Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran ya tattaunawa da takwaransa na kasar Qatar kan dakangantar dake tsakaninsu da kuma abubuwan da ke faruwa a yankin, inda dukkan bangarorin biyu suka yi kira kan muhimmancin yin aiki tare adaidai lokacin da ake cikin wani yanayin a kudu da yammacin Asia.
Wannan tattaunawar tana nuna irin yadda kasashen biyu suke son ganin sun kara karfafa huldar diplomasiya da tattalin arziki a bangarorin daban- daban kuma sun nuna damuwa game da yadda rikici ke kara Kamari tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, don haka sun jaddada game da muhimmacin tabbatar zaman lafiya a yankin baki daya,
Ministocin harkokin wajen sun tabo batun ci gaba da aka samu a baya bayan nan a yankin Gaza, inda suka yi kira da a hada kai a ci gaba da nuna goyon bayan Alummar falasdinu . Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan alamuran gaza, manufofin Amurka da makomar yancin kai na falasdinu, inda ake ganin kasashen biyu a matsayin masu ruwa da tsaki wajen tsara zaman lafiya da tsaro a yankin.