Firay ministan kasar Burtaniya da tokwarorinsa na kasashen Canada da Australia duk sun bayyana amincewar gwamnatocinsu da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta. Wanda ya nuna sauyi babba a al-amuran diblomasiyya wadanda suka sha fi HKI da kuma Falasdinawa. Kafin haka dai, idan an masu maganar samar da kasar Falasdinu sai suce sun barwa HKI ta tattunawa da Falasdinawa don warware matsalar tsakaninsu.
Sauya matsayinda wadan nan manya-manyan kasashen duniya suka yi ya sake bude batun samar da kasashe biyu, wanda kuma zai kara tura HKI zuwa bongo don amincewa da samar kasar Falasdinu da kuma bukatar ta dai kissan kiyashin da takewa al-ummar Falasdinu a Gaz da kuma yankin yamma da kogin Jordan.
Kafin haka Falasdinawa sun bukaci kasashen su amince da samauwar kasa don shi ne mataki na farko na kasa kasar ta Falasdinu.
Ya zuwa yanzu dai kasashen duniya kimani 140 ne suka amince da samauwar kasar Falasdinu, Keir Starmer firay ministan kasar Burtaniya ya yi kira ga HKI ta bude hanyoyi wa kungiyoyin agaji su shigar da abinci zuwa Gaza.
Amma gwamnatin kasar Canada ta bayyana cewa gwamnatin HKI mai ci tana aikin ganin ba za’a taba kafa kasar Falasdinu mai zaman kanta ba.