Kasashen Musulmi bakwai, da suka yi taro a Istanbul a ranar Litinin don tattauna makomar Gaza, sun dage kan cewa Falasdinawa ne kawai ke da hakkin mulkin kansu, inda sukayi fatali da sabon tsarin kafa wata wani kwamitin gudanarwa na kasa da kasa a yankin bayan makonni biyu na tsagaita wutar da akayi wacce ke tangal-tangal.
“Dole ne Falasdinawa su mallaki Falasdinawa, kuma Falasdinawa dole ne su tabbatar da tsaron kansu,” in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, ga manema labarai bayan ganawa da takwarorinsa daga Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Jordan, Pakistan, da Indonesia.
“Akwai bukatar sake gina Gaza, kuma mutanenta suna bukatar komawa gida inji shi.
Ya bayyana fatansa na “sulhu tsakanin Falasdinawa” cikin sauri tsakanin Hamas da Hukumar Falasdinawa ta Mahmoud Abbas, Wanda a cewarsa, zai “karfafa wakilcin Falasdinu a cikin al’ummar duniya.”
Ministocin kasashen bakwai, wadanda dukkansu membobi ne na Kungiyar Hadin Kan kasashen Musulunci (OIC), sun gana da Donald Trump a karshen watan Satumba a birnin New York a gefen Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, kafin a gabatar da shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump.