Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Kasashen Iran da Rasha sun mayar da takunkumin Amurka zuwa wata babban dama ta bunkasa ci gabansu
A yayin zaman babban taro mai taken “Rasha da kasashen Musulmi” da aka gudanar a birnin Kazan na kasar Rasha, Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Ali Baqiri ya tabbatar da cewa: Takunkumai da Amurka ta kakaba wa Iran da Rasha sun zama manyan damammaki na musamman ga kasashen biyu a fagen bunkasa harkar ci gabansu sakamakon hazakar shugabannin Iran da Rasha. Ali Baqiri ya jaddada cewa: Rasha da Iran sun yi nasarar mayar da takunkuman Amurka zuwa wasu sabbin damammaki kuma ba gare su kadai ba, har ma ga daukacin kasashen yankin. Yana mai fayyace cewa: Ba zai taba yiwuwa a samar da zaman lafiya a yankin ba, ba tare da kulla alaka ta kud-da-kud ta fuskar tattalin arziki ba, don haka Rasha da Iran za su ci gaba da karfafa dangantakar da ke tsakaninsu.