Shuwagabannin kasashen Afrika da dama sun hadu da shugaban kasar Kenya a jiya Jumma’a don yiwa tsohon firai ministan kasar kuma shugaban jam’iyyar adawa ta kasar Raila Odinga Jana’iza.
Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa Odinga ya mutu a wani asbiti a kasar Indiya a makon da ya gabata yana dan shekara 80 a duniya, bayan dan gajeren rashin lafiya.
Raila Odinga ya tsaya takarar shugaban kasa har sau biyar amma ba tare da samun nasara ba, amma ya taimaka wajen tafiyar da harkokin siyasa wanda ya daidaita tsarin damocradiyya a kasar Ken a cikin shekaru 30 da suka gabata.
Da farko an ajiye gawar Odinga na wani filin wasanni a birnin Nairobi a ranar Alhamis inda mutane suka yi tururuwa don yin ban kwana da shi. An kaishi majalisar dokokin kasar namma don masa bankwana .
Shugaba Rudo ya bayyana cewa Odinga ya cancanci wannan girmamawar , ganin ya rike kujeru masu muhimmanci a kasar.