Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu.
Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun amince da sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da kuma Mosco, sannan zasu kafa kwamiti na musamman don kawo karshen yaki da kuma kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Daga karshen zasu yi aiki tare don bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu. Har’ila taron da kasar Saudiya ta dauki bakwancinsa a jiya Talata ya sami halattar tokwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov, kuma shi ne mataki na farko na hanyar kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.
A taron na jiya dai babu wakilin kasar Ukraine, wacce da alamun ta kasa samun nasara a yakin da ta shiga da Rasha kimani shekaru 3 da suka gabata.