Ministan harkokin wajen kasar Ali Muhammad Umar ya bayyana cewa; Somaliya za ta iya rattaba hannu akan takardun fahimtar juna da za su bai wa Habasha izinin amfani da tashar ruwa da take a gabar tekun Indiya daga nan zuwa watan Yuni.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai Fira ministan kasar Habasha Abi Ahmed ya kai ziyara zuwa kasar Somaliya inda ya gana da shugaban kasar Hassan Sheikh Mahmud, kuma bangarorin biyu su ka tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashensu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Habasha Nebiat Gatachewa ya ce; kokarin da ake yi na bunkasa alaka a tsakanin Addis Ababa da Magadishu ya haifar da da, mai ido musamman a siyasance da kuma ta hanyar diplomasiyya.
Nebiat ya kuma ce; Sabon shafin da aka bude na alakar kasashen biyu yana da alfanu ga kasashen biyu, sannan kuma da samar da zaman lafiya a cikin yankin.
Sabani a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna ya kunno kai ne a shekarar da ta gabata, bayan da kasar ta Habasha ya kulla yarjejeniya da yankin Somaliland akan tashar jirgin ruwa.
Ita dai kasar ta Habasha ba ta da iyaka da ruwa, don haka take son amfani da mashigar ruwan kasar ta yankin Somaliland. Habashan dai tana son gina wani yanki na kasuwanci a gabar ruwan ta yankin Somaliland.
Yankin Somaliland na kasar Somaliya ne wanda Mogadishu take daukar cewa ba kasa ce mai cin gashin kanta.