Bayan duguwar tattaunawa a birnin Istanbul na kasar turkiya kasashen pakisatan da Afghanistan sun amince da batun tsawaita dakatar da bude wuta a tsakanin iyakokin kasashen, bayan da kasashen turkiya da Qatar suka shiga tsakanin domin samun daidaito.
Gwabzawa a iyakokin kasashen biyu dake mukwabtaka a yan makwannin nan yana barazana sosai ga zaman lafiyar yankin, sai dai wannan yarjejeniyar za ta hana yaduwar fadan da kuma kara samun hadin guiwa kan tsaron iyakokin.
Zabiullah mujahid kakakin kungiyar Taliban ya tabbatar da kulla yarjejeniyar, kuma yace Kabul tana son samun kyakkyawar dangantaa da dukkan kasashen dake makwabtaka da ita, musamman kasar Pakistan bisa mutunta juna da kuma rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen.