Assalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahad Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana Jalaluddeen Ruma ko kuma dai cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) shuwagabannin samarin Aljanna, da muke kawo maku, mun tsaya inda muka bayyana abinda Zahra (s) ta fadawa matan Muhajirun da Ansar wadanda suka zo wajenta bayan khudubarta a masallacin mahaifinta manzon All..(s).
Mun ji har’ilayau irin zubar da jinnin musulmi da aka yi bayan da sahabban manzon All..Suka yi watsi da Ahlulbaiti (a), musamman Aliyu dan Abitalib (a) suka zabi khalifofin da suka gabace shi.
Musamman kuma bayan kissan Khalifa na ukku, Uthman bin Affan. Da kuma yake-yaken da suka auku a Jamal da siffin da Nehrawan a lokacin Khalifancin Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) na tsawon shekaru 4.
A yake-yaken nan guda uku kazal da suka dorawa Amirulmuminina (a) an kashe mutane kimani dubu 150.
Banda haka bayan da Mu’awiya dan abu Sufyan ya sami iko a kasar sham da wasu yankuna a cikin daular Musulunci, ya aika sojojinsa suka yi ta kashe musulmi wadanda suke karkashin ikon Amirul muminina (a). Sannan bayan haka a zamanin banu Umayya da Abbasiyawa wadanda suka zo daga baya, sun kashe muslmi da dama don kare kujerar sarautarsu.
A yakin Hurrah ga misali, a lokacinda mutanen madina wadanda suka yi tawaye wa Yazid dan Mu’awiya, bayan sun kashe kashe Imam Hussain (a) da sahabbansa a Karbala. Yazid dan Mu’awiya ya halattawa sojojinsa Madinan manzon All..(s) na kwanaki uku, ya basu damar su yi abinda suka ga dama, a lokacin. Don haka sojojin suka shiga gida- gida a Madina suna kashewa suna kuma kwace dukiyoyinsu suka kuma yi wa mata badare kiman 300 fyade, suka kashe na kashewa suka kuma kwace dukiyoyinsu. Banda haka matan Madina bayan wannan yakin, sun haifi shegu kimani 1000 a shekarar, wadanda ba’a san iyayensu maza ba..
Daga karshe munji yadda Muslimu dan Uqba ya tara mutanen madina ya tilasta masu bai’a, a matsayin bayin Yazid dan Mu’awiya. Kuma a dole suka yi hakan. Wannan duk sakamakon kuskuren da suka yi tun bayan wafatin manzon All..(s) da kuma kauracewa iyalan gidansa a shugabancin Al-ummarsa a cikin al-amuran shugabanci a a duniya da Lahira.
Daga karshe Muslimu dan Ukba ya wuce zuwa Makka inda a camma ya zubar da Karin jinin musulmi. Ya zubar da jinin Abdullahi dan Zubair wanda yake iko da Hijar a lokacin, wanda kuma ya sami mafaka a dakin Kaaba don kare kansa da kuma kubutar da kansa daga sojojin Muslimu dan Uqba. Amma bai tsira ba Don sojojin Muslimu sun kona dakin ka’aban kansa suka kuma kwace garin Makka a hannunsa.
Wannan banda abinda Hajjaj dan Yusuf Athaqafi gwamnan Abdulmalik dan Marwan yayi a garin Kufa na kasar Iraki. Idan mutum ya karanta irin kissan kiyashin da Hajjaj ya aikata a Iraki, sai ya gane cewa babu inda aka taba yin irin kiyashin da yayi a Iraki a wani lokaci a zamunan da suka gabata.
Malaman tarihi sun bayyana cewa, Hajjaj ya kashe mutane akalla dunu 120 ko 130, wadanda mafi yawansu shi’an Aliyu dan Abitalib ne.
Saboda munin abinda Hajjaj dan Yusuf Athaqafi ya yi a Iraki, ya kai ga Umar Dan Abdul’azi daya daga cikin sarakunan Banu Umayya yak e cewa: Da dukkan al-ummu suka zo da mafi muninsu a ranar kiyama, sannan muka zo da hajjaj da mun rinjayesu.
Wannan ya na Magana ne kan cewa ko da an zo da Fir’auna da Lamaruzu ko Bukhnasr, wadanda suka shahara a kissan mutane, to da abinda Hajjaj yayi da mutanen Iraki, musamman shi’ar Amirul mumnina (a) da sun rinjayi su da hajjaju dan Yusuf .
Wani malami da ake kira Asim yace: Hajjaju bai bar wani hurumi ga All..T da manzonsa (s) ba sai da ya keta shi.
Wannan kadan kenan daga cikin abinda Zahra(s) ta bada labarinsa a maganar ta da matana sahabbai kafin wafatinta (s) na musibun da zasu fadawa musulmi bayan kuskuren da suka yin a rashin taimakawa Ahlubaitin Manzon All..(s) ko kuma kauracewa shugabancisu bayan wafatin ma’aikin All..(s).
A karshen maganarta Zahra (s) ta fada masu irin musibun da zasu sami wannan al-ummar bayan karkatan da magabantasu suka yi, kuma ta ce masu su shiryawa gamuwa da bala’o’ii daban daban, wadanda shuwagabanni azzalumai wadanda za su azabtar da su da zuriyyarsu.
Suwaida dan Ghaflatah ya ce: a lokacinda Zahrau (s) ta kamala maganarta, sai matan suka fitoa suka je suka fadawa mazajensu, sai mazajen suka zo wajen Zahra (s) suna neman gafararta.
Sai dai malaman Tarihi ba su fada mana sunayen matan da suka fadawa mazajessu abinda Zahra ta fada masu, wanda kuma ya tada hankalinsu har suka zo suna neman afwarta da kuma bata hakuri ba, kuma basu fada mana mazaje daga cikin sahabban manzon All..(s) da suka je wajenta (s) suna neman uzurinta ba.
Abin mamaki da wannan uzurin, shi ne sun fadawa Zahra(s) ‘inda Baban Hassan ya bayyana mana al-amarin haka yake, da bamu kulla wata bai’a da wani ba”.
Ga mai hankali wanda kuma ya karanta sirar manzon All..(s) a musamman a karshen rayuwarsa da kuma lokacin mutuwarsa, wannan ba uzuri ne ba ne. Saboda, idan mun fara da ‘alkur’ani mai girma, ayoyinsa nawa ne? suka sauka wadanda suka tabbatar da cewa Aliyu dan Abitalib (a) shi ne wasiyyi kuma Khalifan manzon All..(s) a bayansa.
Shin basu yi wa Aliyu (a) bai’a a Ghadir ba?, kuma manzon All..(s) bai ce masu, wanda ya ji isar da shi ga wanda bai ji ba.
Tsakanin Ghadir da wafatin manzon All..(s) duk bai fi kwanaki 70 ba. Wani tunatarwa ne suke son Aliyu(a) ya yi masu bayan wafatin manzon All..(s).?. Don haka wannan uzurin bai yi ba, saboda, isgili ne ga All..da manzonsa (s) bisa duk abinda suka gabatar masu kafin wafatin sa (s).
Don sun isar da wannan sakon kamar yadda ya dace, kuma kamar yadda ba wanda zai isar da shi fiye da yadda suka isar da shi ba.
Shi ya sa Zahra (s) ta ce masu, su tashi su tafi su barta, saboda sun yi kuskuren da baza su taba gyaransa ba, kuma ita ta sauke nauyin da ke kanta, a khudubar da ta yi a masallacin mahaifinta a kuma gaban Khalifa na Farko.
Sun ji ta ta na jayayya da shi amma kuma suka kasa yin kome, a kan hakan.
Banda haka suna nan a Madina bayan wafatin manzon All..(s) da kwanaki, aka kama Aliyu (a) da karfi aka fitar da shi daga gidansa aka kai shi masallaci, aka ce masa yayi bai’a yaki yin haka. Ya kuma kawo masu hujjoji wadanda suke tabbatar da cewa hakkinsa ne suka kwace, kuma shi yafi cancanta su yi masa bai’a. wannan an yi shi a gaban kowa, tun farkon al-amarin.
Amma sun kasa yin kome, sun kasa tallafawa Aliyu (s) da kuma iyalan gidansa don dawo da al-amura kan hanya.
Banda haka, a sanda suka yiwa Khalifa na farko bai’a, sun manta da cewa akwai wata bai’a a kansu a Ghadir? Wacce manzon All..(s) ya umurcesu suka yi wa khalifansa na farko?. Don haka bai’ar da suka yiwa Abubakara, kwance wacce suka yiwa Aliyu(a) a Ghadir ne. Kwance wacce suka yiwa Aliyu dan Abitalib (s) a ranar 18 ga watan Zulhajjin shekara ta 10 bayan hijira a wani wuri da ake kira Ghadir tsakanin makka da madina ne.
Don haka ba yadda za’a ce sun manta da duk wadannan al-amura da suka faru, a lokacinda suka bi wasu shuwagabanni, ba iyalan gidan manzon All..(s) ba.
Abin mamaki shi ne, suna jin tsaron su warware bai’ar da suka yiwa Khalifa na farko, amma basa jin tsoron sun warware bai’ar da suka yiwa All..da manzonsa (s) a Ghadir.
Ayoyin Alkur’ani ne suka sauka a cikin suratul Ma’ida inda All…Yake cewa
{Ya kai manzon nan, ka isar da abinda aka saukar maka daga ubangijinka, to idan baka isar ba, kamar baka isar da sakonsa ne gaba daya, kuma All..zai kareka daga mutane}.
Wannan ayar ce ta sauka, sannan manzon All..(s) ya tsaya a Ghadir Khom ya yi khuduba mai tsawo a cikin zafin rana, ya daga hannun Aliyu (a) ya ce:
{Duk wanda ni shugabansa ne to Aliyu wannan shugabansa ne, All..ka jibinci wanda ya jibance shi ka kuma tabar da wanda ya tabar da shi..} har zuwa karshen hidisin Ghadir. Sannan bayansa ya saukar da wasu ayoyi inda ya bayyana cewa,
{A yau ne na cika maku addinku, na kuma kammala ni’imata a gareku, na kuma yerje maku musulunci ya zama addini..}.
Banda haka ya kari duk wadanda suke tare da shi, daga ciki har da matansa, suka yiwa Aliyu dan Abitalib (a) bai’a a matsayin shugaban Muminai a bayansa.
Duk tare da wannan sai Aliyu (A) ya tunatar da su bayan wafatinsa? kan cewa shi ne shugabansu bayan wafatin manzon All..(s)?.
Masu sauraro ya zuwa yanzu mun kawo maku khudubobin Zahra (s) har guda uku, wacce ta yi a masallacin manzon All..(s), da wacce ta yi wa Matan Muhajirun da Ansar a gidanta, da kuma wacce ta yiwa wasu mazaje daga cikin sahabban manzon All..(s) wadanda suka zo bata hakuri da gabatar da uzurinsu na nisantar iyalan gidan manzon All..(s).
Mun bayyana isnadin khudubarta ta masallaci a farkon khudunar, yanzun kuma ga kadan daga isnadin khudnar da ta yiwa matan Ansar da Muhajirun bayan wacce ta yi a masallacin mahaifinta manzon All..(s).
01-Littafin Ma’ani Al-Akhbar na shiekh babawaihi Al-kummi, wanda Fatimah diyar Hussain (s) ta ruwaito daga babanta Imam Hussain (a).
02-Daga Umar dan Aliyu, ya ruwaito shi daga mahaifinsa Aliyu dan Abitalib (a).
03-Sai Tabrisi ya kawo cikin littafin Ihtijaj daga Suwaidah dan Ghaflata. 04-Kuma sheikh Dusi ya ruwaito shi daga Abdullahi dan Abbas.
5-Sai Ibnu Abil Hadid cikin sharhinsa na Nahjul Balagha. 6- Allamah Majlisi ya kawo shi a likin Biharul Anwar Jz na 43.
Banda wannan Imam Aliyu dan Abitalib (a) a cikin tsawon rayuwarsa bayan wafatin manzon All..(s), bai bar wata dama, ko fursa ba, face ya tabbatar da hujja ta da nassi alkur’ani ko hadisi ko na hankali wadanda suke tabbatar da cewa khalifanci bayan manzon All..Hakkinsa ne, wanda All..T da manzonsa (s) suka bashi. Ya na yin haka duk da cewa ya san mutane da dama ba zasu amsa kiransa ba. Sai dai yana yin haka ne don ya tabbatar da hujja a kansu. Ta yadda wadannan hujjojin nasa (s) za su isa ga wadanda zasu zo daga baya a cikin wannan al-ummar manzon All..(s) su amfana da su, ko da wadanda aka kafa hujjoji a kansu da shi, basu amfana da ba.
Na biyu kuma, Imam Aliyu dan Abitalib (a) shi ne khalifan manzon All..(s) a bayan wafatinsa, mutane sun bi shi ko sun ki binsa. Kamar yadda yale aiko da annabawa zuwa ga al-ummun da suka shude ne, idan mutane sun ki binsu wannan ba zai All..a tube rigar annabci daga garesu ba.
Haka ma Aliyu (a) shi ne wasiyin manzon All..(s), an bi shi ko an ki binsa. Wadanda suka ki bansa su ne suka yi asara. Amma shi ba abinda za’a rage masa a matsayin da All..ya bashi.
Sannan, haka zamu fada dangane da gonar Fadak, hakkin Zahra (s) ne, an bata ko an hana ta.
Sai kuma batun goyon bayan Aliyu dan Abitalib (a) mijinta, Zahra tana goyon bayansa ne ba don shi mijinta ba, sai don shi ne yake kan gaskiya, da kuma matsayinsa a wajen All….T. ita ma tana da matsayin da All..T ya bata, a duniya da Lahari, kuma ba laifi ne ta kasance tare da mijinta ba, ta taimaka masa don neman hakkinsa wanda aka kwace ba. Kuma tayi hakan ne don neman alkhairi ga al-ummar mahaifinta da kuma don tabbatar da hujjar All.. a kan mutane. Zahra (s) ta tabbatar da hujjar All..a kan mutane, a lokacinda ta yi amfani da matsayin da take da shi a cikin al-ummar mahaifinta, ta kuma bi gida gida na mutanen Ansar da muhajirun tare da mijinta da kuma yayanta Alhasan da Alhussain (a) shugabannin samarin Aljanna, tana tunatar da su kan hakkinta da na mijinta wanda kuma All.. ne ya bashi. Babu wani aibi a cikinsa.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum warahamatullahi wa barakatuhu.