Assalamu alikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake
saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku
kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan
wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Shahid Aya. Murtadha
Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana Jalaluddin Rumi. Ko
kuma cikin wasu littafin. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu day a gaba
a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon All..(s) kuma mahaifiyar
Alhassan da Alhussain (a) da muke kawo maku, mun tsaya inda ta zargi Khalifa
na daya da kwace hakkinta, sannan shi kuma ya maida martani da wani hadisi
wanda yam jinginawa manzon All..(s) inda yake cewa: Mu annabawa ba’a
gadommu, duk abinda muka bari na dukiya mai jibantar al-amarin musulmi a
bayansa ne zai yi abinda yaga ya dace das hi.
Sannan mun ji irin maida martanin da yayi masa. Na kan cewa mahaifinta bai
taba sabawa alkur’ani ba, kuma Alkur’ani mai girma a cike yake da hujjoji
wadanda suka tabbatar da hakkinta na gadon mahaifinta daga ciki har da inda
All..yake cewa {..Ya gaje ni ya kuma yi gado a cikin dangin Yakubu} da kuma
inda yake cewa {Sulaimanu ya gaji Dawuda} da kuma inda ya bayyana hukunce
hukunce gado filla filla ba tare da ya fitar da iyalan annabawa daga cikinsu ba.
Sannan ta kammala da cewa, ransu ne ya sawwala masu abinda suka aikata,
sannan All..shi ne mataimakonsu a cikin wannan al-amarin.
Dagan an sai Khalifa na farko ya ce: All..da manzonsa sun yi gaskiya, kuma
diyarsa ta yi gaskiya, wacce ta kasance mabubbugar hikima, wurin shiriya da
jinkai, rukunin addinin, mabubbugar hujja, bana musanta gaskiyarki, kuma
karyata jawabinki ba, sai dai ga wadannan musulmi a tsakani na da ke, su suka
dora mani abinda na dauka, tare da amincewarsu gaba daya na amince. Su
suka tilasta mani, ina mai kaucewa hakan ko cancantar matsayin ba,
dukkaninsu shaida ne a kan hakan.
A nan bayan da ya ji martaninta da bayaninta da kuma hujjojinta daga ayoyin
Alkur’ani mai girma, da kuma hankali, wadanda ba wanda ya isa ya musantasu
ba, sai ya rasa abinda zai fada sai ya aza nauyin hakan kan sauran musulmi don
su suka zabeshi a matsayin Kahlifa suka kuma aza nauyin shugabanci a kansa
ba don yana son matsayin ba. Sannan yace su shaida ne, kan cewa baya yanke
wata shawara ba tare da su ba.
Sai dai abin tambaya a nan ita ce, shin mutane ne suka taru suka zabi Khalifa
Abubakar a matsayin Khalifan manzon All..(S) bayan wafatinsa? Ko dai ya faken
da wannan maghana ce, don baranta kansa daga laifuffukan da Zahra(s) ta ke
zarginsa da aikatawa?
Wanda ya karanta sirar manzon All..(s) har zuwa wafatinsa, ya san cewa a
sakifa ne sahabban manzon All..(s) mafi yawansu Ansar suka yiwa Khalifa na
farko bai’a, shi dimma tare da jayayya mai tsanani a tsakaninsu. Duk da haka
Sa’ad dan Ubada shugaban kabi aws yaki amincewa da bai’ar da aka yi masa,
kuma ya sha alwashin zai yake su har zuwa karshen rayuwarsa.
Sannan sauran sahabban da suka yi masa bai’a daga baya, ko an tilasta masu,
kuma an kodaitar das u an kuma yi masu alkawurrah. Banda haka ba’a nemi
shawarar Iyalan gidan manzon All..(s) ba wato Aliyu da amminsa Abbas
wadanda sune shugaban wannan babban gidan bayan wafatin manzon All..(s).
Amma ya ce mata karban shugabancin kansa da kuma abinda yake aiwatarwa
gaba daya taron sahabban manzon All…(s) ne suka zabeshi sannan tare da
shawararsu yake gudanar da al-amuran musulmi.
9
A lokacinda Zahra (s) ta ji haka sai ta juya kan mutane wadanda suke cikin
masallacin tana cewa:
Ya ku musulmi wadanda suke saurin karban zancen karya, wadanda ake hada
kai da su don su ana aikata ba dai dai ba! {Shin basa tuntuni a cikin Alkur’ani
ne, ko dai an rufesu da abin rufewarsu ne}. Babu sai dai zukatanku ne suka yi
tsatsa saboda laifuffukan da kuka aikata, sai ya rufe kunnuwarku da kuma
idanunku, kuma tir da abinda kuka yi tawali na Alkur’ani, da kuma munin
abinda kuka kwace, na rantse da All.. zaku sami abinda kuka dauka yayi maku
nauyin, sannan sakamakonsa yana da wuya, idan an yaye maku labule da ke
hanaku ganin gaskiya, abinda yake bayansa ya bayyana a gareku, sannan
Ubangijinku ya bayyana maku abinda baku tsammani ba {A can ne mabarnata
zasu yi asara}.
A wannan bangaren na khudubarta, Zahra (s) ta gabatar da maganarta ga
mutanen da suke cikin masallaci wadanda Khalifa na farko ya tare da yardarsu
yake gudanar da duk abinda yake gudanarwa a shugabancinsa. Inda take
zarginsu da amincewa da wannan jagoranci na bata. Sannan ta kara da cewa
‘shin basa karanta alkur’ani ne?’ ko dai an dode zukatansu ne, ? sannan ta
tabbatar da cewa sun sani da yardarsu ake wannan zaluncin, kuma zasu yi
nadama a lokacinda aka yaye labulen ko shamakin da ya hanasu ganin gaskiya
a wannan duniya, a lokacinda zasu yi nadamar da ba zata amfanesu ba, kuma
zasu tabbatar da cewa sun yi asara, asara babba kuma babu damar komawa.
Mai littafin Kashful Ghumma, ya kawo cewa bayan wannan Khudubar Zahra(s)
ta wuce zuwa kabarin Mahaifinta wanda yake kusa da masallacin sai ta jefa
kanta a kan sa, tana rare baitoci wadanda Hindu diyar Abban dan
Abdulmattalib ya saba rerawa. Daga nan sai yace bamu taba ganin yadda maza
da mata suka yi kuka kamar rannan ba. A lokacinda Zahra (s) ta tabbatar da
10
cewa wadannan mutane biyu, wato Khalifa na farko da kuma na biyu ba zasu
maida mata hakkinta ba, sai ta koma gida sannan ta daga hannyenta masu al-
barka tana cewa: Ya Ubangiji, wadannan mutane biyu lalle sun zaluncen diyar
manzonka (s) sun kwace hakkinta, “ya Ubangiji” ka azabtar da su azaba mai
radadi.
A cikin littafin Sahi Bukhari, a kuma cikin babin Khumusi ya kawo cewa, …bayan
wata maga—don haka Fatima (s) diyar manzon All..(s) ta yi fushi, sannan ta
kauracewa Abubakar kuma ta ci gaba da fushi da shi har ta bar duniya.’.
Har’ila yau a cikin Bukhari, a kuma babin asalin halatun All..’ yana cewa,
“Abubakar ya ki mayarwa Fatimah (s) ko guda daga ciinsu, sai ta yi fushi, ta
kuma kaurace masa bata Magana da shi har da bar duniya’. ‘
Muslimu dan Hajjaj ya ruwaito hadisi mai kama da wannan a cikin sahihinsa, a
cikin babin Jihadi, hakama Baihaki ya kawo a cikin Sunan, Ahmad bin Hambal a
cikin Musnadinsa, sannan Ibn Sa’ad ya kawo a cikin Tabakaat Assahaba, da
sauransu.
Ibnu Abil Hadid mai sharhin Nahjul Balagh ya bayyana cewa, bayan khudubar
Zahra (s) da tasirinsa a cikin Sahabban manzon All..(s) a lokacin, har’ila yau da
kuma yadda suka ta kuka bayan Khudubar, hankalin Khalifa na farko ya tashi ya
kuma tsorata, sannan yayi tsammanin mutane zasu yi masa tawaye, sai ya hau
mimbari a masallacin manzon All..(s) ya fara Khuduba yana cewa:
Ya ku mutane, me yasa kuke rikicewa kan ko wace irin Magana? Ina wannan
ra’ayin a ruwar manzon All…(s), Ku saurara, wanda ya ji ya fada, wanda ya
shaida ya bada shaida, abin sani kawai shi ni, dila ne wanda shaidarsa shi ne
bindinsa, yana rako da duk wata fitina, yana nan kamar wanda yake cewa ‘Ka
sabontashi bayan ya tsufa’ wadan nan sune wadanda suke neman taimako
11
daga raunana, kuna neman taimako daga mata, kamar Tihal, wacce mafi
soyuwa a gareta a cikin danginta ita ce karuwa’ Ku saurara da na so nayi
Magana da na yi, kuma da nayi Magana da na daidaita kome. Amma na yi shiru
matukar ba’a tabani ba.
Sannan ya juya zuwa wajen Ansaru (wato mutanen Madina, yana cewa: Ya ku
mutanen Ansar, zancen wasu wawaye daga cikinku ya riskeni, kune mafi Daraja
daga cikin wadanda suka yi zamani da manzon All..(s), Ya zo maku kuma kun
taimake shi kun bashi mafaka. Ko saurara nib a zan yi ammafi da karfin
hannuna da harshe na a kan wanda bai cancanci haka daga cikimmu ba.’
Wannan shi ne zancen Khalifa na farko bayan Khudubar Zahra(s). Amma Ibnu
Abil Hadid wanda ya rubuta sharhin littafin Nahjul Balagha, yace: Na karanta
wannan maganar ta Khalifa na farko ga malami na Abi Yahyah, Jaafar dan
yahyah dan Abi Zaidu Albasri, sannan n ace masa: Wa yake nufi da
maganarsa,? Sai yace: Ai ba a boye yake ba, a fili yake? Sai yace: inda da a
bayyane yake da ban tambaye ka ba! Daga nan sai yayi Dariya, sannan yace:
Yana nufin Aliyu Dan Abitalib (a). Sai nace: Maganarsa gaba daya yana nufin
Ali(a)? Sai yace: Ee, wannan shi ne iko Ya da na!. Sai nace : To me yasa yayi
Magana da Ansar? Sai yace: Sun amsa kiran Ali(a). Don haka ya ji tsoron cewa
zasu rikice bayan abinda suka ji. (a Khudubar Zahra(s). don haka ya ja
kunnensu. Yace: sai na tambaye shi dangane da wasu maganganun da yayi ciki
khudubarsa bayan Khudubar Zahra (s). Kamar inda y ace: ‘Dila ce wacce
shaidarta itace bindinta’ Sai yace: Karin Magana ce wacce take nufin, bai da
wata shaida masa kan abinda yake ikrari nasa ne sai na jikinsa.
Yace asalin maganar ana cewa, wata rana dila tana son ta ingiza zaki don ya
kashe kora, sai ya fadawa zaki, Kora ya cinye ragomka da ka ajiye don amfanin
kanka, sai Zaki yace: Wa ye shaidarka, sai Dila ta danga bindinta, wanda yake
12
mulmule da jinni, ya ce masa ga shaida nan, a nan sai Zaki ya fusata, don ya
rasa Ragonsa ya je ya kashe kore.
Sai na tambaye shi menen yake nufi da ‘Sabonta shi bayan ya tsofa’ . Sai yace:
Sake sabonta shi abin bayan ya wuce, kuma yana nufin sake tada fitina(ta
neman hakkin Khalifanci bayan an kashe maganar a baya}’.
Sai kuma Ummu Tihal wata mata ce a jahiliyya wacce bata da tsarki, a zamanin
jahilia kafin zuwan addinin musulunci kuma ana amfani da sunanta a Karin
maganar da ta dace da irin yadda take. Karin maganar ita ce “ Wanda yafi muni
a rashin tsarki daga Ummu Tihal’. Don haka ma’arsa a nan ‘wacce tafi muni
daga Ummu Tihal’.
A nan ba abinda zamu iya fada dangane da abinda Khalifa na farko ya fada, kan
Imam Ali (s) da kuma Matarta Fatima (s). wadanda Ayoyin Alkur’ani mai girma
suka tabbatar da tsarkinsu da kuma kubutarsu daga aikata duk wani sabon All..,
Sai dai zamu ce, All..da manzonsa suna ganin yadda aka wulakanta Diyarsa mafi
soyuwan halittu daga cikin iyalan gidansa, sannan sun ji abinda ake dorawa
dan’uwansa kuma jaruminsa a duk yakokinsa har’ila yau wasiyyinsa a bayansa.
A cikin shirimmu na gaba zamu ji maida martini Ummu Salma Ummil muminina
(r ) dangane da maganar Khalifa na farko dangane da da Zahra da Ali (s) bayan
Khudubar Zahra (s).
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata
Fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.