Kasashen Yankin Caribbean Suna Son Bunkasa Alakarsu Ta Kasuwanci Da Nahiyar Afirka

Sakatariyar kungiyar kasashen yankin Caribeans  ( Caricom) ta bayyana cewa; kasashen yankin suna son ganin bunkasa alakar kasuwanci da abokansu na nahiyar Afirka.  Sakatariyar kuniyar

Sakatariyar kungiyar kasashen yankin Caribeans  ( Caricom) ta bayyana cewa; kasashen yankin suna son ganin bunkasa alakar kasuwanci da abokansu na nahiyar Afirka.

 Sakatariyar kuniyar ta kasashen Caribbian ta bayyana hakan ne a lokacin jawabin bude taron karawa juna sani a taron kasuwanci da zuba hannun jari a tsakanin yankin da nahiyar Afirka da aka yi a Grenada. Ta kuma kara da cewa:

 Wajibi ne mu bude sabuwar kafar kasuwanci a tsakanin yankunan biyu, kuma ya kamata ace giman kasuwanci a tsakanin bangarorin biyu ya karu da kaso 3% na jumillar kasuwancinmu.”

Kamfanin dillancin labarun “Reuters’ya bayyana cewa wannan matakin na kasashen Caribbean yana nuni da sauyi a huldarsa ta kasunwaci da Amurka da Canada da kuma kasashen turai da su ne abokansu na cinikayya.

  A cikin watan Aprilu ne dai kasar Amurka ta kakabawa dukkanin abokan kasuwancinta kudin fito da sun kai kaso 10%. Bugu da kari Amurkan tana da gagarumin tasiri a cikin harkokin kasuwanci da zuba hannun jari a cikin kasashen yankin na Caribbean.

 Amurka ce babbar abokiyar kasuwancin kasashen yankin Caribbean da take sayen kaso 1/4 na hajar da yankin ke fitarwa da kudin da sun kai dala biliyan 38.8, yayuin da yankin yake sayo kayayyakin da sun kai Dala biliyan 43.4 daga Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted