64-Assalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahad Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana Jalaluddeen Ruma ko kuma dai cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) shuwagabannin samarin Aljanna, da muke kawo maku, mun bayyana yadda Zahra (s) ta yi ta kuka dare da rana saboda rashin mahaifinta Manzon All..(s), yawan kukanta ya kai ga mutanen Madina suka bukaci Amirulmuminina (s) ya fada mata kan cewa ta yi kuka da dare kawai ko da rana kawai, don tana hanasu barci ko kuma samun ayyuka da rana.
Amma a lokacinda Imam Ali (a) ya fada mata, sai tace: Ai ba zan dade a cikinsu ba, kuma ni ba zan iya daina kukan rabuwa da mahaifina ba, har sai na hadu da shi.
Daga nan sai ya ce mata ta yi abinda ta ga dama. Amma dai daga baya ya gina mata wani wuri, wanda ake kira -gidan bakin ciki- a kusa da makabartar bakiyya inda take yini tana kuka tare da yayanta Alhassan da Alhusain (a).
Sannan munji yadda Zahra (s) ta fara rashin lafiyarta ta karshe, wanda bata sake tashi ba har sai da ta koma ga Ubangijinta. Munji kuma yadda Asma’u diyar Umais matar Jafar dan Abitalib(a) take khidima wa Fadima(s), kuma Fatimah (s) take samun nutsuwa da ita a duk lokacinda ta zo wajenta. Wannan kuwa duk tare da kasancewar ta, a lokacin matar Khalifa na farko ne, kuma takan bayyana karkatarta ga iyalan gidan manzon All..(s) a fili lokacin.
Munji cewa, kusancin da ke tsakaninsu ya kai ga Zahra(s) tana fada mata wasu asiranta. Kuma kamar yadda zamu gani nan gaba, tana gidan Zahra (s) a lokacin da ta bar duniya ko ta yi shahada.
Sai dai kamar yadda muka fada a cikin shirimmu da ya gabata, Fatimah (s) ta bukaci Mijinta Aliyu dan Abitalib (a) da kuma wadanda suka gidan kada su yada labarin rashin lafiyarta, kuma sun amince da haka, sai ko yaya aka yi? labarin rashin lafiyanta ya sulale ya fita daga gidan ya kuma yadu a cikin Madina.
Sai dai labarin da ya yadu bai nuna cewa wata rashin lafiya mai tsanani ce, ta kamata ba. Da dama suna ganin yawan kukan da take yi, da kuma bakin cikin abinda ya faru da iyalan gidan manzon All..(s) ne, suka hadu suka sata rashin lafiya.
Amma kada a manta a kwanakin farko na wafatin mahaifinta, da kuma kokarin da sarakuna suka yi na tilastawa mijinta Aliyu dan Abitalib (a) yin bai’a, ya sa ta zubar mata da cikin danta Muhsinu, sannan taba jikinta da wasu masu kokarin shiga gitanta suka da karfi suka yi, ya bar tabo a jikinta, ya kuma ji mata Rauni jikinta, kuma su ma sun taima wajen tsananta rashin lafiyanta na karshe.
Har’ila yau mun bayyana cewa, bayan wafatin manzon All..(s) shuwagabannin da suka kwace shugabanci a hannun Al-baitin manzon All..(s), sun manta da ayoyin Alkur’ani mairgima da hadisan da suka ji daga bakin manzon All..(s) dangane matsayin iyalan gidansa, a cikin al-ummarsa a bayansa. Sannan suka aikata abinda suka aikata.
Da kuma abinda ya biyo baya, na kin bai’ar da Aliyu (a) ya yi da kuma bin gida gida da suka yi tare da Zahra (s) zuwa gidajen sahabban manzon All..(s) muhajirun da Ansar, suna neman taimakonsu, da khudubobin Zahra (s) a masallacin manzon All..da kuma na cikin gidanta ga mata, da kuma na mazajen da suka zo wajenta, ya sa mafi yawan mutanen madina sun fara kyamar duk wani shugabanci, wanda iyalan gidan manzon All..(s) ba su amince da shi ba.
Wannan ne ya sa shuwagabanni na lokacin suka ga yakamata su yi wani abu, don shafi wannan mummunan tabon, da suka yiwa kansu. Don mutane su manta da abinda ya faru a baya, su koma wajen shuwagabannin, su amince da su, su kuma yarda da su.
Mun san cewa sau da dama shuwagabanni sukan ci mutuncin raunana a wani lokaci, a cikin jama’a, amma sai su je a asirce su nemi gafara ko afwa daga wajen wadanda suka batawa rai ko suka cutarda su, ba tare da kowa ya sani ba, sai su ci gaba da harkokinsu, su yi tsammanin cewa sun sha.
Don haka abinda ya faru kenan bayan da shugabanci ya tabbata a hannun Khalifa na farko.
Ibn Kutaiba ya kawo a cikin littafinsa Al-Imama wassiyasa JZ1 shafi na 4, sannan mai littafin Aalamun Nisah, ya kawo labarin a cikin JZ 3 SH na 314, duk suna cewa: Lalle Umar ya fadawa Abubakar ( r), kan cewa: Tashi mu je wajen Fatima(s) lalle mun fusatata, sai suka tashi gaba daya, suke je wajenta, suka nemi izinin shiga sai ta ki amincewa. Sai suka bi ta hannun Aliyu (s) don ya shigar da su wajenta. Sai Aliyu ya shigar da su wajenta, a lokacinda suka shiga wajenta sai ta juya fuskanta tana Kallon bongo, sai suka yi mata sallama sai ta ki amsa sallamarsu.
To, amma duk da haka, sai Abubakar ya yi Magana, yana cewa: Ya masoyiyar manzon All..(s). Na rantse da All.. makusantan manzon All..(s) sun fi soyuwa a gareni daga dangine. Kuma lalle kin fi soyuwa a gareni daga A’isha diyata. Wallahi naso a ce na mutu a ranar da mahaifinki ya yi wafati, kada in wanzu a bayansa. Kina ganin yadda na sanki, na san matsayinki da daukakanki, zan hanaki hakkinki, ko gadonki daga manzon All..(s)?
Ki saurara, ni naji mahaifinki manzon All..(s) yana cewa: Bama gadarwa, abinda muka bari sadaka ne.
Sai tace: Idan na fada maku wani hadisi wanda kuka ji daga mahaifi na zaku gasgata ni ? Sai suka ce: Eee,
Sai tace: Na hadaku da All..shin baku ji manzon All..(s) yana cewa :{Yardar Fatima daga yarda ta ce, Fushin Fatima daga Fushi na ne, wanda ya so Fatima diyata, hakika ya so ni, kuma wanda ya yarda da Fatimah ya yarda da ni, wanda ya fusata Fatima ya fusahi ni}?
Sai suka: Eee munji manzon All..(s) yana fadar haka.
Sai tace: To lallai ina shaidawa All..da mala’ikunsa kan cewa kun fusatani, baku nemi yardata ba, kuma lalle idan na hadu da manzon All..(s) sai na kai kararku a wajensa. Sai Abubakar ya fara kuka, kamar ransa zai fita. Sai Fatima (s) ta ci gaba da cewa: a duk sanda na yi sallah sai na yi addu’a a kanka.
Sai suka fita, sai Abubakar yana kuka. Sai mutane suka taru a wajensa, sai yace masu. Kowa daga cikinsu yana barci tare da iyalansa yana farin ciki, amma kuka barni a cikin halin da nake ciki. Bana son bai’arku, ku kubutar da ni daga bai’ar da kuka yi mani.
Sannan a cikin littafin ilalushara’I’ii, na sheikh Assaduk (r ) yana cewa: A lokacinda Fatimah (s) ta yi rashin lafiyan da bata sake tashi ba, har ta yi wafati, Abubakar da Umar sun zo wajenta, suka nemi izinin shiga, amma ta ki ta bada izinin shigowarsu. A lokacinda Abubakar ya ga haka sai, ya yi bakance ba zai shiga inuwa ko karkashin wani abu ba, sai ya shiga wajenta ya nemi yardarta. Sai ya kwana a farfajiyar, sai Umar ya zo, ya sami Aliyu (s), ya ce masa: Hakaki mun yi ta zuwa wajenta, munason shiga wajenta, amma taki bada izini, idan zaka iya ka nemammana izinin shiga wajenta, kayi.
Sai yace: Ee zanyi. Sai Aliyu(a) ya shiga wajenta, ya ce mata: Ya diyar manzon All.. kin ga yadda wadannan mutane biyu suka yi ta neman shiga wajenki, sun yi ta zuwa sau da dama kina maidasu, sun bukace ni, in nemammasu izinin shiga wajenki.
Sai tace: Na rantse da All..ba zan yi masu izini ba. Ba zanyi masu Magana ba har sai na hadu da mahaifina, in kai karansu a wajensa. Saboda abinda suka aikata, da kuma abinda suka yi da ni.
Sai Imam Ali(s) yace: Hakika na yi masu alkawali zan shigar da su a wajenki. Sai tace: Idan ka yi masu alkawali, to, gida, gidanka ne, mata kuma suna bin mazaje ne. ba zan sabamaka a kan wani abu ba. Ka yi izini wa wanda ka ga dama.
Sai Imam Aliyu (s) ya fita, ya kuma yi masu izini su shiga wajenta. A lokacinda suka ganta, sai suka yi sallama, sai ta ki amsa sallamarsu. Ta kuma juya fuskanta daga wajensu, sai suka je ta inda ta juya fuskanta, ta juya suka juya, sai da ta gaji …sai tacewa matan da suke tare da ita ku shiga Tsakanina da su, da suka ga haka, sai khalifa na farko ya ce: Ya diyar manzon All…mun zo neman yardarki ne, da kuma kaucewa fushunki. Muna neman ki gafarta mana, ki kuma yafe mana abubuwan da muka aikata.
Sai tace: Ba zan ce maku kome ba sai na hadu da mahaifi na, in kai kararku a wajensa. In fada masa abinda kuka sana’anta, abinda kuka aikata, da abinda kuka yi da ni.
Sai ta juya wajen Aliyu (a) ta ce masa: Ba zan yi masu Magana ba, sai na tambayesu wani abu da suka ji wajen manzon All..(s), idan sun gasgata ni, sai inga abinda ya dace in yi.
Sai suka ce, lalle mun amince ta yi haka. Kuma ba zamu fada ba sai gaskiya, ba zamu shaida ba sai gaskiya.
Sai tace: Na hadaku da All..zaku tuna wata rana manzon All..(s) ya fito daku a tsakiyar dare, dangane da wani abu da ya faru, dangane da Ali?(s). Sai suka ce: Lalle mun tuna.
Sai tace: Na hadaku da All.. shin kun ji manzon All..(s) ya na cewa: Fatimah tsokace daga gareni, kuma ni daga gareta nake, wanda ya cutar da ita ya cutar da ni, wanda ya cutar da ni ya cutar da All…wanda ya cutar da ita bayan wafatina kamar wanda ya cutar da ita a rayuwa ta ne, wanda ya cutar da ita a rayuwata kamar wanda ya cutar da ita bayan wafati nane?.
Sai suka ce: Es Haka ne! Sai tace: Godiya ta tabata ga All… Sai tace: Ya Ubangiji ina shaida maka, ku shaida ! Ya ku wadanda suke tare da ni,: Wadannan mutane sun cutar da ni, a rayuwa ta, a kuma lokacin rasuwata, na rantse da All..ba zan yi magana da ku ba, har sai na hadu da Ubangiji na, in kuma kai kararku a wajensa. Kan abinda kuka aikata da shi da kuma ni. Da kuma laifuffukan da kuka yi mani.
Sai khalif ana farko ya fara cewa, kaito na, …yana ce: Ina ma mahaifiyata bata haife ni ba.
Sai khalifa na biyu ya ce: Abin mamaki da mutane, yadda suka dora maka shugabancinsu ka na tsoho,…— kana firgici saboda wata mata ta yi fushi, kana farin ciki da yardarta, me zai faru da wanda ya fusata wa ta macce. Sai suka tashi suka fita.
Sai kuma a cikin littafin ‘Baitul Ahzan’ yace: bayan sun fita, sai Fatimah (s) ta fadawa Aliyu (s) kan cewa: Na aikata abinda kake so.? Sai ya ce: Ee. Sai tace: Shin zaka yi abinda zan umurceka da? Sai yace : Ee. Sai ta ce: Lalle ni ina hadaka da All..kada su yi mani sallah idan na rasu. Kada kuma su tsaya kan kabarina.
Sai dai malaman tarihi sun bayyana cewa: Babu bukatar kuka ko fadan kaico na, kamar yadda ruwayar Ibnu Kutaiba ta fada, don hakan ba zai dawo da hakkin Zahra(s) da aka kwace ba, kuma ba zai sa ta yafe masa laifukan da suka yi mata ba.
Sai dai Khalifa na farko ya na son ya ci gaba da rike dukiyar Zahra(s), baya son ya mayar mata hakkinta, ya kuma sami yardarta.(s). a ikin wannan halin.
Ba wani mai hankalin da zai taba amicewa da haka. Idan da gaskiya su na son afwarta, da kuma yardarta. Da sai su dawo mata da hakkinta da farko, sannan kuma dawowa duk wanda suka kwace hakkinsa daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), daga ciki har da khalifancin Amirul muminina da suka kwace sannan su nemi afwarta. Amma afawa ba tare da yin haka ba, wasa ne da hankalin masu hankali.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.