Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahad Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana Jalaluddeen Ruma ko kuma dai cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) shuwagabannin samarin Aljanna, da muke kawo maku, mun yi maganar kan yadda Fatima (s) ta fara shiryawa wafatinta, bayan mafarkin da ta yi da mahaifinta manzon All..(s) a wani dan guntun barcin da ta yi da rana.
Sannan munji yadda ta gabatar da wasiyoyinta masu yawa ga mijinta Amirulmumina Aliyun dan Abitlin (a) jim kadan kafin wafatinta. Ta yi masa wasiyya, kan al-amura da dama, daga ciki ta bukaci ya aure Umama diyar yar’uwamta, don za ta kasance ga yayanta kamar kanta.
Ta kuma yi masa wasiyyan kan kada ya bar wadanda ba ta son shi, su yi sallah, sannan ta bukaci ya boye inda kabarinta zai kasance.
Don haka a lokacinda ta ga alamun mutuwa, sai ta koma kan shimfidanta a tsakiyar gida, ta kwanta kan hannunta na dama, ta sanya hannun a karkashen kumatunta. Asma’u diyar Umais matar Ja’afar Attayyar, kuma matar khalifa na farko a lokacin tana tare da ita, akwai Fiddatu kuyangarta, sannan kafin haka ta kai yayanta mata, wato Zainab da ummu Khulthum da Ruqayya gidan da ya daga cikin Hashimawa don kada su ga yadda mahaifiyarsu zata bar duniyar.
Wannan zai rage masu mummunan halin da zasu shiga ciki, idan sun ji labarin wafatinta. Kafin haka kuma ta hadawa yayanta abinci ta ajiye.
Har’ila yau a dai-dai lokacin wafatinta (a), kamar yadda ya zo a cikin wani hadisi daga Imam Aliyu Zainul Abidan, yana cewa: Imam Ali da yayansa Alhassan da Alhussain (s) basa cikin gida a dai-dai lokacin rasuwar Fatimah(s).
A dai-dai lokacin rasuwarta, Asma’u diyar Umais tace: An yaye mata labuce, sai ta kafa idonta a bude na wani lokaci, sai Tace:
Aminci ta tabbata ga Jabra’il.
Aminci ya tabbata ga Manzon All..(s).
Ya Ubangiji, ina tare da manzonka (s).
Ya Ubangiji ina cikin yardarka, da kusancinka, da gidanka, gidan aminci (Darussalam).
Sai tace: kuna ganin abinda nake gani.?
Sai wadanda suke tare da ita suka ce: Me kike gani?.
Sannan tace: Ga wannan tawagar ma’abuta sammai.
Ga kuma Jibirilu, ga manzon All..(s), ya na cewa: Ya diyata, ki taho, abinda yake gabanki yafi maki Alkhairi.
Daga nan sai ta bude idanunta, sai tace: Ya mai daukan rayuka, aminci ya tabbata a gareka, ka gaggauta da ni, kada ka azabtar da ni.
‘Zuwa gareka ya Ubangiji, ba zuwa wuta ba.
A nan ta rufe idanunta, ta mike hannayenta da kafafuwanta, sai ta rabu da duniya.
Sai Asmau ta yayyaga aljihunta, ta fada kanta tana sumbantarta, tana cewa: Ya Fatimah idan kin je wajen mahaifinki ki isar masa da sallamar Asma’u diyar Umais.
Su na cikin wannan halinne sai Alhassan da Alhussain(a) suka shiga gidan, suka sami mahaifiyarsu tana kwance. Sai suka ce: Ya Asma’u, me yasa mahaifiyarmu take barci a wannan lokacin, ?.
Sai tace masu: Ya ku yayan manzon All..(s), mahaifiyarku ba barci take ba, sai dai ta bar duniya ne.
Sai Alhussain (a) ya ce: Ya dan’uwa na! All..ya yawaita ladarka, sannan sai Alhassan ya jefa kansa a kanta, yana sumbartan kafafunta, yana cewa: Ya umma! Ki yi mani Magana, kafin ruhina ya fice daga jikina.
Hakama Alhussain ya jefa kansa a kanta yana sumbantar kafafuwanta. Yana cewa: Ya ummah !! nine danka Alhassan!! Ki yi mani Magana kafin zuciyata ta fashe in mutu.
Sai Asma;u ta ce masu: Ya ku yayan manzon All..(s) ku je wajen mahaifinku, ku fada masa dangane da rasuwar mahaifinku. Sai suka fita suna kuka, suna cewa: Ya muhammadaa!! Ya Ahmadaa!! A yau an sabonta mana wafatinka, a lokacinda mahaifiyarmu ta yi wafati. Suna haka har zuwa lokacinda suka kai kusa da masallaci, sai suka daga muryoyinsu da kuka.
Sai wasu daga cikin sahabban manzon All..(s), suka yi gaggawa zuwa wasunsu, suka tambayesu abinda yasa suke kuka. Sai suka ce: Ai mahaifiyarmu Fatima (s) ta rasu. !!
Sai Imam Ali (s) ya fadi kasa, yana cewa: Wa kuma zai lallace mu, ya diyar Muhammad (s)!? Ke ce kike lallatarmu, a yanzun kuma wa zai yi hakan bayan ki.
Sai mai ruwayar ya ce: Sai Imam Ali (a) ya dauki Alhasan da Alhussain(a) suka koma gida. Suka samu Asma’u tana zaune kusa da gawarta, ta na kuka, ta na cewa ya ku marayun Muhammad.
A lokacinda idanunsa suka fada kan gawarta (s), sai ya cire rawaninsa ya jefa, ya cire, mayanin da ke wuyarsa ya jeafar, sai ya fara kuka da babban murya.
Daga nan sai ya bude fuskanta sai ya ga wata takarda wacce a cikinta aka rubuta: ‘Ya Baban Alhassan, ni ce Fatimah, Diyar Muhammad (s). All.. ya auraddani kai, don in kasance matar ka a duniya da lahira. Kai kafi cancanta da aurena kan kowa.
Ka sanya mani ‘Hamud’ (wato turare, kamar miski, Ambar, da Kafur da sauransu a jikin mamaci) bayan kayi mani wanka, ka sanya mani likkafani na cikin dare, ka yi sallah a gareni, sannan ka sanyani a kabarina a cikin dare.
Kuma kada ka fadawa kowa. Na barka cikin amincin All..sai ranar kiyamah, sannan ka isar da sallamata ga yayana.)
Daga nan sai kuka ta game Madina, Mutane maza da mata, suna ta kuka, kamar irin kukansu a ranar wafatin manzon All..(s).
Mata suka taru a gidan shugaban matan Al-Janna suna ta kuka, sannan suna ganin marayunta yayanta suna kewaye da ita, suna kuka, suna ganinta a kwace a cikin dakinta. Suna cewa, diyar Muhammadu (s) ta rasu a cikin kurcciyarta tana diyar shekara 18 cakal a duniyar.
Mutane sun yi tururuwa zu wa gidanta, suna kuka. Imam Ali (a) da ‘ya’yansa Alhassan da Alhussai (a) suna kuka a gabansa. Hakama sauran yayanta suna kuka. Ummu Khulthum tana kuka, tana cewa:
Ya babana ya manzon All..! A Yanzu ne hakika muka rasaka. Rashin da babu haduwa kuma har’abada.
Daga nan sai A’isha matar manzon All..(s) ta zo ta shiga, sai Asma’u ta hata shiga, sannan ta sanya haudaju a kan Fatimah(s). Sai ta juya ta fadawa babanta, khalifa na farko, ta ce: wannan akuyar ta hana ni shiga wajen diyar manzon All..
Sai Khalifa na farko ya zo kofar gidan, ya tambayi Asma’u kan cewa, me ya sa ta hana mantan manzon All..(s) shiga gidan manzon All..(s), sannan kika sanya Haudaju na uare a kanta?
Sai Asma’u ta ce: Fatimah (s) ce, ta umurce ni da hakan, tace kada wani ya shiga wajenta. Abinda tace in yi tana da ranta kenan, sannan ta umuceni da in yi haka bayan wafatinta.
Sai Abubakar ya ce: Ki yi abinda ta umur ce ki, sai ya juya ya tafi.
Sai Abubakar da Umar suka zo suna ta’aziyya ga Aliyu, suna ce masa: Ya baban Hassan kada ka rikamu sallah a kan gawar diyar manzon All..(s).
Sai Aliyu bai basu amsa ba. Sai Umar ya fadawa Abubakar kan cewa Aliyu bai amsa mana ba, don tsananin bakin ciki.
Mutane sun jira a fitar da Jana’izarta (s) sai Aliyu (a) ya umurci Ammar, ko salman a wasu ruwayoyi, kan su fadawa mutane an jinkirta Jana’izar a wannan daren. Sai Umar ya fadawa Abubakar kan cewa: Lalle suna son binneta a asirce ne. Da jin haka, sai mutane suka waste suna tsammanin za’a yi Jana’izar a gobe da safe. Don ta yi wafati ne bayan la’asar ko kuma a farkon dare.
Sai kuma a can cikin dare, gari yayi shiru, idanu sun yi barci. Sai Imam Ali(a) ya tashi, ya dauki gawarta mai tsarki, ya kuma kaita inda ya ajiyeta don yi mata wanta.
Imam Ali (s) bai tube mata kayanta ba, kamar yadda ta yi wasiyya, don haka a kan kayakinta aka zuba ruwa aka yi mata wanka.
Haka Aliyu (a) ya yi wa manzon All..(s) ba tare da ya cire masa kayansa ba.
Wata ruwaya daga Imam Hussain (a) ya ce, an yi mata wanka sau 3, sannan sau 5, sannan ya Sanya kafur kadan a wanka na karshe.
Banda haka, Asmasu diyar Umais ce ta kasance mai bashi ruwa a lokacin wankan. Sannan ya Sanya mata mayafi babba ba tare da Sanya mata wani abu ba.
Yana karanta wannan adduar, a lokacinda yake sanya mata mayafi babba. Yana cewa:
Ya Ubangi lalle baiwarka ce, diyar manzonka ce, tsarkakkiya, kuma zababbiyarka a cikin halittunka, Ya Ubangiji ka lakkana mata hujjarka, ga girmama dalilinta, ka daukaka darajarta, ka hada ta da mahaifinta Muhammad (s).’
A lokacinda ya gama wanka, sai ya Sanya ta a kan likkafaninta, sannan ya busar da ita da burgon da ya busar da manzon All..(s) da shi. Sannan ya Sanya mata Hanut watu ( hadin turaren, miski kafur da sauransu) daga sama, wanda ya bambanta da na duniya.
Kamar yadda muka bayyana a baya, Hanud da aka Sanya mata na wanda aka yiwa manzon All..(s) Hanud da shi ne. wanda Jibril (a) ya zo masa da shi daga Ajannah. Sannan ya sanyata cikin likkafini har guda 7.
Wadannan al-amura gaba daya daga wanka da likkafani da Hanut da sauransu, Imam Ali (a) shi kadai ne ya ya yi mata(s), bai nemi taimako wani daga cikin matan da suke tare da shi ba.
Kuma ya yi haka ne don aiwatar da wasiyanta,(s). Sannan yayi haka ne, don kasancewar su ‘Masumai’, baya halatta ga hannun wadanda suke yin zunubi, ya taba jikin wanda ya kasance, mai tsarki.
Kamar yadda Aliyu (a) shi ne ya yiwa manzon All..(s) shi kadai, hakama shi kadai ne yayi wa matarsa Fatimah diyar manzon All..(s).
Har’ila yau a baya mun kawo hadisi daga Imam Sadik (s) yana cewa Zahra (s) Siddikace, don haka ba wanda zai yi mata wanka sai wanda ya kasance siddik irinta (s).
A wani hadisi Imam Ali (a) yana cewa: Na yi mata wanke cikin kayanta, ban tube mata kayanta ba. Na rantse da All..ita abin yabo ne, kuma tsarkakakkiya ce, kuma mai tsarki ce, … har zuwa karshen hadisin.
Masu sauraro, saboda kurewar lokaci a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.