari na duniya, za’a raba shi 8, matan manzon All..(s) su
dauki 1/8 su raba a tsakaninsu su 9 dai dai, sannan Zahra’u (s) ta dauki sauran
dukiyar wato kaso 7/8. Daga ciki har da gidansa inda matansa suke zama.
Don a cikin Al-kur’ani mai girma All..T yana cewa: {Kada ku shiga gidajen
Annabi sai an baku izini na cin abinci…..} Al-Ahzab 53. Yaya aka yi khalifa na
farko ya bar matan manzon All..(s) a gidajen Annabi (s) har zuwa karshen
rayuwarsu, bai kwacesu ba, kamar yadda a kwace gonar Fadak daga hannun
Zahra (s) ba, ko kuma bai fitar da rabonta a cikin gidajen ba, kamar yadda ya
bar ko wacce daga cikin matansa a dakin da take ciki har zuwa karshen
rayuwarta?.
Sannan mun san cewa manzon All..(s) yace:Nine birnin ilmi kuma Aliyu ne
kofarsa, ta yayi wanda ya kasance kofar ilmin manzon All..(s) bai san wannan
hadisin ba, duk da cewa matarsa Fatimah (s) ce kadai wacce zata gaji mafi
yawan abinda manzon All..(s) ya bari? Banda haka Khalifa na farko ya tabbatar

4

da cewa annabawa suna gadar da ilmi da hikima da kuma annabci ga
zurriyarsu. Ta yaya Zahra wacce ta gaji ilmin mahaifinta(s) bata san wannan
hadisin ba, bata kuma san wannan hukuncin ba? Ko dai ana tuhumarta da
rashin amfani da ilmin da ne ? wanda ta gada daga wajen mahaifinta?.
Sannan idan gaskiya ce Zahra (s) abin gasgatawa ne a kan duk abinda ta
hukunta, me yasa ba’a bata abinda ta nema tun farko ba, na cewa gonar fadak
tatace, kuma ta kawo shaidu wadanda ba wanda ya isa ya karyatasu, amma
duk da haka an hana ta?.
Banda haka babu wani musulmi wanda ya sake ruwaito wannan Hadisin daga
manzon All..(s) sai shi Khalifa na farko. Wanda banda ayoyin alkur’ani da
hadisan manzon All..(s) ingantattu da suka tabbatar da sabanin abinda hadisin
ya kunsa. Wato annabawa ana gadonsu a cikin dukiyar da suka bari, amma
annabci ba ko wani annabi ne yayansa suke gadon Annabcinsu ba, don shi
annabci zaben All..ne.
A cikin littafin kashful Ghumma, ya zo kan cewa a lokacinda Uthman bin Affan
khalifa na uku ya zama Khalifa, Ummul muminina A’ish ta zo wajensa tace
masa: Ka bani abinda Babana da kuma Umar suke bani a lokacin khalifancinsu!
Sai ya ce mata: Ni banga wani hakkinki a littafin All..da kuma sunnar manzon
All..(s) da zan dogara da shi in baki wani abu ba, amma tunda Abubakar da
Umar suna baki saboda ra’ayinsu, ni ma zan baki kamar yadda suke baki.
Sai tace ka bani gadona daga manzon All..(s). Sai yace: Ba ke ce da kuma Malik
dan Aws Annadri kuka shaida kan cewa manzon All..(s) yace: Mu annabawa
baa’aa gadommu ba?, da haka kuma kuka bata hakkin Fatimah (s) na gadon
mahaifinta ? Sannan a yanzun ki ce kina son a baki gadonki daga manzon
All..(s)?.

5

Abin mamaki, ta yaya Khalifa na farko ya karbi shaidar A’isha kan cewa hadisin
‘mu annabawa ba’a gadommu..’ amma yaki karban shaidar Zahra’u (s) wacce
ayoyin Al-Kur’ani mai girma sun tabbatar da tsarkinta?.
Sannan yaya aka yi Khalifa na farko ya karbi shaidar Malik dan Aws kan hadisin
‘mu annabawa ba’a gadommu..” amma an ki karban shaidar Amirulmuminina
Aliyu dan Abitalib (s) kan hakkin matarsa Zahra’u(s) tana da gaskiya a kan
hakkinta na gadon manzon All..ko kuma na gonar Fadak?.
Banda haka, Khalifa ya fadawa Zahra(s) a lokacin da ta kawo Mijinta a matsayin
shaidar mallakar gonar Fadak, kan cewa shi na kusa da ita ne, don haka ba zai
iya shaida mata ba, a yayinda ya amince da shaidar Ummul muminina A’ish kan
ingancin hadisin da ya kirkiro duk da cewa diyarsa ce?.
Daga nan zamu fahinci cewa a lokacin yake cewa: wannan ba ra’ayinsa shi
kadai bane, ba yana nufin ra’ayin manya manyan sahabban manzon All..(s)
bane ko kuma Ahlul-Baiti ba ne, sai dai yana nufin Ra’ayin diyarsa A’isha ce.
Sannan daga karshe, khalif ana farko ya rufe maganarsa, da cewa: shin kina
ganin yakamata in sabawa manzon All…(s) a cikin wannan Lamarin ne?.
Abin mamaki, Fatimah (s) da mijinta wanda shi ‘Naf” na manzon All..(s) ne ana
tuhumarsu da sabawa manzon All..(s), a yayinda khalifa na farko wanda bai da
wannan tsarkin ya na ganin shi ne yake tare da manzon All..(s) yake kuma
aiwatar da umurninsa.
To. Amma mu ji martanin Zahra (s) ga jawabin Khalifa na farko a cikin
Khudubarta (s), ta Al-Fadakiyya.
Tace: Tsarki ya tabata ga All..! Mahaifi na manzon All..(s) bai taba sabawa
littafin All..ba ko kuma ya musanta hukunce hukuncesa ba, sai dai yana bin
hukunce-hukuncensa yana bin umurninsa. Shin zaku taru a kan jingina masa

6

karya ne, a bayan wafatinsa? Bayan karyayyakin da kuka jingina masa a
rayuwarsa.?
Ga Alkur’ani mai girma nan, mai bayyana adalci yake kuma fadar gaskiya yana
cewa {Ya gajeni ya kuma yayi gado a cikin Dangin Ya’akuba} kuma yana cewa
{Kuma Sulaimanu ya gaji Ya’kuba} sannan All..mai girma da daukaka ya
bayyana a cikin rabon gado, ya hukunta kan abinda ya shafi rabon gado, ya
bayyana a binda ya halatta na rabon mazaje da mata na gado. Ya kuma
fayyace, kome da kome wanda ya kauda rikitattun abubuwan da mabarnata
suka zo da su.
Babu, wato {Sai dai, zukatanku sun sawwala maku wannan al-amari, to, hakuri
mai kyawu ya fi dacewa, kuma All..shi ne mai taimakawaa kan abinda kuke
surantawa}.
A cikin wannan bangare na khudubarta(s) ta bayyana cewa, ba yadda za’a yi
mahaifinta ya sabawa Al’kur’ani mai girma, sannan hakan ba zai taba yiyuwa ba
gareshi. Saboda yana bin umurnin Al-Kur’ani sau da kafa. Wannan kariya ce da
aka jingina masa bayan wafatinsa, kamar yadda aka sha yi haka a rayuwarsa.
Don haka zukatanku ne ya sawwala maku hakan, mu kuma hakuri mai kyau ya
fi dacewa da mu, sannan All..shi ne mai taimaka mana a cikin wannan al-
amarin.
Masu sauraro saboda kurewar lokaci a nann zamu dasa aya a cikin shirimmu na
yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa
rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments