Kissoshin Rayuwa Azzahra(s) 70

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawai na maulana jalaluddin Rumi ko kuma dai ciki wasu littafan da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar shuwagabannin samarin Aljanna, Alhassan da Alhussain da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi maganar yadda aka yi jana’izar Zahra (s) a asirce a cikin dare. Kuma an yi haka ne saboda wasiyyar da ta bari, kan kada wasu wadanda suka cutar da ita su yi mata sallah.

Sannan bata son su ziyarci hatta kabarinta, don haka ta bukaci a boye kabirinta(s).

Imam Ali (a) wanda shi ne zai aiwatar da dukkan wasiyanta(s), ya sa aka tona kaburbura akalla 7 a bakiyya don kada a gane inda kabarinta yake. Don haka ne malamai suka yi sabani kan inda kabarinta (s) yake. Wasu sun ce an yi mata kabari ne a gidanta, don haka, idan hakan gaskiya ne to kuwa a halin yaznu kabarinta(s) ya na cikin masallacin manzon All..(s) dake Madina. Wasu kuma suke ce a bakiyya ne aka bisneta. Amma dai har yanzun ba a san inda take idan har tana bakiyya.

Don haka All..ya karbi addu’arta ya kuma boye kabarinta, saboda masu hankali daga cikin al-ummar mahaifinta su yi bincike don su gano abinda yasa ba san inda kabarinta yake ba.

Sannan mun ji yadda shuwagabanni a lokacin suka ji zafin yadda ta hanasu sallar gawanta mai tsarki, sai suka zabi wasu mata a madina su tona dukkan sabbin kaburbura a bakiyya, don su gano inda aka bisneta su fitar da ita su kuma yi mata sallah. Amma Imam Ali (s) ya sanya kayan yakinsa, ya dauki takobinsa zulfikar ya kuma rantse da All..sai ya shayar da kasa jinin duk wanda ya taba daya daga cikin sabbin kaburra da suka bakiyya a lokacin.

A lokacinda suka fara taurin kai, sai ya daga khalifa na biyu ya kadashi a kasa, sai da khalifa na farko ya ceceshi ya kuma yi alkawalin ba zasu yi abinda ba ya so ba.

A ci gaba da karshen sirar Fatimah (s), zamu ji cewa Imam Ali (s) bayan wafatin Fatima (s) ya zauna a gidasa baya fita sai don sallar Jama’a da kuma ziyarar kabarin manzon All..(s). in ba haka ba yana gida, ya na kuma ya waita kuka.

A cikin littafin Anwar Al-alawiyya, an kawo cewa, Ammar dan yasir (r ) yace: Na je gidan shugabana kuma jagorana Aliyu dan Abitalib (a) (bayan wafatin Fatimah (s)), na nemi izinin shiga sai ya ce in shigo. Da na shigo sai na sameshi yana zaune, zaman mai bakin ciki, sannan Alhassan da Alhussain(a) suna zaune a dama da hagunsa, sai ya na sami cewa shi ya kuka, nima na yi kuka mai tsanani saboda kukansa.

A lokacinda na dawo cikin hayyacina, na kuma sami nutsuwata, na daina kuka, sai na ce masa, ka yi mani izni in yi Magana ya shugabana, sai yace: kayi Magana! ya kai baban Yaqzan,  sai na ce: Ya shugaban na, kun umurci mutane da hakuri, kan musibun da suka samesa, menene wannan bakin ciki mai tsawon da kuke yi…?

Sai ya juya wajena, sai ya ce: Ya Ammar! Lalle bakin cikin irin wanda na rasa yana da girma. Lalle ni na rasa Manzon All..(s) da rashin Fatimah (s).

Lalle ta kasance a karan kanta mai tunatar da mu manzon All..(s) ne,  sannan samuwarta ya ke bamu hakuri na ntsuwa. Idan ta yi Magana muryarta na tunatar da ne muryar manzon All..(s), tafiyarta na tunatar da ni tafiyar manzon All..(s). Gaskiyan al-amarin ban ji zafin wafatin manzon All..(s) sai bayan wafatin Fatimah (s).

Don haka rashinta shi ne babban rashi a wajena. A lokacinda na sanya ta kan wurinda na yi mata wanka, sai na sami cewa da ya daga cikin kasusuwan awazarta ya karye, sannan akwai bakin tabo daga gefen jikinta, saboda bulalanda aka yi mata, ta yi ta boyesu gareni, don kada ta kara fusatani.

Sannan ba lokacin da zan kalli Alhassan da Alhussain(a) sai na zubar da hawaye. Hakama idan na ga Zainab ta na kuka sai zuciyata, ta sosa don tausaya mata.

Banda haka malamai sun yi sabani dangane da ranar wafatinta(s). Kamar yada suka yi sabani kan ranar haihuwarta(s). Wasu sun ce an haifeta kafin annabci a cikin jahilyya a yayinda wasu kuma, musamman su iyalan gidan manzon All..(s) sun bayyana cewa an haifeta ne a shekara ta 5 bayan fara annabci sannan halittarta daga aljanna ce. Bangarenta Hurul’ini ce

Banda haka sun yi sabani kan yawan shekarunta, don sun yi sabani kan ranar wafatinta(s). Al-Yakubi ya bayyana cewa ta rasu bayan manzon All..(s) da kwanaki 30 ko 35. Wannan shi ne mafi karanci daga cikinsu.

Wasu kuma sun ce, kwanaki 40 bayan wafatin mahaifinta (s). Sannan ra’yi na uku ya ce ta yi wafatin bayan kwanaki 75 da wafatin mahaifinta (s) kuma shi ne ra’ayin mafi yawan malamai a mazhabar iyalan gidan manzon All..(s).

Wasu kuma sun ce ta yi wafati kwanaki 95 bayan manzon All..(s), shi me yana da karbuwa a wajen wasu malaman. Akwai wasu ra’ayoyin, sai dai tunda wasu kwanakin suna kusa da juna, ana kirin ranakun gaba daya, a matsayin ‘Ayyamul Fatimiyya’ wa to ranakun Fatimah (s), wato ranakun wafatinta (s).

A cikin irin wadannan ranaku ne a cikin watan Jamada-Aula, masu rera makoki sukan hau kan mimbarori su ambaci wani abu daga cikin rayuwarta(s), da matsayinta a wajen All..T da rayuwarta da mahaifinta (s) da kuma mijinta sannan daga karshe su ambaci wahalhalun da ta sha bayan wafatin mahaifin(s) da kuma yadda wafatinta ya kasance, da kuma yadda aka yi mata jana’iza a asirce.

Sai dai duk tare da cewa an kwace gonar Fadak daga hannunta, Zahra(s) ta barwa yayanta wasu gonaki guda 7, wadanda ta barsu a hannun Amirulmuminina (a) bayan shahadarsa, zasu kaura zuwa hannun Al-hassan(a), sannan Alhussain(a) sannan zuwa hannun mafi girma daga cikin jikokinsa, Imam Muhammad Akbakir(a).

Muhammad bin Ya’akub Al-kulaini ya kawo a cikin littafinsa Al-kafi yadda wasiyyar kula da gunakin ta kasance.

Da sunan All..mai rahama mai jinkai, wannan shi ne abinda Fatimah Diyar Muhammad(s) ta bada umurni dangane da gonakinta guda 7, wato al-‘Awāf, al-Dalāl,  al-Burqah, al-Maythab, al-Ḥusnā, al-Ṣāfiyah da kuma Māl Umm Ibrāhīm, da farko ga Aliyu dan Abitalib(a), idan ya wuce Alhassan(a), idan ya wuce Alhussain(a), sannan daga nan sai mafi tsofa daga cikin jikokinna.

All..ne maishaida, sannan Miqdad dan Aswad da  Zubair dan Awwam,  kuma Aliyu dan Abitalib (a) ne ya rubuta da hannunsa.

Abin tambaya ita ce, ta yaya Zahra(s) ta sami wadannan gonaki guda 7? Asam’udi ya bayyana cewa akwai wani malami bayahude daga kabilar Banu Nadhir a Madina da ya musulunta, ya kuma yi shahada a yakin Uhudu. Sunansa ‘Mukhayriq’, ya bada gonakinsa guda 7 ga manzon All..(s), wanda daga baya mjanzon All..(s) ya badasu ga Zahra (s) a shekara ta 7 bayan hijira.

Kafin haka, manzon All..(s) yakan yi amfana da albarkatun gonakin, a lokutan da ya ke karban baki, ko kuma don wata bukata.

Bayan haka ta bukaci a bawa aukiya 12 (mai kimar dirhami 480) na amfanin wadannan gonaki ga ko wacce daga cikin matan manzon All..(s) 9. Sannan takan bawa ko wacce daga cikin mata Hashimawa daga albarkan gonakin. Sannan tana bawa Umamatu diyar Abis Ass. Diyar yarta Zainab (a).

Idan zaku tuna, a cikin shirye-shiryemmu a baya, Fatimah (s) ta fadawa Imam Ali (s) a lokacin wafatinta, kan cewa ya auri diyar Zainab yayarta, wacce ake kira Umamah, ta ce Umama zata kasance ga yayanta kamar kanta.

Don haka Imam Ali (s) ya aureta bayan Fatimah (s) kuma wasu suka ce ta haifammasa da mai suna Muhammad Ausad, wasu kuma suka ce bata haihu ba.

Har’ila yau Umamah ta rayu a matsayin matar Imam Ali (a) har zuwa shahadarsa a shekara ta 40 bayahn hijira, sannan ita kuma ta rasu a shekara ta 50 bayan Hijira.

Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, a lokacinda Imam Ali(a) ya kusan kai ga sahada, ya fadawa matarsa Umamah kan cewa, idan yayi shahada kuma tana son aure, to ta auri Mughiratu dan Naufal.

Wasu sunce Imam Ali (a) ya ji tsaron kada mu’awiya dan Abusufyan ya aureta bayan shahadarsa.

Umama ta ruwaiti hadisai da dama daga Imam Ali (a). Malaman shia, musamman Sayyid Khoee,  sun sanyata cikin mata wadanda suka ruwaito hadisai da dama daga Imam Ali(a).

Mahaifiyar Umamah itace Zainab diyar manzon All..(s) wacce ta yi wafati a shekara ta 8 bayan hijira. Kuma itace babban diya, ga manzon All..(s) a cikin yayansa mata. (a). Sannan ta auri mijinta Abil Ass ne tun kafin bayyana musulunci.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa ramatulahi wa abarakatuh.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments