Kasashen Kawancen Sahel Sun Kadaddamar Da Tutar Kungiyar

Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya. An kadaddamar da

Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya.

An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko.

Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya bayyana a yayin bikin, cewa “Tutar kungiyar AES, launin kore, tana dauke da tambarin kungiyar a tsakiyarta.”

 Ya jaddada cewa launin kore yana nuna alamar bege da wadata, wanda ke wakiltar dukiya da karfin tattalin arziki.

Wannan sabuwar alamar ta kunshi hadin kai da muradin bai daya na kasashen uku, inda suka kuduri aniyar yin aiki tare domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar yankin inji shi.

Kaddamar da wannan tuta na zuwa ne kasa da wata guda bayan da aka kaddamar da fasfo din kungiyar a ranar 29 ga watan Janairun 2025, Da nufin karfafa hadin gwiwarsu da saukaka zirga-zirgar jama’a da kayayyaki cikin ‘yanci a cikin yankin.

Wannan taron, wanda wani bangare ne na taron ministocin da ke ci gaba da gudana har zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu, ya tabbatar da aniyar Mali, Burkina Faso da Nijar na kulla kawance mai karfi da ‘yanci, bayan ficewarsu daga ECOWAS da suak zarga da zama ‘yar amshin shatan kaashen yamma musamman faransa wacce ta yi musu mulin mallaka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments