Kissoshin Rayuwa Fatimah (s) 56

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwaa cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshiwadanda suka zo cikin

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa
a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi
wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka
hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shaheed Murtadha Muttahari ko kuma
cikin littafin mathnawa na maulana jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan
da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.
///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a
kuma cikin sirah ko kuma kissar Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo
maku. A cikin shirimmu da ya gabata mun yi magana dangane da auren Zahra (a)
da kuma yadda manya-manyan sahabban manzon All..(s) suka gabatar da kansu
don auren Zahrah (s) amma manzon All..(s) bai basu amsa ba, ko kuma ya ce masu
yana jiran hukuncin All..dangane da aurenta.
A lokacinda suka ga manzon All..(s) ya mayarda su gaba daya, sai suka bawa
Aliyu (a) shawarar ya gabatar da kansa a gaban dan amminsa manzon All..(s) don
neman auren Zahra (s).
Daga karshe ya amince da shawararsu, duk da cewa bai da wani abin duniya da zai
iya rike gida a lokacin. Sannan a lokacinda ya gabatar da kansa, manzon All..(s),
ya fada masa cewa kafinka, wasu mazaje sun ambaceta, amma da yayi mata
Magana sai ya ga rashin amincewa a fuskarta. Don haka ya ce masa ya jira bari ya
shiga wajenta ya ji ra’ayinda dangane da bukatarsa.
A wani hadisin ya cewa Aliyu (s) ya zauna ya jira shi har ya sami inzininta da
yardarta, ya shiga wajenta ya kuma fada mata cewa, Aliyu ne ya zo neman aurenki.
Mun san cewa mahaifi a irin wannan halin a matsayinsa na mahaifi zai gabatar
mata da shawara, da kuma wasu Karin sifofin wanda yake son aurenta wadanda

2

suka hada da matsayinsa a wajen All..da ilminsa na sanin All.. da abinda ya
mallaka na abin duniya da sauransu.
Sai dai dangane da Aliyu (a) wadan nan al-amura ba boye suke ga Zahra (s) ba.
Don haka manzon All..(s) ya takaita mata da cewa: Ya Fatimah. Lalle Aliyu dan
Abitalib (a) wanda kika sani din nan, wanda kika san kusancinsa da falalarsa da
kuma musuluncinsa, kuma lallai ni na roki All..T ya auradda ke ga mafificin
halittunsa kuma wanda yafisu daga cikinsu, ya ambaceki me kike gani?
Sai ta yi shiru bata juya fuskanta ba, manzon All..bai ga bata fuska a wajenta ba,
sai ya tashi yana cewa: All.. mai girma, shirunta yardarta ne. Manzon All..(s) ya
dauki shirinta yardarta ce, kuma muwafakarta da auren ne. Wannan kuma saboda
yan mata badare wadanda basu taba aure ba suna jin kunya su bayyana
amincewarsu da auren wani, amma idan basu amince ba, ko kuma basa son wani
ba zasu ji kunyar cewa basa son shi ba.
Manzon All..(s) ya dawo ya sami Aliyu (a) yana jiransa, sai ya fada masa cewa ta
amince. Sai dai kuma bai san irin tanadin da Amirulmuminina (a) yayiwa wannan
al-amari ba. Don dole sai an yi sadaki an kuma yi shirin bikin aure, da kuma wurin
zama.
Banda haka wannan aure na musamman ne tsakanin tsarkakakku, Musamman a
bangaren saukin sadakin auren, da kuma rage yawan kudaden da ake kashewa a
cikinsa.
Banda haka auren Zahrah (s) aure ne wanda zai zami misali ga dukkan musulmi
har duniya ta dade, ga wanda yake son bin sunnan manzon All..(s) a aure. Saboda
sauran yayan manzon All..(s) mata, wato Rukayya, ummu Kulthum da zainab(a),
duk an yi aurensu ne kafin hijira a Makka ko kafin annabci. Don haka musulmi ba
su san yadda aka yi aurensu ba.

3

Manzon All..(s) ya cewa Aliyu (a) kana da wani abu wanda zan auram maka da
shi?
Sai ya ce: iyayena fansarka, ba abinda yake buye a gareka dangane da al-amarina.
Ina da takobi na, garkuwata da kuma rakumi.
Wannan shi ne dukkan abinda Imam Ali (s) ya mallaka a dunkiyar duniya, kuma
ya na shirin aure.
Amma manzon All..ya saurare shi da nutsuwa sai yace: Ya Aliyu, takobinka dole
ne ka rike shi, don ka yi jihadi ko yaki da shi a kan tafarkin All… kuma ka yaki
makiyan All…da shi, sai kuma rakuminka kana bukatarsa don daukar kayakanka
ko kuma hau shi. Don haka, na aurar maka da garkuwarka, kuma na yarda da
hakan a matsayin sadaki. Ka saida shi ka kawo mani kudin.
Malaman tarihi sun bayyana cewa Ali (a) ya sami wannan garkuwan ne a matsayin
ganimar yakin Badar. Kamar yadda Allamah Askalani ya kawo a cikin littafinsa al-
isaba fi ma’arifatis Sahabah. Shafi na 365 Jz 4.
Manzon All..(s) ya bashi ita a lokacinda ya raba ganimar yakin Badr. Ana kiranta
(Alkhadmiyya) wato mai karyawa, wato mai kakkarya takubba saboda karfinta,
takobi baya huda shi. Malaman tarihi sun bayyana cewa Aliyu ya saida garkuwar
tasa da dirhama 450 ko 500. Ya kawowa manzon All..(s) kudin, sai ya bawa
matarsa ummilmuminina ummu salma ta ajeye su.
Don haka tare da wannan an tabbatar da cewa sadakin shugaban matan duniya
daga farkonta har karshenta, kuma shugaban matan Aljanna, har’ila yau diyar
mafificin halittun All….kuma cikamakin annabawa da manzanni dirhami 500 ne.
Manzon All..(s) ya aurad da diyarsa da wannan kudin ne, ga khalifansa a bayansa
Aliyu dan Abitalib (a) ne, don ya warware al’adun larabawa musamman

4

shuwagabanni da manya manya daga cikinsu, na tsawwala sadakin auren yayansu
mata da suke yi a jahiliya.
Yayi haka ne don wadanda suka kasance kasa da shi a daraja, su yi koyi da shi.
Har’ila yau yayi haka ne don sauran mata, musulmi kada ga su cewa sai an basu
sadaki mai yawa fiye da wanda ya aurad da diyarsa Zahra (s) da shi.
Har’ila yau akwai wasu hikimomo da dama da suke cikin wannan auren mai
albarka, amma ba nan ne wurin ambatonsu ba.
Wannan shi ne abinda manzon All..(s) ya yi a duniya kenan, amma All…T ya
kiyayewa shugaban matan aljanna, matsayinta a wajenshi, don haka an gudanar da
bikin aurenta da Aliyu dan Abitalib(a) a sama a wajensa.
Don haka All..T ya auradda Fatima (s) ga Aliyu dan Abitalib (a) a wajensa kafin
mahaifinta ya auradda ita gareshi a nan duniya.
Wannan kuma ba abin mamaki bane, don All..T ya aurad da wacce ba ta kai
darajatta ba a sama, ummil muminina Zainab Aljahash, kafin manzon All..ya
aureta a kasa. Kamar yadda ya zo cikin alkur’ani mai girma inda All..T yake cewa:
{to a lõkacin da zaidu ya ƙãre bukãtarsa daga gare ta, Mun aurar da
kai ita……} Ahzab 33:37
Hakama All..T ya aurad da wata mata wacce ta bada kanta ga manzon All..(s), a
sama. Don haka, ba abin mamaki bane, All..T ya auradda Zahra (s) ga Aliyu(a) a a
wajensa kamar yadda ruwayoyi suka bayyana, a kuma yi bukukuwan auren
wadanda mala’ikun All…T suka halarta suka kuma nuna farin cikinsu, kafin a yi
na kasa.

5

Amma dukkan wadann nan abubuwan sun faru ne don girmama mahaifinta, da ita
kanta da mijinta da kuma yayan da zasu Haifa bayan auren. Bikin auren Zahar(s)
da aka gudanar a sama ta 4 ta musamman ce, halittu basu taba ganin irinsa ba.
An kafa mimbarin karamah, wanda ya kasance mimbari ne da aka yi shi daga
Haske, All..T ya yi wahayi ga mala’ikan Sa mai suna Arrahil, kan ya daga wannan
mimbarin, ya kuma gode masa da godiyarsa, ya kuma daukaka shi da daukakarsa.
Ya kuma yabe shi da yabon da ya dace da shi. Babu wani daga cikin mala’iku
wanda yafi Arrahil iya Magana da fasahar Magana da kuma murya mai dadi: Sai
Arrahil Ya hau membari ya ce:
Godiya ta tabbata ga All..kafin farawar na farko, kuma wanzazze bayan karewar
talikai, muna gode masa a lokacinda ya Sanya mu mala’ikunsa Rawhaniyyawa.
Wadanda suke yada kasancewarsa Ubangiji.
Kuma muna gode masa bisa ni’imar da yayi mana, ya kuma kiyaye mu daga
dulmuya a cikin abubuwan sha’awa. Ya Sanya shaawarmu a cikin tsarkake shi da
kuma ambatonsa.
Mai shimfida rahamarsa ga bayinsa, mai bada ni’imominsa garesu, ya daukaka
daga kafircewar mutanen kasa, daga cikin mushrikai. Ya kuma daukaka tare da
girmansa daga kariyar kafirai….. har zuwa inda yake cewa— All…Sarki mai
buwaya ya zabi zababbun karamcinsa, bawan girmansa, ga al-ummarsa shugaban
mata, diyar mafi alkhairin annabawa, kuma shugaban manzanni limamin masu
tsaron All..Sai ya sadarda igiyar sa, da igiyar wani daga cikin iyalan gidansa,
sahabinsa, kuma wanda ya gasgata kiransa, mai gaggawa zuwa ga umurninsa, bisa
sadarwa, da Fatimatul Batul diyar manzo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments