Kasashen turai da dama sun bada sanarwan cewa zasu dakatar da batun bawa yan kasar Siriya mafaka.
Tashar talabijin ta Presstv ta bayyana cewa gwamnatin kasar Jamus wacce take daukar nauyin mafi yawan yan kasar Siriya masu gudunhira a kasashen Turai, ta bada sanarwan cewa za ta dakatar da karban yan gudun hijirar kasar ta Siriya saboda sauye-sauyen da aka samu a kasar a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Wata jami’ar hukuma mai kula da yan gudun hijira ta gwamnatin kasar Jamus ta fadawa wasu kafafen yada labarai kan cewa, daga yanzu batun karban yan gudun hijira, zai zama bisa wasu al-amura ne kadan.
Labarin ya kara da cewa yan asalin kasar Siriya kimani miliyon 1.3 suke samun mafaka a kasar Jamus, kuma mafi yawansu sun shigo kasar ne daga shekara ta 2015-2016 a lokacinda shugaban gwamnatin kasar Jamus ta lokacin Angerla Merkel ta bada umurnin a shigo da su kasar.
Alice Weidel, jami’a mai kula da al-amuran shige da fice na kasar tana cewa, duk wanda ya ke murna da sauyin gwamnati a kasar Jamus, ya yi shirin komawa gida.
A ranar Lahadin da ta gabata ce wasu yan kasar ta Siriya suka fito kan tituna suna murnar faduwar gwamnatin shugaba Asad.