Kissoshin Rayuwa Fatimah (57)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu dasake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawomasu kissoshi wadanda suka zo cikin

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da
sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo
masu kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin
wasu litattafan wanda suka hada da littafinDastane Rastan da Aya. Shahid
Murtadga Mutahhari, ko kuma cikin littafin Mathnawai na maulana
Jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu
kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya
gabata a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) da muke kawo maku, mun
bayyana yadda aka yi bikinta na aure da Aliyu dan Abitalib (a). Mun kuma
bayyana yadda manzaon All..(s) ya kawo alfadari ya Sanya mashi sirdi
sannan ya cewa Zahra (s) ta hau san ya fadawa salman a lfarisi ya ja shi
daga gaba sannan shi kuma yana korarsa daga baya.
Mun kuma ji yadda mala’iku 70,000 tare da Jabra’ilu suka sauka sannan
wasu dubu 70 tare Mika’ilu suka sauka don rakiyar Zahra (s) zuwa gidan
Mijinta, banda haka, sun ci gaba da zikiri da ambaton All..har gari ya waye.
Sannan munji yadda manzon All…(s) ya kurkura ruwa a bakinsa ya tofa a
cikin kwano sannan ya yayyafa shi a kan Zahra (s) da kirjinta da kafadunta
haka ma yayi wa Aliyu (s) sannan yayi masu addu’a ta neman albarkar All..
a auren nasu, da kuma zuriyyar da zasu Haifa. Sannan ya fita.
Daga karshen mun ji dan bayani dangane da Asma’u diyar Umais Matar
Jaafar dan Abutalib (a) inda malamai suka rikice kan yadda ta ruwaito
hadisai da dama dangane da wafatin Khadiza, da auren fatoma (s) da
tarewar Aisha matar manzon All..(s), da haihuwar Hussain (s). inda mai
littafin ‘Fatimatuz Zahra minal Mahdi ilal Lahadi’ wato sayyeed Muhammad

Kazim Alqazwini ya bayyna cewa gaskiyar al-amarin shine ita da mijinta
jaafari sun yi ta kai kawo tsakanin Habasha da Makka, da kuma madina
wanda ya bata damar halattar dukkan wadannan al-amuran da aka
ambaceta a cikinsu.
Don haka gaskiya ne ita ce ta ruwaito wadannan hadisan gaba daya,
amma malaman tahiri basu gano haka ba. Ko basu kawo hakan a cikin
tunaninsu ba.
A cikin shirimmu nay au zamu fara da sanin al-amuran da suka shafu
Ummu Salman ummulmuminina (s).
Da farko akwai matsalar lokacinda manzon All..(s) ya aureta, malamai da
dama sun bayana cewa ya aureta a shekara ta 4 bayan hijira, sannan mun
san cewa auren Zahra (s) ya kasance a shekara ta 2 bayan hijira bayan
yakin Badar kuma kafin yakin Uhudu, ta yaya manzon All..(s) ya bata ajiyar
sauran sadakin Zahra ya kuma wallaka wasu al-amura da dama na Zahra
a lokacinda bata zama matarsa ba.
Malamai sun yi maganganu da dama a kan haka, inda suke fada mai yuwa
ya aure kafin auren Zahra(s) ko kuma mai yuwa auren Zahra (s) ya
kasance a cikin shekara ta 4 ne bayan hijiya.
Ammma ni- wato sayyid Muhammad Kazim Qazwini – ina ganin wannan
batun za’a warware shi ne ta hanyar sanin cewa ita Ummu Salma diyar
ammar manzon All..(s), don haka mai yuwa wasu al-amuran da ake
danganta mata, sun auku ne tun bai aureta ba. Wato tun kafin mijinta na
farko Abdullah dan Abdulasad ya yi shahada a shekara ta 4 bayan hijira
sanadiyyar raunuka da ya ji a yakin Uhud. Sannan ta auri manzon All..(s) a
shekara ta 4 bayan hijira bayan wafati ko shahadar Abdullah dan

Abdulasad (a). Wannan shi ne muke ganin hanyar warware wannan al-
amari na ummu salama (a). All… ya fi sani.
Amma menen matsayin gidan Fatimah (s), a wajen All..da manzon All..(s).
Ko wa ya sani a wannan zamani, an fara gano matsayin wuraren tarihi,
kuma an himmatu da shi da kuma hatta matsayin wasu magabata. Don
haka aka kafa dokoki don kiyaye tarihi, da kuma mutanen tarihi. Yana daga
cikin ayyukan hukumar UNESCO ta MDD kiyaye wadannan al-amura don
al-ummu masu zuwa. Don kuma sanin matsayin wadannan wadannan
magabata a cikin wannan rayuwar da kuma ta gaba.
Amma a wajen All..T wadanda mutane ko kuma wurare na tarihi suna da
matsayi a wajen All..da kuma waliyyan All…don haka, ake girmama wurare
masu tsarki kamar masallatai da kaburburan waliyyan All.. daga cikin
annabawa da manzanni da limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon
All..(s). Haka ma mala’iku suna zuwa wadannan wurare masu tsarki. An
kuma hana kawo najasa a cikin wadannan wurare
Kuma saboda haka ne addinin musulunci ya hana mutanen wadanda basu
da tsarki shiga wadanan wurare, kamar masu janaba da masu haila da
sauransu. Da mushrikai ko kuma duk abinda zai Sanya kazanta a cikinsa.
Har’ila yau an haramta misali yin farauta a haramin Makka ga mahajjata
saboda mutunta hurumin wadannan wurare masu tsarki.
An ruwaito cewa a zamanin sarki Haruna Rashid daya daga cikin
sarakunan abbasiyawa ya je, ya je farauta a wajen birnin kufa wani lokacin,
sai ya ga wata barewa ya saki karensa, amma a lokacinda ta je ta hau kan
wani tudun sai karen ya juya baya ya barsji, ya yi haka har sau uku.
Wannan yasa yayi shakkar cewa akwai wani abu a kan tudun nan wanda

yake boye ga mutanen amma dabbobin nan suna ganinsa. A lokacinda ya
zurfafa bincike sai aka gano cewa nan ne kabarin Aliyu dan Abitalib (a). da
haka kuma aka samar da garin Najaful Asharaf. Wasu kuma sun bayyana
cewa daya daga cikin limamai masu tsarki na iyalan gidan manzon All..(s)
ne suka nuna inda kabarin yake.
Don haka kowa ya san kabarin irin wadannan waliyan All..a cike suke da
mala’iku da kuma abubuwa masu tsarki.
Bayan ambaton wannan mukaddimar yakamata musan cewa gidan
Fatimatuz Zahra (s) na daga cikin wadan nan gidaje, ko kuma wurare masu
tsarki. Gidan da Fatimah (s) take rayuwa gida ne wanda mala’iku suke
sauka, sannan hasken annabci yake yaduwa a cikinsa. Hakama gida
wanda bai kamata marasa tsarki ko kuma kazanta ya je kusa da shi ba,
wannan tabbataccene ga duk wanda ya san Fatima (s) da kuma hakkinta
da matsayinta a wajen All..T, a kuma wajen Mahifinta cikamakin annabawa
da manzanni(s).
Wannan tabbatacce ne ga wanda ya san Fatima da babanta da mijinta da
kuma yayanta (a).
Allamah Majlisi, ya ruwaito daga daga Anas dan Maliku, daga kuma
Buraibatul Aslami yana cewa,: Manzon All..(s) ya karanta
{A cikin waɗansu gidãje waɗanda Allah Yã yi umurnin a ɗaukaka
kuma a ambaci sũnansa a cikinsu, sunã yin tasbĩhi a gare Shi a
cikinsu, sãfe da maraice.} Noor 36,
Sai wani mutum ya tashi ya ce: Wadanne gidaje ne ya Manzon All..(s) Sai
Yace: Gidajen Annabawa. Sai Abubakar ya tashi ya ce: Ya manzon All..!

Wannan gidan yana daga cikinsu ? ya nuna gidan Fatimah! Sai ce: EE,
yana daga cikin mafifitansu.
An karbo wani hadisin daga dan Abbas yana cewa: Na kasance a cikin
masallacin manzon All..(s) , sai wani mai karatu ya karanta:
{A cikin waɗansu gidãje waɗanda Allah Yã yi umurnin a ɗaukaka
kuma a ambaci sũnansa a cikinsu, sunã yin tasbĩhi a gare Shi a
cikinsu, sãfe da maraice.} Noor 36,
sai nasce: Ya manzon All..(s): Wadanne gidaje ne ? Sai manzon All..(s)
yace: Gidajen annabawa! Sai ya nuna gidan Fatima (s).
Daga cikin littafin Kafa, an karbo daga Jabir Dan Abdullahil Ansari y ace:
ManzonAll..(s) ya fito daga gidansa yana son zuwa wajen Fatimah(s), ni
kuma ina tare da shi. A lokacinda muka karasa zuwa kofar gidan, sai ya sa
hannunsa ya ture kofar, sannan yace: Assalamu Alaikum. Sai Fatima (s)
tace : Alaikumussalam ya manzon All..(s).
Sai yace: In shiga? Sai tace: Ka shiga ya manzon All..(s). Sai yace: In
shiga da wanda yake tare da ni? Sai tace: ya manzon All..bani da hijabi,
Sai yace: Ya Fatima, ki kama ragowar mayafinki ki rufe kanki da shi, sai ta
yi hakan.
Sannan ya sake cewa: Assalamu alaikum! Sai tace : Wa alaikumus Salam
ya manzon All..(s). Sai yace : In shiga? Sai tace: Ka shiga ya manzon
All..(s). Sai yace: Ni da wande yake tare da ni? Sai tace: Kai da wanda
yake tare da kai… har zuwa karshen Hadisin.

Wannan shi ne yadda manzon All..(s) yake shiga gidan diyarsa Fatima (a),
shi kadai ko kuma shi tare da wani. Don girmamata da girman da All..T yayi
mata a matsayin yar gidan annabci.
Baya shiga gidanta sai yayi sallamah, kuma idan yana tare da wani sai ya
nemi izinin shigarsu tare don ta Sanya suturan da addinin musulunci ya
dora mata. Sannan a cikin wannan hadisin zamu fahinci cewa da shi kadai
ne zai shigo, bata bukatar da rufe kanta da mayadi saboda babantane
muharraminta ne.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata
fitowa idan All..ya kaimu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments