Kissoshin Rayuwa Azzahra (s) 63

Assalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo

Assalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahad Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana Jalaluddeen Ruma ko kuma dai cikin wasu littafan.  Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) shuwagabannin samarin Aljanna, da muke kawo maku, mun tsaya inda muka bayyana irin musibun da suka fadawa al-ummar musulmi saboda kauracewar da suka yiwa iyalan gidan manzon All..(s). Musibu wadanda Zahra'(s) ta fada wa wasu sahabban manzon All..(s) dangane da su, a cikin khubobinta guda uku wadanda ta yi masu. Ta farko itace, wacce ta yi a cikin masallacin manzon All..(s) sai kuma daya ga matan Madina wadanda suka ziyarceta a gidanta, da kuma wacce tayiwa wasu sabban manzon All..(s) ita ma a gidanta.

Mun kawo misalai da dama dangane da hakan. Inda muka fara da kissan Khalifa na uku Uthman bin Affan, da kuma yake-yaken da suka faru a lokacin khalifancin Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) da kuma yakin Hurrah a kusa da madinan manzon All..(s) da abinda Hajjaj dan Yusuf Athaqafi ya yi da yan shia a Kufa na kasar Iraki.

Mun bayyana cewa Hajja kadai ya kashe musulmi wadanda yawansu ya kai dubu 120 ko 130.

Mun bayyana cewa Aliyu dan Abitalib (s) yakan dauki Zahra (s) da yayanta Alhassan da Alhussain (a) a cikin dare, yana zuwa cikin madina, suna bi gida gida su na neman taimakon sahabban manzon All..(s) don dawo da hakkinsu da aka kwace. Sai dai dama daga cikinsu suna cewa, ya diyar manzon All..(s) a halin yanzu mun rika sun yiwa wannan mutum bai’a, da ace mijinki ya zo wajenmu kafin Abubakar, da bamu barshi ba.

Sai Imam Ali yana cewa: Kuna ganin in bar manzon All..(s) a gidansa ba’a yi masa Jaza’iza ba, in fito ina jayayya da wadannan mutane kan shugabanci ne? Sai Fatima(s) ta na cewa abinda Baban Hassan ya yi shi ne dai dai, sun aikata abinda All..zai yi masu hisabi a kansa.

Zahra (s) bayan ta kasa gamsar da mutanen madina wajen taimaka mata da mijinta (s) wajen maida hakkokinsu, ta koma gidanta tana kuka dare da rana. Kuka wanda ya sa wasu dattawa daga cikin sahabban manzon All..(s) suka zo wajen Amirulmuminina (a) suka fada masa, cewa: Ya Baban Hasan, Fatima(s) tana kuna dare da rana, bama iya birci a gindajemmu dare sannan bama iya fita da rana don yin ayyukammu na rayuwa. Da ka ce mata ta zabi dare ko kuma rana don kukanta.

A lokacinda ta ga Imam Ali (a) ya shigo wajenta(s), ya gan tana kuka babu tsayawa, sai da ganshi sai ta daina kuka kadan, Sai ya ce mata, ya diyar manzon All..(s) dattawan Madina sun zo sun bukaci in fada maki, ko kiyi kuka mahaifinki da rana ko kuma da dare, saboda basa iya barci saboda kokanci da baya yankewa. Sai tace, ya Baban Hassan, dadewata a cikinsu ba za iyi yawavba, ai lokaci kadan ne ya rage mani zan bace daga cikinsu, na rantse da All.. ba zan daina kukan rashin mahaifina ba, dare ko da rana. Har sai na hadu da mahaifi da shi manzon All..(s). Sai Amirulmuminina (a) ya ce mata, kiyi abinda kikaga dama ya diyar manzon All..(s).

A nan muna iya cewa wadannan dattawan madina basu san kimar da daraja da kuma matsayin manzon All..(s) ba, basu sanci kimar abinda suka rasa ba, basu san manzon All..kamar yadda ya dace su san shi ba. Da sun sanci yadda ya dace, da sun yi tarayya da diyarsa tilo, wajen kukan wafatin mahaifinta babu kakkautawa.

Da sun taimaka mata wajen zubar da hawaye kan rashin mutum mafi daraja a cikin daukkar mutane kamar mahaifinta manzon All..(s).

Amma inama da itace, tunda basu iya tarayyar da ita a kakun da takeyi ba, da sun yi shiru da yafi masu. Ina ma da, ba su yi kokarin hanata kukan mutum mafi girma da ta rasa kamar manzon All..(s) ba?.

Amma suna da gaskiya, don gwamnati ta lokacin ta hanasu kukan rashin shugaban halittu kuma shugaban annabawa manzon All..(s). don haka ya cancanta ga Fatima (s) ta ki amsa kiran dattawan Madina wadanda  basu san kimar abinda suka rasa na samuwar manzon All..(s) a cikinsu ba.

Daga nan sai Imam Ali (s) ya gina mata daki ko rumfa a kusa da makabartan baki’a, inda take yi ni tana kukan rabuwa da mahaifinta. Daga nan sai a duk sanda gari ya waye sai ta dauko Alhassan da Alhussain (a) ta sa su a gaba ta je makokinta a Baki’a ta yi ta kuka duk tsawon rana tana kewaye kaburburan da suke cikin makabartan. Tana tunawa da rashin mahaifinta. Sannan idan yamma ta yi sai Imam Ali (a) yakan je ya daukota ya dawo da ita gida.

Don haka wadanda kukanta yake damunsu sun huta da jin diyar manzon All..(sa) tana kokun mahaifinta dare da rana, don haka suna samun barci, mai zurfi ba tare da kukanta ba (s).

Assamhudi ya kawo a cikin littafinsa, Tarihin Madina Jz na 2 shafi na 95. Imam gazali yana cewa: mustahabbi ne yin sallah a masallacin Fatimah (s) a Madina. Wasu malaman kuma sun bayyana cewa, ana kiransa (gidan bakin ciki), inda Fatima (s) ta zauna a lokacin da take bakin cikin wafatin mahaifinta(s).

Hakama mawaka, sun bayyana a cikin kisidunsu, dangane da haka, inda daya daga cikinsu yake cewa:

Sun hana Batulu yin kuka a lokacinda ta zamo- Tana kukan Mahaifinta dare da Rana.

Daga nan ba’a dadeba sai Zahra (s) ta fara rashin lafiyanda, ba ta sake tashi ba. An karbo hadisi daga Imam Bakir (a) yana cewa, (a lokacinda ta fara rashin lafiyanta ta karshe) tana yawaita addu’a tana cewa:

“Ya hayyu ya qayyum! Ina neman taimakonka da rahamarka, ka taimaka mani, Ya Ubangiji ka nisantar da ni daga wuta, ka kuma shigar da ni Aljanna, ka sadar da ni da Muhammadu(s).”

A lokacinda Amirulmumina Aliyu dan Abitalib (a) ya ji tana wannan addu’ar, sai ya ce mata: All..ya baki lafiya ya kuma wanzar da ke. Sai ta ansa da cewa: Ya Baban Hassan, ina gaggawar haduwa da manzon All..(s).

An karbo hadisi daga Imam Aliyu Zainul Abidin (a), ya karbo daga mahaifinsa Imam Hussain (a) ya na cewa, a lokacinda Fatimah (s) diyar manzon All..(s) ta yi rashin lafiya,  ta yi wasiya ga Amirulmuminina (a) ya boye al-amarinta, kada ya bari a ji labarin halin da take ciki. Kada kuma ya bada izini ga wani ya shigo wajenta a lokacinda take rashin lafiyar. Sai yayi hakan. Ya kasance yana jinyarta da kanshi, sannan Asma’u diyar Umais tana taimaka masa wajen boye rashin lafiyarta …. Har zuwa karshen hadisin.

Fatuma(s) ta zabi Asma’u daiyar Umaice, duk da cewa a lokacin ita matar Khalifa na farko ne, ammam ta zabeta don ta yi mata jinya ta kuma kasance tare da ita a wannan lokaci na karshe a rayuwarta. Watakila saboda soyayya ta musamman dake tsakaninsu. Ko kuma don ta taba kasancewa matar Jaafar dan Abitalib, don haka tana daukarta a cikin Banu Hashim.

Kafin haka dai, Asma’u diyar Umais matar Jaafar dan Abitalib ce, a lokacinda Jaafar yayi shahada a yakin Mutatah a shekara ta 8 bayan hijira, Labari ya zuwa manzon All..(s) damgame da hakan, sannan ya kai ga kunnen matansa daga banushim suka yi ta kukan shahadarsa. Sannan ya shiga wajen Asma’u diyar Umais matar Jaafar, ya kira yayansa, yana ta shafar kansu, sai Asma’u ta tambaye shi , ko akwai labarin da ka samu dangane da Jaafaru ne, sai ya yi kuka (s) ya ce mata, All.. ya yawaita ladarki ya ke Asma’u Jaafar ya rasu. Sai ta daga murya tana kuka.

A lokacinda manzon All..(s) ya fita daga wajenta, sai ya shiga wajen diyarsa Fatimah, (s) yace mata, kiyi abinci wa gidan Jaafaru don sun shagalta da makokin Jaafaru.

Sai Fatima (s) ta tashi ta dauko garin fulawa, ta dama ta yi bredi mai yawa sannan ta hada da dabino ta aika gidan Jaafaru.

Sannan wani abin lura a nan shi ne, manzon All..(s) bai umurci Matansa da kuma daya daga cikin matan Hashimawa su yi hakan ba, sai ya umurci diyarsa Fatimah (s), saboda mai yuwa yana son ta sami wannan ladar mai yawa.

Mai yuwa kuma manzon All..(s) ya umurceta da haka ne, saboda irin yadda Asma’u diyar Umais ta kasance, mai khidima ga iyalan gidan manzon All..(s), sannan tana da halaye masu kyau, musamman kan abinda ya shafi iyalan gidan manzon All..(s) tun suna Makka.

Mai yuwa kuma manzon All..(s) ya fada mata kan cewa Asma’u diyar Umais ta kasance wajen mahaifiyarta Khadiza (s) a lokacin wafatinsa, kamara yadda muka fada a baya, don haka har ta yi mata wasiyya, kan cewa ta wakilceta a auren Fatima idan har ta rayu zuwa lokacinda za ta yi aure. Ta kasance kamar mahaifiyarta saboda yan matan da suka yi aurensu na farko suna bukatar iyayensu mata kusa da su.

Don haka mun san yadda Asma’u bintu Umaisa ta kasance a wajen Iyalan gidan manzon All..(s), kuma mun san irin taimakon da tayi da ayyukan da tayi a lokacin auaren Fatima (s). Sannan ta na daga cikin, ko kuma itace ta yiwa Fatimah (s) ungozoma a lokacinda ta Haifi Imam Hussain (a), wato danta na biyu. Sannan sauran matan suka taimaka mata.

Bayan shahadar Jaafar dan Abitalib (s) mijinta na farko, a yakin Mutatah, Khalifa na farko ya aureta har kuma ta haifammasa da mai suna Muhammad dan Abubakar. Wanda ta haifeshi jim kadan kafin wafatin manzon All..(s). wasu malaman tarihi sun bayyana cewa an haifi Muhammad dan Abubakar ne a Hajjin bankwana.

Amma duk da haka, Asma’u ba ta sauya, waila’arta da halayenta ga iyalan gidan manzon All..(s) bayan wafatinsa ba. Ta zama mai  cika alkawari da kuma binsu sauda kafa.

Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa a dai dai lokacinda mijinta na lokacin ya kwace khalifanci daga iyalan gidan manzon All..(s), sannan aka shiga yakin cacan baki tsakanin sabbin shuwagabanni bayan manzon All..(s) da kuma Banu Hashin, Asma’u ta zama barazana ga mijinta a lokacin. Don hakan bai karkata ra’ayinta da kuma biyayyarta ga iyalan gidan manzon All..(s) ba, wani lokaci a fili tana bayyana haka. Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa ta na zuwa gidan Zahra (s) ta yi masu khidima bayan wafatin manzon All..(s) tare da izinin mijinta Khalifa na farko.

Ko yaye al-amarin yakasance dai, mun ga cewa Fatima (s) ta na samun nutsuwa da Asma’u diyar Umais a duk sanda take wajenta, tana bayyana mata wasu asiranta, tana bayyana mata damuwarta, kamar yadda zata bayyanawa yarwanta. Tana daukarta daga cikin mutanen da tafi so, kuma wadanda suka fi kusa da ita.

Fatima (s) ta fadawa Asma’u diyar Umais a karshen rayuwarta kan cewa, na zama kasusuwa, sannan ga busheshen fata a kan kasusuwa na, me zaki yi mani? ke suturceni?, sai ta ce a lokacinda nake Habasha na ga yadda suke idan haka ya faru,       idan kinga dama inyi maki, sai ta bayyana mata yadda habashawa suke yi idan macce ta rame kamar haka, sai ta yi mata ta kuma ji dadin hakan har ta yi murmushi. Sun ce wannan shi me murmushinta na farko tun bayan wafatin mahaifinta manzon All..(s). To masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sau kuma wata fitowa      idanAll..ya kai wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments