A wannan Alhamis ne miliyoyin mutanbe a fadin kasar Iran suka gudanar da gangami da jerin gwano domin tunawa da cikar kwanaki 40 na shahadar jagoran juyin juya halin musulunci Shahid Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.
A yauin tarukan an tar era taken la’anatar Amurka da Isra’ila da masu mara musu baya, tare da jaddada ci gaba da bin tafarkin shahid Ayatollah Khamenei.
Amurka da Isra’ila sun kaddamar da hari a kan gidan Ayatollah Khamenei ne a ranar farko ta yakin da suka kaddamar a kan Iran a karo na biyu,a ranar 28 ga watan Fabrarirun 2026.
Babbar manufar yakin dai ita ce rusa kasar Iran tare da kawo karshen gwamnatin juyin musulunci, tare da kafa wani sabon tsarin tafiyarwa a karkashin manufofin Amurka da Isra’ila.