Kasashen Turai Da Amurka Suna Kokarin Samar Da Wani Sabon Kuduri Kan JMI Dangane Da Shirinta Na Makamashin Nukliya

Wasu masana a nan kasar Iran suna ganin take taken kasashen Turai da Amurka shi ne sake samar da wani sabon kuduri kan JMI dangane

Wasu masana a nan kasar Iran suna ganin take taken kasashen Turai da Amurka shi ne sake samar da wani sabon kuduri kan JMI dangane da shirinta na makamashin nukliya.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin yan watannin da suka gabata, kasashen Turai da Amurka suna kokarin samar da wani kuduri na kushe shirin makamashin nukliya na kasar Iran na zaman lafiya.

Labarin ya kara da cewa JMI ta sha nanatawa kan cewa shirinta na makamashin nukliya na zaman lafiya ne, sannan babu wata shaida da ta tabbatar da cewa ta aika makamai masu linzami zuwa kasar Rasha don yakar Ukraine da su. Amma duk da haka kasashen yamma sun kakaba mata sabbin takunkuman tattalin arziki. Kuma akwai yiyuwan su samar da wani sabon kuduri a kanta dangane da shirin. A cikinshekara mai zuwa na yarjeniyar shirin nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wacce ake kira JCPOA yake kawo karshen amfaninsa.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments