Rahotanni sun bayyana cewa kimanin kaso 8% na mambobin majalisar dinkin diniya ne suka sanar da amincewarsu da kasar falasdinu, a daidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da kisan kare dangi a Gaza kuma take kara fadada mamaye yankuna a gabar yammacin kogin jodan.
Kasaashen faransa, luxambourg , malta da manako ne suka sanar da amincewa da yankin falasdinu a matsayin kasar a wajen taron babban zauren majalisar dinkin duniya, prime ministan kasar kanada marka caney ya fadi cewa amincewar tana da muhimmanci sosai, kana yayi gargadin cewa an shafe batun yancin cin gashin kai ga yankin falasdinu.
Sai dai duk da amincewa da yankin na falasdinu a matsayin kasa, amma ta’addancin da Isra’ila ke yi a yankin gaza yasa an rufe wasu Asibitoci guda biyu,kamar yadda ministan lafiya na yankin falasdinu ya bayyana.